Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Wani Kamfani A Nijeriya Ya Kirkiro Manhajar Gano Wayoyin Da Aka Sace

Wani Kamfani A Nijeriya Ya Kirkiro Manhajar Gano Wayoyin Da Aka Sace

Wani kamfani a Nijeriya, E.F. Network Ltd, ya kirkiro manhajar wayar sadarwa da ake amfani da ita wurin lalata wayar da aka sace, domin hana barayi sakat da tseratar da muhimman bayanan mai ita.

Kakakin kamfanin, Ameh Ochojila ya ce manhajar mai suna ‘ephonetaxi’ za ta taimaka wurin tseratar da dubban wayoyi da barayi ke sacewa.

“Ephonetaxi za ta taimaka ka kange dukkan wanda ba shi da alaka da amfani da wayarka, ta yadda za ka mayar da wayar mara amfani tamkar fanko”, inji shi.

Ya ce an kirkiro manhajar ce don ba wa masu waya da bayanansu da ke cikin wayoyinsu kariya daga sharrin barayi.

“Za ta taimaka wa masu wayoyi maido da bayanansu zuwa E-mail dinsu.

“Sannan za ta ba wa masu waya damar rufe rumbunan hotuna da bidiyonsu a cikin wayar ta yadda mai wayar ne kadai zai iya ganin su ko sakonninsa ko lambobin wayar da ke ciki.

“Tana sanar da mai waya idan sauya masa katin sim, sannan ta lalubo inda wayar take, ta kuma dauki hotunan barayin da suka sace wayar ta tura masa zuwa Imel din sa”, inji shi.


Wani Kamfani A Nijeriya Ya Kirkiro Manhajar Gano Wayoyin Da Aka Sace

Ochojila ya kara da cewa, “Mai ainihin wayar na da damar aiwatar da duk abun da aka lissafa don maganin barayi.

“Wani abun shi ne, duk wanda ya sayi wayar to tamkar ya barnatar da kudinsa ne”, kamar yadda ya ce.

Manajan Kula da Sashen Kwararru na kamfanin ya yi karin haske ce wa, ana amfani da ephonetaxi wurin gano masu garkuwa da mutane ta yadda za ta bayyana hakikanin wuri da kuma lokacin da masu garkuwa suka sace mutum.

Shugaban kamfanin Mista Gideon Egbuchulam, ya ce ephonetaxi daya ce daga manhajojin da kamfanin ya samar don kaiwa matsayin da Nijeriya take fata na samun masu fasahar kirkire-kirkire a fannin kimiyya.

Egbuchulam ya ce wa, yanzu kamfanin ya bude ofishinsa a Abuja don kyankyasar kwararrun matasa masu kaifin basira a bangaren kimiyya da sadarwa (IT).

“Hakan zai ba wa Nijeriya damar samar da matasa da za su zama jagorori a fadin nahiyar Afirka.

“Kusan dukkannin kamfanonin kimiyya a duniya na sha’awar kasuwanci da Nijeriya saboda haka yanzu haka kamfaninmu zai dauki ma’aikata 1,000 masu kaifin basira zuwa karshen 2020”, a cewarsa.

Kamfanin dillancin labarai a Nijeriya (NAN) ya bayar da rahoton da ke cewa a shekarar 2016 an sace sama da wayoyi 400,000 a Amurka, kuma galibin wayoyin an fitar da su ne zuwa kasashen duniya don a sake siyar da su.

Binciken ya tabbatar da cewa yawancin wayoyin da ake sacewa ana siyarwa ’yan fashi da gungun masu aikata miyagun laifuka ne, ta yadda suke samun muhimman bayanan ta yadda suke samun shiga asusun ajiya na banki su yi satar kudade ba tare da masu asusun sun ankara ba.mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *