Assalamu Alaikum yan uwa barkan
mu da war haka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin sabo shirin namu wanda
yake zuwa muka kai tsaye daga mujallar Duniyar Fasaha, Insha Allahu yau zamu
koyi yanda ake goge sakon da ake tura bisa kuskure koda kuwa ya isa wajen wanda
aka tura wa.
MATAKAI BIYAR DA ZAKA BI WAJEN GANIN BLOG NAKA YA ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAFUKA MASANA
Tare Da Muhammad Abba Gana
{Jikan Marubuta}
A zamanin namu na yanzu mutane da dama suna aiki da blog ne
kawai da manufar samun kudi, ko hanyan samun kudi wasu kuma suna aiki dashi ne
saboda hanya ce da zai taimaka sosai wajen kasuwanci.
Haka kuma ma danfara sukan
samu hanyar danfaran mutane saboda yanda mutane suka sha’afa da aiki dashi. Sau
da dama mutane sukanyi korafin cewa basu samun mutane suna ziyartan shafinsu
wanda sun bi duk wata kayatacciyar hanya daya dace a abi dan ganin mutane
suna da masaniya a kanta.
Abu daya kamata mu sani shine yawan sa ran samun kudi
ta hanyan yanar gizo yana daya daga cikin abubuwan dayake janyo rashin ziyartan
mutane saboda bazaka sa ko kayi abunda ya dace ba kawai matsalar ka kaga dubban
mutane suna ziyar tan shafinka wanda hakan ba karamin abu bane kuma ba abun
gaggawa bane.
Yana da kyau ka kasance na musamman in kana son cimma manufarka
na zama daya daga cikin shahararrun masana kan yanar gizo ko kuma zama daya
daga cikin hamshakan mutane da suke samun kudi ta hanyan yanar gizo.
Maganar
gaskiya, akwai dubban hanyoyi da ake bi wajen ganin shafi ya riske mutane da
dama abu na farko ya kunshi abubuwa masu inganci, duk da cewar ba bangaren nan
zan tabo ba yau zan mayar da hankali ne game da asalin shi shafin wato sarki da
kansa wanda shine “abun dake ciki” ko yaya shafinka ya kasance misali gwani
wajen sura (design) yawan sa a wajen mutane a karshen mako abinda ke cikin
shafinka ne zai sanar da mutane manufanka,
ABUBUWAN DA KE SA MACE TA FITA DAGA ZUCIYAR MIJINTA
Tare Da Muhammad Abba Gana {Jikan Marubuta} A hakikanin gaskiya suna da yawa amma ga kadan daga ciki
RIKO
Riko
shine idan an aikatama wani laifi kabar abin a ranka ba tare da ka yafe ba
uwargida ta riki maigida a xuci sakamakon wani abu ko maigida yana sa ta fita
daga zuciyar miji duk sanda namiji ya yi miki wani abu yana sane ko bai sani ba
to ki samu wani lokaci da yake cikin nutsuwa ko yake cikin nishadi ki nuna masa
cikin tausasa harshe misali “wane kayi min kaza nasan in Allah ya yarda zai dau
kuskuren shi kuma za ki kuma shiga zuciyar shi
Cikakken Bayani Game Da Hosting Tare Da Amfanin Sa
Tare Da Muhammad Abba Gana {Jikan Marubuta}
A wasu lokutan mukanji sunayen wasu abubuwa daga yan uwa da abokan arziki ko kuma daga yanar gizo wadda kan zamo mana sabo sabili bamu taba jinsa ba ko kuma wasu sa’an mukan ji mutane suna yawai ta ambatan sunayen, wadda a hakikanin gaskiya bamu sansu ba balle mu san yadda suke aiki.
Yadda ake girka kazar Indiyawa
yadda ake girka kazar indiyawa |
Yadda ake girka kazar Indiyawa
Assalamu Alaikum Uwargida tare da fata ana
cikin koshin lafiya. Kamar yadda na saba fada muku, yana da kyau idan za a yi
girki a rika taba birni da kauye har da kasashen waje. Hakan ya sa a yau na
dauko muku irin girkin mutanen Indiyawa ‘chicken curry’. Tare da fatan za a
gwada shi wata rana ga mai gida ko kuma ga manyan gobe domin kara ilimantar da
su a kan abincin kasashe waje.
Abubuwan
da za a bukata
·
Man zaitun
·
Albasa
·
Kori
·
Madara
(nonon da aka tafasa)
·
Gishiri
·
Dakaken
masoro
·
Heaby
cream (za a iya samu a manyan shagunan da ke sayar da kayan girke girke)
·
Kaza daya
·
Timatir
guda daya.
·
Ganyen
kori.
Hadi
A wanke kaza sannan a silala ta da kayan
kamshi da albasa da magi har sai ta yi laushi sosai. Sannan a sauke ta huce. A
sami wuka a daddatsata kanana sannan a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta
sannan a zuba man zaitun, idan ya yi zafi sai a zuba albasa sannan a yi ta
juyawa kamar na tsawon minti bakwai sannan a zuba kori kamar cokali biyu na cin
abinci, sai a ci gaba da juyawa na tsawon minti daya.
Sannan a zuba tafasashiyar madara a cikin
hadin tare da ‘cream’ da gishiri da magi da kuma yankakken timatir kanana sosai
sai a ci gaba da juyawa.
A dauko kazar da aka riga aka daddatsa a zuba
a cikin miyar sannan a rufe na tsawon minti biyu kacal sannan a sauke. Za a iya
sanya ganyen kori idan ana da bukata. A tafasa farar shinkafa sannan a dauko
hadin miyar Indiyawa a zuba a kan shinkafar tare da hada shi da jus din lemun
zaki. Hmnnn! A ci dadi lafiya!