Barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon Shirin namu na fasaha wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha. Dafatan an shiga sabon shekara cikin koshin lafiya, Allah shi bamu ikon cin jarrabawar wannan shekaran Ameen!.
Insha
Allahu yau zamu maida hangene akan wani bangare na kwanfuta na musamman wadda akewa
lakani da “Keyboard” a turance wato wajen rubutu. Akwai abubuwa bila adadin da
muke amfani dasu a yau da kullum wadda yawancin mu bamusan dalilin da yasa aka
yi su a yadda suke ba ko kuma yadda muke ganin su ba.
Karanta: Abubuwa Da Za’ayi La’akari Dasu Kafin Siyan Kwanfuta
Mafi
akatsarin lokuta ba a san cewar akwai dalilan da ya sa aka wallafa wadannan
abubuwa ba, wasu ma tunaninsu kawai rashin kan gado ne, ko kuma rashin basira
ne ba su san cewar akwai abubuwan da akayi Nazari akai kafin yin hakan ba.
Hargitsa Wajen Rubutun (keyboard) din kwamfuta
A
zamanin data gabata lokacin da ake amfani da tafireta a matsayin abin rubutu
mafi sauki. Wajen rubutunsa wato keyboard din a shirye yake yadda harufan
turanci suke wato daga A har zuwa Z.
Wannan
ya sa masu amfani da ita ke saurin lakantar inda kowane harufa suke, don haka yasa
sai suka rika yin sauri wajen rubutu fiye da yadda kwakwalwar za ta dauka, har
ta kai ga tafireta na yawan lalacewa lokaci zuwa lokaci.
Karanta: Yadda Za’a Magance Rashin Tashiwar Kwanfuta A Kan Lokaci
Hakan ya sa kwararru sukayi Nazari mai kyau dangane da matsalar da ake fama da shi daga baya suka yanke shawarar hargitsa wajen rubutu wato keyboard a turance, aka kuma kirkiro kwamfutar da muke amfani da ita yau aka kuma yi keyboard dinsa a hakan, don magance wannan matsalar.
No comments:
Post a Comment