A duk ranar 14 ga watan Nuwamba ne aka kebe a
matsayin ranar masu ciwon Siga “Diabetes na duniya. Kwararrun likitoci a fanin
ilimin ciwon Siga sun bayyana cewa ba yawan shan zaki ke jawo cutar Siga ba. Wani
malami a jami’ar Legas dake koyarwa a sashen koyar da aikin likita, Ifedayo
Odeniyi, yace cutar siga na kama mutum ne idan aka samu matsala da wasu daga
cikin ababen da ke sarrafa abincin da muke ci a Shi Insulin ya na aiki ne a
jiki wajen tace sinadarin ‘Carbonhydrate’ dake cikin abincin da muke ci don samar
wa mutum kuzarin da yake bukata a jiki.” Ya kuma kara da cewa rashin aikin sa
‘Insulin’ yadda ya kamata ne ya ke sa a kamu da cutar siga. Bayan haka kuma ya
yi kira ga mutane da su yi watsi da camfin da ake yi wai shan zaki ne ke kawo
cutar siga.
Ya
ce hakan ba gaskiya bane.
” Likita ya ce saboda irin wannan camfe-camfe
ne ya sa mutane ke hana kansu cin abinda ya kamata don samun kuzarin da suke
bukata a jikin su.” Ya ce tabas yana da mahimmanci idan mai dauke da cutar siga
na kiyaye sharuddan da ya shafi irin abincin da ya kamata ya ci, amma haka ba
yana nufin kada mutum ya hana kan sa cin abincin da ke da sinadarin ‘Carbonhydrates’
saboda samun kuzari a jikin su.
Likita Odeniyi ya ce cutar siga yakasu kashi
kashi; Akwai wanda shi Insulin baya aiki kwata kwata a jikin mutum wanda ake
kira da ‘Type 1 diabetes’ sannan akwai wanda shi insulin din yana aiki amma ba
yadda ya kamata ba wanda ake kira ‘Type 2 diabetes’ shine mafi yawan ‘yan
Nijeriya ke fama da shi.
Ya ce alamomin cutar su hada da yawan jin yunwa,
yawan yin fitsari da sauransu. Bayan haka Oladimeji Agbolade ma’aikacin
kamfanin sarrafa magunguna dake kasar Faransa ‘Sanofi ’ya ce kula da masu dauke
da cutar siga na da matukar wuya ganin yadda magungunan cutar ke da tsadar
gaske.
No comments:
Post a Comment