Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Illar Aikata Wasu Abubuwa Bayan Cin Abinci

Illar Aikata Wasu Abubuwa Bayan Cin Abinci

A hakikanin gaskiya akwai abubuwa bila adadin da muke aikatawa da zarar mun gama cin abinci wadda ke kawo matsala da illa ga lafiyar jikinmu. Wasu na sane da matsalolin dake tattare da hakan amma saboda ganganci suna cigaba da aikatawa, haka zalika wasu kuma suna yine bisa rashin sani.

 

Insha Allahu yau a Duniyan Fasaha zamu tattauna ne a kan wasu dabi’u wadda mukeyi muddin mun gama cin abinci wadda ke kawo mana matsala ga lafiyar jiki. Wasu daga ciki sun hada da:

1.==> BARCI: Wannan na daya daga cikin manyan da’biu da mukeyi da zarar ciki ya koshi, Mutane da dama na yawaita yin barci da zarar sun gama cin abinci wadda hakan na sa kumburin ciki, muddin mutum ya sabawa kansa haka yana sa barci na babu gaira babu dalili a lokutan da basu kamata ba.

Bincike ya nuna cewa masu yawan yin barci da zaran sun gama cin abinci suna saukin samun cutar bugun zuciya (stroke) da kuma hawan jini. Yana da kyau a dakata akalla sa’a 2 bayan cin abinci kan a yi barci domin hakan zai taimaka wa wasu bangarori na jiki wajen narka kayan abinci da aka shigar.

2.==> SHAN SHAYI: Shayi na da muhimmanci amma shan sa bayan an gama cin abinci yana kawo karancin sinadarin ”Iron” wanda ke iya sanya jiri da rashin kuzari da gajiya, kamata ya yi a sha shayin kan a ci abinci. Har wayau karancin” iron” na iya kawo cutar (anaemia) da jikin dana dam.

3.==> SHAN SIGARI: Sigari nada sinadarin” nicotine” wadda ya ke haifar da ciwon daji da huhu. Wannan illa ta shan sigari tana zama ninki goma idan aka sha sigarin da zarar an gama cin abinci ko kuma jin kafin aci. Har wayau shan sigari bayan gama cin abinci yana hana narkewar abincin da wuri. Idan ya zama dole sai an sha sigarin to a bari sai bayan kamar sa’a 2 (2 hours) bayan gama cin abincin domin gujewa wasu matsalolin.

4.==> WANKA DA RUWAN DUMI: Yin wanka da ruwan dumi bayan gama cin abinci yana tsinka jinin jiki wanda hakan na hana jini isa ga tumbin dan adam. Hakan yana kawo cikas ga narkewan abincin da aka gama ci sannan hakan na iya haifar da cututtuka masu yawan gaske.

5.==> CIN ‘YAYAN ITATUWA: ‘Yayan itatuwa na dauke da sinadarai da suke daukan tsawon lokaci kan su narke su bi jikin dan adam. Shan su ko cinsu kan a ci abinci zai bada damar amfana da sinadaran gina jiki da suke dauke da su. Shan su kuwa bayan gama cin abinci na jinkirta narkewan abinci da kuma yawan gyatsa.

Illolin aikata wasu abubuwa Kenan bayan cin abinci wadda mukeyi a koda yaushe yana da kyau mu gujewa yin hakan domin fadawa cikin tsaka mai wuya. Allah shi bamu damar kiyayewa ya kuma karemu daga kamuwa da wasu cututtuka.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *