Bari ba Shegiya ba ce! Facebook ta amsa kiran ‘Yan
Afirka
Bayan da aka akai harin kunar bakin wake a kasar Faransa
a ranar Juma’a 13/Nuwamba/2015 munate da dama basu ji dadin yadda babban shafin
sada zumunicin nan mai suna Facebook ya fito da wani tsari na canza hoton da ke
wakiltar mutum zuwa tutar kasar Faransa.
Mutane daga kowane bangare na Duniya sun nuna bakin
cikinsu dangane da wannan mummunan hari na ranar Juma’a sai dai a wani bangare
kuma an samu korafe-korafen jama’a kasancewar kamfanin Facebook ya nema jama’ar
duniya da su yiwa kamar faransar Addu’o’in zaman lafiya.
Wannan kira da kuma neman jama’a su can hotunan su ya
bakantawa mutane da dama rai musamman mutaken yankin Larabawa da kuma nahiyar
Afirka, musamman saboda ganin irin zubar da jini da ake yi ba dare babu rana a
yankunan amma kuma daidai da nuna wani abu yana faruwa wannan kamfani bai taba
nuna wa ba.
Hakan ya san wani shararren marubu ci mai kishin kasa
Jafar Jafar ya rubuta zungureriyar wasika zuwa ga Mark Zuckerberg wanda shi ne
shugaban wannan kamfani yana mai nuna damuwar sa da ko in kula da bai nuna wa
ga jana’ar Afirka musamman idan aka dubi cewar mutane kusan sama da dubu goma
sha takwas sun rasa rayukansu a hare-haren da Kungiyar Boko Haram take kaiwa a
Arewacin Najeriya.
Ba ma Jafar da ya yi wannan rubutun ba kusan mutane sun
yi amfani da wannan kiran da shi Mark Zuckerberg ya yi suna canza hotunan su
zuwa hotunan kasarsu, kuma suka rika yin amfani da kalmar bai daya (Harsh Tag)
suna cewar ayi wa duniya baki dayanta addu’ar neman zaman lafiya.
SAFETY
CHECK
Wannan shi ne tsarin da kamfanin facebook suka fito da
shi a Labara 18/Nuwamba/2015 bayan da aka kai harin da ya hallaka mutane a
kalla talatin a garin Adamawa.
Wannan tsari ne da yaka baiwa duk wanda ya ke kusa da
inda abin ya faru ya sanar da al’umma irin halin da yake ciki na yin makin
cewar yana lafiya ko kuma shi babu abin da ya shame shi.
Wannan ba karamin ci gaba bane idan muka yi la’akari da
irin korafe-korafen da jama’a suke yi na cewar ana nuna musu launin fata.
Duk da haka, wasu jama’a suna ganin cewar wannan fito da
wannan tsari ba wani abin a zo a gani ba ne, domin har zuwa yanzu kamfanin bai
dawo da tsarin da zai baka damar ka canza hotonka zuwa ga tutar Najeriya ba. A
na su ra’ayin jama’a suna ganin idan dai ba nuna wariyar launin fata ba ya
kamata a ce shi ma wancan tsarin na canza hoto ya kamata a ce yana aiki, kuma
suna ganin kamar yadda yayi magana a cikin shafinsa na a nemawa Faransa zaman
lafiya, ba wai dawo da tsarin fadin yanayin da mutum ya ke ciki za su ba,
magana zai yi.
Sai dai muce Allah Ya kyauta kuma ya gafartawa suka riga
mu da imani amin.
No comments:
Post a Comment