Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

MATAKAI BIYAR DA ZAKA BI WAJEN GANIN BLOG NAKA YA ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAFUKA MASANA

MATAKAI BIYAR DA ZAKA BI WAJEN GANIN BLOG NAKA YA ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAFUKA MASANA


Tare Da Muhammad Abba Gana {Jikan Marubuta} 

A zamanin namu na yanzu mutane da dama suna aiki da blog ne kawai da manufar samun kudi, ko hanyan samun kudi wasu kuma suna aiki dashi ne saboda hanya ce da zai taimaka sosai wajen kasuwanci. 

Haka kuma ma danfara sukan samu hanyar danfaran mutane saboda yanda mutane suka sha’afa da aiki dashi. Sau da dama mutane sukanyi korafin cewa basu samun mutane suna ziyartan shafinsu wanda sun bi duk wata kayatacciyar  hanya daya dace a abi dan ganin mutane suna da masaniya a kanta. 

Abu daya kamata mu sani shine yawan sa ran samun kudi ta hanyan yanar gizo yana daya daga cikin abubuwan dayake janyo rashin ziyartan mutane saboda bazaka sa ko kayi abunda ya dace ba kawai matsalar ka kaga dubban mutane suna ziyar tan shafinka wanda hakan ba karamin abu bane kuma ba abun gaggawa bane. 

Yana da kyau ka kasance na musamman in kana son cimma manufarka na zama daya daga cikin shahararrun masana kan yanar gizo ko kuma zama daya daga cikin hamshakan mutane da suke samun kudi ta hanyan yanar gizo. 

Maganar gaskiya, akwai dubban hanyoyi da ake bi wajen ganin shafi ya riske mutane da dama abu na farko ya kunshi abubuwa masu inganci, duk da cewar ba bangaren nan zan tabo ba yau zan mayar da hankali ne game da asalin shi shafin wato sarki da kansa wanda shine “abun dake ciki” ko yaya shafinka ya kasance misali gwani wajen sura (design) yawan sa a wajen mutane a karshen mako abinda ke cikin shafinka ne zai sanar da mutane manufanka,

ABU NA FARKO

GWAJIN KWARI (QUALITATIVE CONTENT)

MATAKAI BIYAR DA ZAKA BI WAJEN GANIN BLOG NAKA YA ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAFUKA MASANA

Kamar yanda na ambata a baya bazanyi Magana a kan suran shafiba wato design a turace, yanda aka jera shafi da sauransu, zanyi bayani a kan sarkin shafi shine inganta rubuta koh abunda ake sawa a ciki wanda shine jijiyan shafinka kuma nasaranka. 

Shawara na anan shine, in kana son shafinka ya dauka ka to dole ka lura ka kuma inganta wayannan abubuwa dan ganin shafinka ya daukaka wanda zai iya zama ta hanya daban-daban wanda sun hada da harshe, nahawu, gabatarwa, hotuna da dai makamantansu.

ABU NA BIYU

 INGANTA DABI’A (USE CASUAL MANNER)

MATAKAI BIYAR DA ZAKA BI WAJEN GANIN BLOG NAKA YA ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAFUKA MASANA


Wani abu da zaka ga a sabbin shafuka suna farawane da niyyan samun kudi wanda basu da masaniya akan yanda ake tafiyar da abun, yaya ake budewa ko kuma yaya za’a magance idan matsala ta taso wasu daga cikin su kuma sam basu da dabiu masu kyau wasu sukan bude dan labarai wasu dan wakoki wasu shafukan idan ka gani kamar inji mai aiki da kansa ne ya bude, yana da kyau in zaka bude shafi ka zauna kayi nazari a kan shin maisa zan bude?? 

Ta wani bangaren zan taimaka? Shin wani yana yin abunda zan yi? Wayannan sune kadan daga cikin abubuwan da ya kamta ka tambayi kanka kafin bude shafi haka zalika in kazo rubuta abu da zaka sa a shafinka ya kasance ka rubuta cikin nitsuwa kayi tunanin mai zaka rubuta yaya kuma zaka rubuta yana da kyau in zaka rubuta abu kayi tunanin kamar tadi kakeyi da abokinka ko dan uwanka ta hanyan nishadarwa tare da nuna girmamawa a rubutunka wanda zai sa mutane da dama suyi sha’awar dawowa shafinka.

ABU NA UKU

KADA KA RUBUTA ABU MAI TSAWO (DON’T POST LONG ARTICLES)


MATAKAI BIYAR DA ZAKA BI WAJEN GANIN BLOG NAKA YA ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAFUKA MASANA


Mutane da dama suna da ra’ayin kin karanta rubutu masu tsawo a yanar gizo in suna so su karanta novel sukan ware lokaci na musamman, kayi kokarin zuwa kai tsaye abunda kake son sanarwa ya zamana a gajarce duk da cewar akwai wasu abubuwa da bazasu iya gajartuwa ba ko kuma a kankantar dasu in hakan ya kasance ka rarrabasu zuwa gida-gida wannan ba kawai zai kara mutane masu ziyartan shafinka ba, mutane da dama zasu ji dadin karanta abu a shafinka saboda basu son karatanta abu mai tsawo.

ABU NA HUDU

KA YAWAI TA DUBA HARUFFAN KALMA (ALWAYS CHECK YOUR WRITING SPELLING)

MATAKAI BIYAR DA ZAKA BI WAJEN GANIN BLOG NAKA YA ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAFUKA MASANA

Yana da kyau kafin ka saka post a blog kabi rubutun da kayi dan duba in da akwai matsala da yanda nahawu naka ya kasance kafin ka sawa masu karatu  ga wayanda suke aiki da wordpress akwai wani plugin mai suna “after the deadline” wannan plugin yakan taimaka sosai wajen duba harrufa da kuma jimla da ka rubuta a harshen turanci amma yana aiki ne da harshe turanci. 

ABU NA BIYAR

KA DAGE WAJEN SAKA SABIN ABUBUWA (TRY AND POST OFTEN)



MATAKAI BIYAR DA ZAKA BI WAJEN GANIN BLOG NAKA YA ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAFUKA MASANA


Mabiyanka wanda suke son abubuwan da kake rubutawa zasuna marmarin suga kasa abu sabo, in ya kasance kana sa abu sabo sau guda a wata ko kuma sau daya a cikin sati uku  mabiyanka zasu iya canza shafi izuwa wani wanda a koda yaushe yana sa sabbin abubuwa, yana da kyau ka ringa sa sabbin abu a kalla sau uku koh biyu a sati.


Shin kana da wani hanya wajen ganin blog naka ya zama daya daga cikin shafuka masana?? zamu so muji ta bakinka dan allah a ajiye a shashin nunaa ra’ayi wato comment box 



-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Za'a iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan
Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

3 comments:

  1. Asslm, muna godiya sossai da sossai.
    Ina da bukatar koyon hada website, inada tambayoyi kuma da dama wadanda za'amin karin haske akansu.

    ReplyDelete
    Replies
    1. Waalaikumussalam, bismillah ina saura ronka

      Delete
    2. Alhamdulillah, Insha Allahu Zan Tuntubeka Ta Facebook Da WhatApp Gabadaya.
      Allah Ya Kara Basira.

      Delete

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *