Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Fasahar E-Naira: Ma’ana, Fa’idoji Da Tsarin Gudanuwarsa

Fasahar E-Naira: Ma’ana, Fa’idoji Da Tsarin Gudanuwarsa

A ranar Jumma’a, daya (1) ga watan Oktoban 2021 ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya so kaddamar da sabon nau’in kudin zamani mai suna: e-Naira, a tsarin gwaji.

Sai dai CBN ya dage kaddamar da sabon nau’in kudin saboda wasu dalilai da ya alakanta da al’amuran da za a gudanar a kasar na bikin cikarta shekara 61 da samun ’yancin kai.

Haka kuma wannan jinkiri ya zo na kwana guda bayan da wani kamfani mai suna ENaira Payment Solutions Limited ya shigar da karar Babban Bankin Najeriya a gaban Babbar Kotun Tarayya kan amfani da sunan ENaira.

Wannan gwaji da Babban Bankin ya so aiwatarwa zai kai har zuwa karshen wannan shekara, kafin tsarin ya game kowa da kowa.

Don haka, na ga dacewar fara bayani a fayyace, cikin harshe mai saukin fahimta, don bai wa masu karatu damar fahimtar wainar da ake toyawa.

Wani dan uwa, wanda masani ne a harkar sadarwar zamani, ya kira ni kwana 5 da suka gabata, inda yake yi min tambaya kan wannan nau’in kudi.

Daga salon tambayarsa ce na fahimci lallai akwai bukatar yin bayani don kara wayar da kan jama’a. Makalarmu ta yau dai za ta zo ne a salon tambaya da amsa. A sha karatu lafiya.

Mene ne e-Naira?

Kudin e-Naira nau’in kudi ne da yake maye gurbin makwafin takardar Nairar Najeriya a tsarin hada-hadar kudade da ake gudanarwa a kafafen sadarwa na zamani.

Darajarsa daya ce da takardar Naira. Sai dai ana iya amfani da shi wajen cinikayya kai-tsaye, a ko’ina ne a duniya.

Kamar yadda karbar takardar Naira take wajibi a Najeriya, haka yake wajibi duk wanda aka sayi hajarsa, ko ya gudanar da wani aiki aka ba shi wannan nau’in kudi ya karba.

Wannan nau’in kudi, kamar takardar Naira da Bankin CBN ne ke bugawa, da tantancewa, da kuma bayar da shi.

Kuma kasancewar rayuwarsa gaba daya a kan tsarin magudanar fasahar hada-hadar kudade ta Intanet ce (Blockchain), akwai tsaro mai karfi ta yadda ba wanda zai iya kirkirar jabunsa.

A takaice dai, nau’in kudi ne na zamani da ake amfani da shi ta hanyar kafafen sadarwar zamani, wanda ake kira Stable Coin.

Idan haka ne, mene ne bambancinsa da su Bitcoin?

Akwai abin da ya hada su, kuma akwai abin da ya raba su. Abin da ya hada su shi ne, kowane daga cikinsu nau’in kudaden zamani ne, wato Digitial Currency, kuma ana kirkira tare da aika su ne ta hanyar fasahar Blockchain, wato magudanar da ake amfani da ita wajen aiwatar da hada-hadar kudade mai cike da tsaro a Intanet.

Amma kuma, a daya bangaren, yayin da e-Naira ke amfani da killataccen tsarin aikawa da karbar kudade a Blockchain, Bitcoin yana amfani ne da tsarin da ke warwatse; ma’ana, babu wata hukuma da take iya sanin abin da masu amfani da madaukan ke karba ko aikawa. Wannan shi ake kira Distributed Ledger System.

Duk abin da ka mallaka a taskarka, kai kadai kake sanin nawa ne, kuma wa da wa suka aiko maka kudi. Amma a tsarin da aka gina e-Naira, Bankin CBN ne yake gudanar da komai, wajen samar da kudin da killace yawansa da kuma bai wa bankunan ’yan kasuwa damar aikawa da karba a yanayi daban-daban.

Ta wace hanya zan iya mallakar eNaira?

Wannan sabon tsari yana dauke ne da manyan matakai guda biyu.

Matakin farko shi ne ya kunshi alaka ce a tsakanin Babban Bankin Najeriya (CBN) da sauran bankunan kasuwanci (Commercial banks).

Mataki na biyu kuma tsakanin bankunan kasuwanci ne da masu ajiya.

A matakin farko, Bankin CBN zai bai wa bankunan kasuwanci damar isa ga tsarin, tare da bude musu asusun ajiyarsu ta Intanet (eNaira Wallet), wanda yake dauke da adadin abin da suka saya na e-Naira.

A karkashin wannan tsari ne zai ba su damar bude wa masu ajiya asusunsu su ma, da ba su damar iya saya musu nasu nau’in eNaira din, ta amfani da babbar magudanarsa (CBN Blockchain).

Sai mataki na biyu, wanda zai kasance a tsakanin bankunan kasuwanci da masu ajiya.

A wannan mataki, bankunan kasuwanci za su yi mu’amala ce da nau’in mutane biyu.

Na farko su ne masu taskar ajiya a bankunansu. Na biyun kuma wadanda ba su da taskar ajiya a kowane banki.

Yaya karbuwar wannan kudi yake a duniya?

Ba ka da matsala wajen hakan. Yadda takardar kudin Najeriya take halattacciya kuma amintacciya wajen kasuwanci, haka wannan nau’in kudi na eNaira yake halattacce.

Da zarar ka loda wani adadi na kudi a taskar eNaira Wallet, za ka iya aiwatar da cinikayya da shi kai-tsaye, a kowane shagon sayar da kayayyaki. Koda kuwa farashin hajar na wata kasa ce daban. Wannan ba damuwa ba ce.

Da zarar ka shigar da bayanan taskar ajiyarka ta eNaira, nan take tsarin zai kimanta adadin kudin da za ka biya da eNaira, gwargwadon farashin kudin kasar da ka aiwatar da cinikayya da shi.

A daya bangaren kuma, kana iya aika wa dan uwanka ko wani naka wannan nau’in kudi a ko’ina yake a duniya, ta amfani da lambarsa ta eNaira Wallet idan yana da shi, ko ta taskar ajiyarsa a ko’ina yake a duniya.

Idan ina son ciro kudin a zahiri kuma fa?

Wannan abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka. Sai kawai ka loda kudin zuwa taskar ajiyarka na banki.

Daga nan ka yi amfani da katin ATM dinka ka ciro su. Ko ka je bankinka ka cira kai-tsaye. Ko kuma ka aika wa wani a taskarsa, shi kuma ya ba ka takardun kudi.

Wannan bai takaitu ga adadin kudin da wani ya aiko maka ta manhajar eNaira Wallet dinka ba kadai.

Hatta adadin kudin da ka loda daga taskar ajiyarka na banki, sai daga baya ka ji kana bukatar ka dawo da su don ka cire saboda wasu bukatu ko lalurar rayuwa da ta shafi kudi, kana iya sake dawo da su taskar ajiyarka ta banki kai-tsaye, ba tare da wani caji ba, sannan ka cire su don biyan bukatarka.mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *