Assalamu alaikum Uwargida. Yaya iyali? Tare
da fatan a na lafiya. A yau na kawo muku yadda ake miyar karkashi da kubewa
danya. Wannan miyar dai bata cika son yawan kayan hadi ba sannan kowace mace da
yadda take tata miyar karkashin. Wata karkashin zallah kawai take girkawa. Amma
idan har ana son aci miyar tayi dadi sosai kyawunta a hadata da kubewa danya domin
jin ainihin gardin miyar da kuma dadinta. Don haka na kawo muku yadda ake miyar
karkashi hade da kubewa danya domin sanya kunnen maigida motsi. A ci dadi
lafiya.
Abubuwan da ake bukata
==>
Ganyen karkashi
==>
Kubewa danya
==>Tokar
miya ko kanwa
==>
Attarugu
==>
Bandar kifi
==>
Nama
==>Albasa
==>
Danyar tafarnuwa
==>
Garin citta
==>
Magi
Hadi
A kankabe ganyen karkashin tsaf sannan a yayyanka
shi kanana sosai. A samu kubewa danya a yayyankata sannan a saka a turmi a daka
ta tayi laushi sosai. In kuma da kanwa za’ayi miyar sai a daka tare da kanwa
kadan. Sannan a kwashe a ajiye a gefe. A daka attarugu da tafarnuwa sannan a
kwashe. A wanke bandan kifi da ruwan dumi a cire kayoyin sannan a yayyanka
albasa kanana.
A daura ruwa a tukunya sannan a tafasa nama
har sai yayi laushi. Sai a kara ruwa kadan akan romon naman sannan a zuba
yankakkiyar albasar da jajjagaggen attarugu da garin citta da bandan kifi har
sai sun tafasa sannan a dauko kubewar da aka daka a zuba a rika gaurayawa har
sai ta fara nuna sannan a dauki karkashin a zuba a dauki maburgi a buga sannan
a cigaba da juyawa. Idan har ba’a sanya kanwa a miyar ba, a wannan lokacin
yakamata a sanya tokar miyar sannan a jika magi ya narke a zuba sai a cigaba da
gaurayawa har sai dandanon ya fito sannan a sauke. Za’a iya cin wannan miyar da
tuwon semo.
you are welcome
ReplyDelete