Shugaban
kamfanin sada zumuntar intanet na Twitter, Jack Dorsey ya sauka daga
mukaminsa, sama da shekara daya da tsallake rijiya da baya da ya yi, bayan
da wani dan gwagwarmaya mai hannun jari a kamfanin ya jagoranci yunkurin tsige
shi.
Dorsey, wanda shi ne shugaban kamfanin hada-hadar kudade na Square ya shiga cikin matsin lamba a shekarar 2020 daga hukmumomin kamfanin Elliott, wadanda suka bayyana damuwar cewa ya mamaye ko ina, kuma ayyuka na yi masa yawa ta wajen tafiyar da kamfanoni 2.
A
wata sanarwa, Dorsey ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne la’akari
da cewa kamfanin ya shirya ci gaba da harkokinsa ba tare da wadanda suka
assasa shi ba.
Kamfanin
ya ce yanzu shugaban bangaren injiniyoyinsa, Parag Agrawal ne zai maye gurbin
Dorsey, inda tuni shugaban mai barin gado ya bayyana kwarin gwiwarsa a kansa.
Dorsey
zai ci gaba da kasancewa mamba a majalisar zartaswar kamfanin har zuwa shekarar
2022 lokacin da wa’adinsa zai kare a yayin taron masu hannun jarin kamfanin.
Kamar sauran masu manyan kamfanonin sadarwar zamani irin su Mark Zuckerberg da Steve Jobs zuwa Bill Gates ko Michael Dell, Dorsey bai kammala karatun jami’o’in da ya halarta a garinsa na Missouri da New York ba.
No comments:
Post a Comment