Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Miyar karkashi da kubewa

Miyar karkashi da kubewa

Assalamu alaikum Uwargida. Yaya iyali? Tare da fatan a na lafiya. A yau na kawo muku yadda ake miyar karkashi da kubewa danya. Wannan miyar dai bata cika son yawan kayan hadi ba sannan kowace mace da yadda take tata miyar karkashin. Wata karkashin zallah kawai take girkawa. Amma idan har ana son aci miyar tayi dadi sosai kyawunta a hadata da kubewa danya domin jin ainihin gardin miyar da kuma dadinta. Don haka na kawo muku yadda ake miyar karkashi hade da kubewa danya domin sanya kunnen maigida motsi. A ci dadi lafiya.

Abubuwan da ake bukata
          ==> Ganyen karkashi
          ==> Kubewa danya
          ==>Tokar miya ko kanwa
          ==> Attarugu
          ==> Bandar kifi
          ==> Nama
          ==>Albasa
          ==> Danyar tafarnuwa
          ==> Garin citta
          ==> Magi

Hadi

A kankabe ganyen karkashin tsaf sannan a yayyanka shi kanana sosai. A samu kubewa danya a yayyankata sannan a saka a turmi a daka ta tayi laushi sosai. In kuma da kanwa za’ayi miyar sai a daka tare da kanwa kadan. Sannan a kwashe a ajiye a gefe. A daka attarugu da tafarnuwa sannan a kwashe. A wanke bandan kifi da ruwan dumi a cire kayoyin sannan a yayyanka albasa kanana.


A daura ruwa a tukunya sannan a tafasa nama har sai yayi laushi. Sai a kara ruwa kadan akan romon naman sannan a zuba yankakkiyar albasar da jajjagaggen attarugu da garin citta da bandan kifi har sai sun tafasa sannan a dauko kubewar da aka daka a zuba a rika gaurayawa har sai ta fara nuna sannan a dauki karkashin a zuba a dauki maburgi a buga sannan a cigaba da juyawa. Idan har ba’a sanya kanwa a miyar ba, a wannan lokacin yakamata a sanya tokar miyar sannan a jika magi ya narke a zuba sai a cigaba da gaurayawa har sai dandanon ya fito sannan a sauke. Za’a iya cin wannan miyar da tuwon semo.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

1 comment:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *