Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Za'a Samar Da Fasahar Intanet A Duniyar Wata

Za'a Samar Da Fasahar Intanet A Duniyar Wata

Shekaru kusan 50 kenan da dan Adam ya fara taka kafarsa a duniyar wata, sa’ar da mahaya Kumbon Apollo 11 suka ziyarci duniyar.

Daga wancan lokaci zuwa yanzu dai an samu ci gaba a fannin kimiyyar sararin samaniya sosai.

Wannan ya sa a halin yanzu Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Kasar Amurka (NASA), ta kudiri aniyar sake komawa duniyar wata a shekarar 2024.

Sai dai a wannan karon ziyarar za ta sha bamban da ziyarar farko. A karon farko mace za ta kasance cikin ayarin. 

Sannan za a hada da bakin fata, cikin masu tafiya.

Bayan duk wannan, za a samar da Intanet mai zaman kansa, wanda zai dace da yanayin wancan muhalli, don taimakawa wajen sauwake sadarwa a tsakanin maziyarta.

Wannan nau’in Intanet da za a samar a duniyar wata dai an kira shi da sunan: LunaNet, wanda ke nufin nau’in Intanet din da ya dace da sararin samaniya.

Wannan shi ne abin da shafin Autoevolution ya tabbatar, daga Hukumar NASA da ke Amurka.

Wannan nau’in Intanet mai suna LunaNet dai zai taimaka wajen hada alakar sadarwa a tsakanin masu lura da cibiyar tauraron dan Adam ce a wannan duniyar tamu, da wadanda suke can duniyar wata a cikin kumbo.

Wannan shiri na samar da Intanet a duniyar wata ya faro ne tun shekarar 2019, daga cibiyar bincike ta NASA da ke Goddard (Goddard Space Flight Center), a Jihar Maryland ta kasar Amurka.

Asalin manufar shirin shine samar da tsarin sadarwa a tsakanin kananan taurarin dan Adam da ke shawagi a harabar wata da ke sararin samaniya.

Sabanin tsarin Intanet irin wanda muke amfani da shi, wanda kana iya aika sako amma ya kasa isa inda aka aika saboda matsalar yanayin sadarwa, LunaNet na dauke ne da wani tsari mai suna: Delay/ Disruption Tolerant Networking (DTN).

Aikin wannan tsari shi ne, duk sakon da aka aika sai ya isa adireshin da aka aike shi.

Idan ma ya samu matsala a hanyarsa, tsarin na iya taskance shi, ya ci gaba da neman hanya ingantacciya marar matsala.

Da zarar ya samu sai ya saki sakon, har ya isa inda aka aike shi.

Bayan haka, wannan nau’in Intanet zai rika taimaka wa masu shawagi a duniyar wata wajen gano bigiren da suke a taswirar duniya, tare da samun hanya mafi sauki wajen zirga-zirga a muhallin da suke.

Hakan kuwa zai yiwu ne ta hanyar siginar sadarwa da tsarin zai rika aika musu a iya kadadar sadarwa da suke.

Daga cikin siffofin LunaNet har wa yau, tsarin zai rika amfani da hanyar karbar siginar yanayi a sararin samaniya wajen sanar da masu shawagi a duniyar wata duk wani abu mai hadari da ke tafe ko yake kusa da su, musamman tartsatsin yular wuta da ke fetsowa lokaci-lokaci daga jikin rana ko harshen tururin wuta da ke yawo a sararin samaniya.

Sannan akwai tsarin nemowa da ceto wanda ya fada cikin wani hadari (Search and rescue).

Bayan haka, abu na karshe mai kayatarwa game da LunaNet shi ne, an gina masa tsarin nemo sigina mai dauke da bayanan wasu duniyoyi da suke makwabtaka da duniyarmu, musamman duniyoyin da suke nesa da mu ainun.

Wannan tsari, a cewar masana, zai bai wa malaman sararin samaniya damar aiwatar da bincike a aikace, don gwajin ka’idojin kimiyyar sararin samaniya da aka dade da rubuta su a nazarce.

Kuma sakamakon da za a samu zai taimaka matuka wajen kara gano yadda tsarin halittar duniyar take gaba daya ma, ba wannan duniyar tamu ba kadai.

Sai dai, wannan nau’i na Intanet da ake kan ginawa, ba irin wanda muke amfani da shi ba ne a wannan duniya tamu, wanda za ka hau a shafin Google, ko Youtube ko Facebook.

A’a, yanayi ne na sadarwa da ke bai wa na’urorin sadarwar da ke muhallin da suke damar ganin juna da sanin bigiren da kowane yake, ta hanyar shafi na musamman da tsarin zai samar.

Kuma idan ba a mance ba, a mukalar farko da aka fara bugawa a wannan shafi mai albarka, na yi mana bayanin ma’anar Intanet da cewa, tsari ne da ke “bai wa kwamfutoci da sauran na’urorin sadarwa damar magana da juna wajen aikawa da karbar sakonni a iya zango ko kadadar sadarwa na musamman.”

Ka’idar da ke taimaka wa kwamfutoci aiwatar da irin wannan nau’i na sadarwa dai ita ce ginanniyar ka’idar sadarwa mai suna: Internet Protocol (IP, wadda ke amfani da adireshin kowace kwamfuta ko na’urar sadarwa a tsarin lambobi, don aiwatar da sadarwa a tsakaninsu.

Irin wannan tsari na sadarwa shi ne LunaNet ke amfani da shi don taimaka wa masu shawagi a duniyar wata.

Ana kuma sa ran fara amfani da shi a shekarar 2024, sa’ar da Hukumar NASA za ta koma duniyar wata dauke da mahaya na musamman.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *