Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

ABUBUWA 8 DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN ASIYA WAYA KO TABLET (SMARTPHONE

ABUBUWA 8 DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN ASIYA WAYA KO TABLET (SMARTPHONE
ABUBUWA 8 DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN ASIYA WAYA KO TABLET (SMARTPHONE
 
Idan aka ce smartphone ana magana ne da wayar da ta cika gari a wannan lokacin wacce zai yi wahala ka samu mutum biyu wadanda suke rike da waya amma kuma ba a samu mai ita ba. Irin wadannan wayoyi sun cika ko’ina, ga shi kuma kamfanonin da suke yin su kullum kara fito da sababbi suke yi kasuwa.

Kodayake a irin tunani namu na bakaken fata kasancewar waya na da tsada shi ne ke nuna cewar wannan wayar tana da kyau, wani lokaci kuma neman iyawa da bajinta da nuna isa shi ke sa mu mallaki waya wacce take da tsada ba yin la’akari da me ke cikin wannan wayar ba ko kuma me wannan wayar zata iya yi mana.

Wani abu kuma da yake daurewa masu son su siya sabuwar waya shine, idan na samu kudi wace irin waya ya kamata in siya, ko kuma mene ne abin yin la’akari da shi idan ina son canza waya ko kuma sake sabuwa. Amsoshin wannan tambayar ya danganta da me kake son yi da wayar, domin wani yana yin la’kari da karfin wayar wurin rike wuta ko caji, wani kuma yana yin la’akari da kyau na hoto da take dauka, wani kuma yana yin la’akari da karfin network da take da shi, wani kuma yana yin la’akari da girman fuskarta, da dai makamantan wadannan.


1. ==> GIRMAN FUSKAR WAYAR

A wurin siyan waya ko tablet mutane suna yin la’akari da girman fuskar wayar wato (screen). Wani yafi so ya ga waya faskekiya a wurin sa, wani kuma baya son ganin haka. To shi dai maganar fuskar waya ra’ayi ne, kuma wanda yayi maka ba dole ba ne yayi wa wani. Amma dai a zahiri idan kasan kai mutum ne mai son wayarka ta rika zama da caji to girman fuskar waya da barin ta cikin haske sosai na taimakawa wurin cinye caji.

2. ==> KAURI DA NAUYI

Kauri da nauyin waya abu ne mai muhimmanci a lokacin da mutum zai sayi waya ko tablet. Kauri dai an fi lura da shi akan komai, wani lokaci sirantaka a wurin kayan computer bai cika bayar kaya masu inganci ba a wani lokaci. Saboda haka ya danganta gare ka idan kana son kyau fiye da inganci sai ka tsallaka siriyar waya ko tablet. Kodayake wadansu wayoyin suna da jikin karfe ne saboda haka tun kafin kabar wurin siya ka tabbatar ka duba don kada karfen ne ya sata tayi nauyi.

3. ==> MANHAJOJIN (Operating System) DA WAYA TAKE AMFANI DA SU

Babbar Manhajar da take sarrafa komai da ke jikin waya shi ake kira da Operating System, shi yake lura da hatta maballan da kake tabawa wurin kunnawa da kashewa, shi yake lura da sauti da kalan da yake fita a wayar. To lallai wurin siyan waya yana da kyau ka duba da kyau domin ka san wane irin manhaja ce a cikin wannan wayar. Kamar yadda da yawa daga cikin mu suka sani cewar wayoyin da muke rikewa suna da banbanci wurin gininsu da kuma wane ne yayi su? Kunga dai wayoyi idan ya zo ga maganar Operating System akwai na Android, sannan ga iOS, sai Microsoft Phone 7, sai Blackberry ga kuma web OS da Symbian, dukkan wadannan da na lissafo da yawa daga cikin mu sun dauka cewar waya ce. A a kamfani da yake yin karfe da kyan da suke jikin waya daban sannan manhajar da ake saka mata da ba. Wadancan sunaye da aka ji na lissafo mutane sun fi sabawa da su a matsayin waya maimakon Babbar Manhaja ce.

4. ==> WURIN ADANA BAYANAI

Mafi yawan kanfanonin da suke yin wayoyi da tablet a wannan lokaci suna kokarin ganin sun yi mata mazubi da ya kai girman gig 16GB, wanda zai baka dama domin a jiyar hotuna da rubutu da sauti da hotuna masu motsi. Kodayake wadansu saboda yanayin yadda suke tara abubuwa a cikin wayoyinsu suna bukatar karin abubuwa a ciki. To a nan yana da kyau ka sani wayoyin da kamfani Apple suke yi su basa bada ramin kara ma’ajiya wato Memory, saboda haka idan kasan kai mai sun ajiyar abubuwa ne sai ka nemi koda wayar Apple amma mai mafi girman mazubi.

5. ==> KARFIN SHIGA INTERNET

Kusan dukkan wayoyin tafi da kidan ka suna zuwa da tsarin sadarwa maras waya (wireless) wanda ya ke basu damar iya kulla alaka tsakaninsu da ko kamfanin layukansu ko kuma hanyoyin shiga intanet da yake gida ko kuma ofis da dai makamantansu. Irin wadannan hanyar da ake amfani da ita domin samun sinadarin shiga intanet ba tare da amfani da layin waya ba shine ta hanyar amfani da Wai-Fai (Wireless Fidility). Amma yana da kyau wanda zai sayi waya a wannan lokaci ya san cewar yanzu ma muna karni na uku bane 3G (Third Generation) ta wurin shiga intanet, a’a a wannan kasa yanzu haka akwai kamfanoni da suka tsallaka karni na hudu 4G.

Wayoyin da aka yi a baya sun fara ne da 1G sai kuma suka shiga 2G wanda irin wadannan wayoyin ba sa ba msutum damar shiga intanet da sauri, koda kuwa a inda mutum ya ke akwai network mai kyau da karfi. Daga baya suka shigo da 3G wanda yake bamu damar har kallon hotuna masu motsi (video) muke yi ba tare da yana tsayawa ba. Saboda haka yanzu mafi yawan wayoyin da ake yi suna baka damar amfani da karfin network na 3G da 4G, sai a kiyaye idan an je siya.

6. ==> KANA NAN MANHAJOJI

Daya daga cikin abin da mutane da dama suke yin la’akari da shi shine idan na sayi waya iri kaza shin dawe application ne zan iya aiki, kusan a wannan lokaci da muke ciki kasancewar wayoyin Android sun fi yawa da kuma saukin koyan yadda ake kirkiran manhajojinsu, yasa mutane da dama suke son siyar wayar Android. Amma kuma idan aka zo ga zafafan Manhajoji to sai muce manhajojin da ake amfani da su a waya kirar Apple sun fi shahara da kwarjini.

Misalia shagon Apple akwai manhajoji dubu dari uku na kyauta da kuma na siyarwa, a kuma shagon Android akwai manhajoji dubu dari biyu da hamsin na kyauta da kuma siyarwa. Suma sauran manhajoji irin su Blackberry da makamantansu suma suna da shagunan da ake samun manhajojinsu saidai ba su kai na Apple da Android yawa ba.

7. ==> Kamara da Nado Sauti'

Hakika wadannan abubuwa guda biyu sun karawa wayoyin tafi da gidanka daraja, kusan a yanzu mutane da dama suna yin amfani da kamarar jikin wayoyinsu domin daukar shagulgulan biki da suna da taron siyasa, wa’azi, wasan kwaikwayo da dai makamantansu. Wannan dalilin ne ya sanya wayoyi a wannan lokacin suke kara yin tsada, duk da cewar mutane da dama basu cika kiyaye haka ba.

Kusan a yanzu akwai wayoyin da ake da su wadanda saboda karfi da kyau yanayin hotuna da suke dauka hatta mawaka suna amfani da su wurin shirya wakokinsu. Haka yan jarida a wannan lokaci suna yin amfani da wayoyi wurin nado sauti da zasu iya kai rahoto da shi. Duk da cewar karfin wata wayar ya fi na wata, amma waya da kamara da kayan daukan sautin da ke jikinta ya mayar da mutane ‘yan jaridan tafi da gidanka amma wasu ba su sani ba. To ba kowace waya bace ta ciki inganci a kan haka. Sannan idan ka san kai baka damu da kyau na hoto ba to ba sai ka sayi waya mai tsada ba.

8. ==> DADEWAR BATIRI

Lallai ko ba a fada maka ba kasan cewar batir yana da matukar muhimmamci a jikin waya domin duk irin aikin da waya zata yi maka idan har batirin wayar baya dadewa abin ya zamo da shirme ke nan. Shi yasa kuwan mafi yawan kamfanonin da suke kirkirar waya suka fi mayar da hankali wurin ganin batar na dadewa, duk da irin kurakurai da ake samu wadansu kamfanonin suna yi sai ka samu kamfani yayi waya kuma cikawa batirin sinadari da idan ya ji rana zai kama da wuta, amma dai suna kokari.

 Zaka samu wayoyi a wannan lokaci ana inganta batirinsu har kaga waya tana iya kwana uku tana aiki, kodayake ba kowa yasan wayoyin wannan lokacin suna haka ba, kasancewar idan muka sayi waya bama karanta takardar da take zuwa da ita.


Wannan shine abubuwan da zan iya kawo muku wadanda sune abubuwan da ya kamata mu rika yin la’kari da su wurin sayin waya.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *