DON ME KAIMA BA ZAKA HADA SHAFIN RUBUTU NA KANKA BA? |
Dan Uwa mai ka/ki ke jirane da haryanzu ba ka/ki bude shafin ka/ki na rubutun kai a yanar gizo ba? Ko kasan cewa wannan abu ne mai matukar sauki wanda baya bukatar sai ka zama wani kwararre ta fannin kwamfuta kafin ka yi shi? Ina gayyatarka da kuma ke ‘yar uwa da ku shigo daga ciki. Idan ba’a manta ba munyi sharhi akan yadda matasanmu na yanzu ke yawan bata lokutansu a saman internet ba tare da sunyi wani abu wanda zai amfanesu ba kuma bazai amfani kowa ba. Sannan kuma mun kawo mu hanyoyin da za’a iya bi domin amfani da wannan lokutan da muke batawa a yin chatting ko kuma wani abu mai kama da hakan a saman Internet wanda baya tsinana mana komai sai asaran kudi. Insha Allahu yau zamuyi bayanine akan shafin rubutun kai a yanar gizo tare da amfaninsa.
Shi dai “Web Designing” wanda kalmane a turance wanda ke nufin hanya da ake bi wajen hada ko kuma gina shafin yanar gizo wato Website. Harkar gina Website ta samo asali ne tun daga lokacin da aka kir-kiri yanar gizo ita kanta -wato shekaru da dama da suka gabata. A wancan lokacin gina website abune ne musamman saboda sai masana da kuma kwararru ta fannin ilimin kwamfuta ne kadai ke iya yinsa, saboda komai ana yinshi ne da yaren da kwanfuta ke fahimta wanda aka fi sani da Programming a turance wanda kuma ba kowa ne ya iya ba ko a cikin masana kwamfutar. To yau gashi ci gaban zamani ya kawo mu, gina website ya zama wani abu mai matukar sauki, saboda a yau zaka sami wanda bai da ilimi akan kwamfuta zai iya hada website nashi na kanshi cikin yan wasu dakikai.
A wancan lokaci duk wani abu da kake so a matsayin suran shafin ka (website) to dole ne ka rubuta sa bisa fahimtar kwanfuta wanda aka fi sani da “Code” a turanche (programming). Amma a yanzu komai an riga anyi maka sai dai kawai ka dauka ka dora inda kake bukata ba tare da bukatar rubuta komai ba na programming. Wannan tsarin da zaka iya gina abu ba tare da kayi Coding ba shi ake kira da Drag-And-Drop a turance.
Akwai abubuwa da dama da muke bata lokutanmu akan saman Internet alhalin kuma zamu iya amfana daga garesu domin samun abin yi. Mafi yawanci wadannan abubuwan sun hada da:
1. Sharhi akan al’amuran Yau da kullum
Akwai mutane da dama wadanda sanannu ne ta bangaren bayyana ra’ayoyinsu akan harkokin yau da kullum da kuma fannuka daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. Hanya mafi sauki wadda wadannan mutane zasu iya sanar da al’umma matsayarsu akan wani lamari da ya kunno kai shine ta hanyar amfani da shafin yanar gizo, a inda cikin kankanen lokaci zasu janyo hankullan mutane da dama bayyana ra’ayinsu akan wannan lamari da ya taso, tare da fadakar da su akan abin da suke tunanin ya dace. Akwai da dama daga cikin matasannmu wadanda kwararru ne ta wannna fanni, to don ba zaka hada website dinka ba a mai-makon ko da yaushe kana a saman Facebook wanda babu ta inda kake karuwa da hakan.
2. Tallata Hajarka
Wani abu wanda ba kasafaye mutanenmu suka gane alfanunshi ba shine hada ma kamfaninsu ko kuma sana’arsu website da kuma tallata hajojinsu a shafinsu na yanar gizo. A mai-makon ka kashe makudan kudi wajen kai talla a kafafen yada labarai, wacce ba ma kowa ke sauraronta ba, hanya mafi sauki shine ka kir-kiri shafinka na yanar gizo inda zaka tallata hajarka ga dubban mutane ba tare da ka kashe sisin kobo ba. Dama daga cikin mutane masu sana’a suna daukar yin chatting a matsayin wani abu wanda zai debe musu kewa idan sunje kasuwa, musamman ma idan babu ciniki. Shin don mi ba zakayi amfani da wannnan dama ba wajen tallata ma mutane irin hajarka a saman Internet din?
Duk wasu manya-manyan kamfanunnuka da ka sani kamar su Konga , Dealdey , Dangote, da dai saurnasu, zaka ga cewa duknansu suna da website inda suke tallar kayansu a lokaci guda kuma suna mu’amala da kwastomominsu. Shiga Kasuwa
3. Ilimantarwa
Akwai mutane da dama da suka sadaukar da lokutansu domin ilimantar da sauran mutane a addinance ko kuma a zamanance. A mai-makon ka dogara da kafar Facebook kadai, kaima zaka iya yin website dinka don fadakar da mutane. Akwai malamai da kuma masana fannoni daban-daban da kan bude shafinsu a yanar gizo domin ilimantar da mutane akan fannoni da dama. Akwai malaman addini kamar Sheik Aminu Ibrahim Daurawa, da makamantansa, da ke da website inda ko dai su rika amsa tambayoyin al’umma ko kuma su rika sanya wasu tafsirai da suka gabatar. Akwai kuma masana da dama da kanbude shafin su a Internet don su sanar da mutane wani ilimi na musamman kamar yadda ake hada wasu abubuwa da dai sauransu.
4. Nishadantarwa
Akwai mutanen da su kuma abinda suke da sha’awa akanshi shine abubuwan nishadantarwa kamar wasana kwaikwayo, fina-finai, da dai sauransu. Wasu mutumen kuma zaka ga su dama can Allah ya halitta su mutune ne masu ban dariya da kuma sanya mutane raha. A lokuta da dama wadansu daga cikin wadannan mutanen sukan hada website dinsu domin nuna ire-iren wasannin barkwancinsu wanda zai baiwa mutane dariya, a yayin da a gefe guda kuma suke samun makudan kudade ta hanyar mutanen da ke ziyarar wannan shafin nasu. Misalin wadannan mutane sune Mark Angel da kuma Basket Mouth.
5. Labaran Wasanni
Zaka ga da dama matasanmu suna maida hankali sosai a bangaren harkokin da suka shafi wasanni. Wasu daga cikin wadannan matasa masu hikima sukan yi amfani da wannan dama su kir-kiri website domin mabiya wani club kamar Arsenal, Manchester, Real Madrid, Barcelona, Bayern Munich da dai sauransu. Ta hanyar mutanen da zasu rika tururuwa zawa wannan shafi, shi wannan matashi mai hikima zai iya samun makudan kudi na gaske. Muna yin abubuwa da dama wadanda ya kamata ace muna amfani da kafar internet domin gabatar dasu. Dalilan da zasu iya sanya ka ko kuma su sanya ki gina website basa da iyaka. Duk wani abu da kake tunanin zai iya janyo hankullan jama’a to abu mafi sauki da zaka iya janyo mutanen nan shine ta hanyar amfani da Website. A inda kai kuma zaka samu alheri mai yawan gaske ta hanyar tara wadannan mutane.
A post namu ta gaba, in Allah yaso, zamu kawo muku alfanun ko kuma amfanin hada website naku na kanku da kuma yanda zaku amfana daga gareshi. Ku kasance tare damu. Ga duk mai wata tambaya sai yayi comment da tambayarsa a nan kasa. Ga dukkan mai bukatar samun darasinmu kuma ta hanyar Whatsapp shima sai yayi comment da Lambar sa.
No comments:
Post a Comment