Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Ma’anar Google Adsense, yanda ake amfani dashi da yanda ake samun kudi dashi bisa rubutun ra’ayin kai a yanar gizo.

Ma’anar Google Adsense, yanda ake amfani dashi da yanda ake samun kudi dashi bisa rubutun ra’ayin kai a yanar gizo.
Ma’anar Google Adsense, yanda ake amfani dashi da yanda ake samun kudi dashi bisa rubutun ra’ayin kai a yanar gizo.

Assalamu Alaikum yan uwa barkanmu da warhaka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabon shirin namu wanda yake zuwa muku kai tsaye daga nan mujallar Duniyan Fasaha insha Allahu yau zan tattauna ne game da abunda ake kira da “Google Adsense” ma’anarsa da kuma amfaninsa.

Me ake nufi da Google Adsense?

Google Adsense wani campanine wanda yake guda karkashin babban kuma sannanne kamfaninan wato Google, shi Google Adsense an kirkiresa ne saboda masu rubutun kansu a yanar gizo ko wanda suke amfani da shafukan yaran gizo a ayukan yau da kullum, shi Google Adsense yana amfani ne ta hanyar nuna tallan kaya ta bangare daban daban yakan iya fito wa a siffar rubutu, hoto ko kuma hoto mai mosti wanda aka fi sani da video.

Menene Amfanin Google Adsense

Shi wannan kamfanin kamar yanda na ambata a baya yana aiki ne ta hanyar nuna talla a sifar hoto, rubutu ko kuma hoto mai mosti (video) wannan shafin yana daya daga cikin manya kuma sanannun shafuka wanda suke taimaka wa mutane masu rubutun kansu a yanar gizo samun kudi na asali. Wasu zasuyi mamakin abunda na fada eh gaskiya ne mutum yakan samu kudi na asali a yanar gizo ta hanyoyi daban daban wanda zanyi bayanin su a yan kwanaki masu zuwa, sai dai duk hanyoyin ba su zuwa cikin sauki suna bukatar aiki tukuru kamar dai komai a rayuwa bazaka zauna jiran kudi yazo neman ka ba sai dai ka fita ka nemi aiki dan samun kudin kashewa haka zalika aiki a yanar gizo.

A gaskiya wannan ba sabuwar hanya bace an jima ana samun kudi a yanar gizo sai dai mune hausawa bamu san dashi ba amma wasu shafukan suna amfani dashi misali Duniyan Fasaha, bbc hausa, aminiyata, alumata da dai sauransu, a koda yaushe in muna bukatar abu da ya shafi nema a yanar gizo mukanyi yunkuri dubawa a Google Search wajen neman sa musamman idan ya shafi harkar boko, idan muka nemi abu misali “yanda za’a rage zubar gashin kai” in har da harshen turanci zamu duba wannan Kalmar a yanar gizo zamuyi la’akarin cewa shafuka sama da dari ne suka rubuta mafitar wannan matsalar amma shin ka/kin taba tambayar kaka/kanki maisa ba shafi daya kawai ya kamata a samu wannan amsar ba? Maisa shafuka da dama suka rubuta hanyoyin magance wannan matsalar? sannan kuma maisa kowa yayi nasa bisa fahimtarsa? Shin ka taba bawa kan ka/ki wannan tamabayar ko amsa a matsayin ka/kin a dan/yar boko? To a hakikanin gaskiya zan iya fadan cewa yawanci shafukan da ake rubuta su da harshen turanci ana yinsu sabonda kudi kuma Alhamdullilah suna samu shine gaskiyar maganan.

Yanda ake samun kudi ta hanyar amfani da Google Adsense   
   
Yana daya daga cikin manyan hanyoyi da ake bi wajen samun kudi a yanar gizo, za,a samu kudi ne ta hanyar sanyasa a shafin rubutun kai (blog/website), za ka/ki iya zaban nauo’I daban daban na girma wanda ya dace da shafinka sannan ka samar da wani code wanda zaka sa a shafinka dan nuna tallace tallace. Zaka samu yan wasu canji ne ta hanyar amfani da google adsense kawai in har mutum ya danna wannan tallace tallace da akeyi a shafinka. Google Adsense suna amfani da saka kaine (roboot) wanda sukan karanta abunda kake rubutawa a shafinka koda wani yarene, sannan zasu samar da talla wanda ya dace da abunda kake rubuta wa sai su saka ba lallai bane su sa abunda ranka ke so sai dai baza su nuna kayan tsiraici, batsa ko abu makamancin haka.

Yaya zanyi na samu kudina Cikin ajihu?   

Google de kamfanine da suka wuce tsanmaninka saboda suna da ma’aikata sama da 50 a kowace kasa a fadin duniyan nan dan haka samun kudinka ba abun damuwa bane kawai dai bisa dokar su dole sai kudinka ya kai dala 100 wato $100 wanda ya kama naira dubu talatin da shida N 3600 a yanda canji dala yake a yau ba lallai ya zauna a haka ba zai iya fin haka ko kuma ya zama kasa da haka saboda ya danga nane da canjin dala. Google Adsense suna tura kudi a bisa hanyoyi guda biyu a nan Nigeria na farko shine ta hanyar cheque wanda suke turawa ta hanyar sako, za,a ba mutum ya kawo maka har gida in dai kana cikin gari a kowace jiha a cikin fadin duniyannan kuma yana zuwa ne a siffarsa na dalla wanda zaka kaiwa zuwa banki sannan a canza maka zuwa kudin kasarka wanda zai iya daukan yan wasu kwanaki. Sai na biyu wanda shine banki, sukan iya turama kai tsaye zuwa account naka dake banki in dai ka/ki cika sharrudansu wanda zamuyi bayanin su a kwanaki masu zuwa.

Wace matsalece zan iya fuskanta wajen fara aiki da adsense?


Eh toh babban kalubalen da zan iya cewa zaka/ki fuskanta da fari shine wajen amincewa da shafinka a hakikanin gaskiya a yanzu Google Adsense basu karban shafukan da ake rubuta su da harshen hausa ba ma hausa kadai ba tare da wasu harshunan, suna karban harshuna guda sha daya ne kacall duk fadin duniyan nan wanda ya hada da turanci amma wannan ba mastala bane in dai ka iya rubuta abu mai ma’ana da harshen turanci zasu iya karbanka In har kuma ka samu karbuwa a wancan shafin naka na turanci zaka iya amfani dashi a kowani irin tsafine koda kuwa yana dauke da wani yarene wanda basu amince ba sai dai kawai karka sa abunda suka tsana misali kayan batsa, iskanci, yanda ake sace kayan wani ko wata, yanda ake hacking da dai sauran wasu kayan almundaha wanda basu dace ba.  


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *