Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Abubuwa 5 Da Za Su Sa Budurwa Ta So Ka Cikin Ranta

Abubuwa 5 Da Za Su Sa Budurwa Ta So Ka Cikin Ranta

Insha Allahu yau a Duniyan Fasaha zamu mai da gani  ga ’yan mata da masoyansu da irin abubuwan da suka fi so a yau da kullum domin dorewar soyayya a tsakaninsu wadda zai kai ga aure.

Mun tattauna da ’Yan mata bila adadin wadda suka bayyana mana wasu abubuwan da ke sa su karkata tare da samun nutsuwa da masoyansu maza.

Ga wasu manya biyar daga cikin abubuwan da ’yan matan suka fi kaunar su samu daga masoyansu, wadanda idan namiji ya yi musu, son shi kan shiga har ya mamaye birnin zukatansu:

 

Karanta: Illar Aikata Wasu Abubuwa Bayan Cin Abinci

 

Ba da cikakken lokaci: Budurwa na son ta ga masoyinta yana ba ta lokacinsa ta hanyar tuntubar ta domin sanin halin da take ciki. A cewar wata tana son ganin masoyinta wajen kasancewa tare da ita haka zalika kuma ya kasance mai sauraronta a-kai-a-kai domin yin hakan na kara gida kauna sosai a cikin majalisar zuciya.

 

Ta kara da cewa; babu abu mafi muni a wurinta irin ta ga ba ta samun lokacin daga masoyinta, mahadin rayuwarta, farin cikinta, abin kaunarta.

 

Yabawa Da Ambato: Amina Ibrahim ta ce tana son masoyinta ya kasance mai yaba alheri da da kuma komai da ya shafe ta a koyaushe. Ta ce masoyinta ya kasance mai godiya da kuma yabawa da kananan abubuwan da take yi masa, baya ga manyan yana da muhimmanci a gare ta. Kadan daga cikin abubuwan da ’yan mata ke bukata ke nan daga masoyansu domin soyayya mai armashi.

 

Kulawa: Wasu ’Yan mata sun bayyana cewa suna matukar kaunar su ga namiji yana nuna ya damu da su a aikace kuma a kowane lokaci. Wannan kuma ya hada kuma da kyautatawa.

Aisha Abdulkarim ta ce zuciya na kaunar mai kyautata mata don haka kyautatawa na daya daga cikin muhimman abubuwan da take bukatar ta samu daga mutumin da take so.

 

Karanta: Illoli Goma(10) Da Rashin Shan Isasshen Ruwa Ke Haifarwa Ga Lafiyar Jiki

“Ina so koyaushe ya zama yana kyautata min saboda hakan yana kara dankon soyyaya,” inji Aisha.

 

Zara Idris, ta ce, “ina son namiji ya rika kyautata min saboda ni ma ina kyautata mishi. Ai kama tudinu tudan,” inji ta.

Sakin hannu: ’Yan magana kan ce yaba kyauta tukwici, Hafsat Salis ta ce tana son masoyinta ya kasance mai kyauta da sakin hannu.

Hafsa ta ce, ita a wurinta kyauta ba ta kadan kuma duk kyautar da aka yi mata tana matukar faranta mata rai da kara martabar wanda ya yi mata ita.

Matashiyar ta ce kyauta na kuma kara dankon soyayya, “inda a yawancin lokuta za ka ji kana shaukin ganin masoyinka kana kuma kewar sa kana tuna shi ta hanyar kyaututtukansa da ke tare da kai.”

Sauraro: Suna kuma son namiji ya rika sauraron su da sauraron damuwarsu sannan ya ba su shawara ko taya su da addu’a game da halin da suka tsinci kansu a ciki.

Fatima Abubakar na cikin masu son hakan daga wurin mosayinta, ta ce tana son mutumin da za ta iya dogaro da shi a koyaushe musamman idan tana da bukatar shawarwari ko samun kwarin gwiwa.

 

Karanta : Amfanin Cin Namijin Goro

 

Ta ce abin da take so shi ne, ya zama wanda in ta bayyana masa damuwanta zai saurare ta da kyau kuma ya ba ta kyakkyawar mafita.

To samari, kun ji daga bakin masu ita, da fatan za ku dabbaka wadannan abubawan ga masoyanku.mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *