Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Abubuwa goma (10) da Man Zaitun keyi da yanda ake amfani dashi

Abubuwa goma (10) da Man Zaitun keyi da yanda ake amfani dashi 

Amfanin Man-Zaitun guda 10 (Olive oil/ Olea europea ) wani irin nau’in mai ne da ake samarwa daga ‘ya’yan itaciyar zaitun (Olive tree). Ana amfani dashi wajen girki, gyaran fata, magani, hada sabullai da kuma man-fitila (a gargajiyance). Man-zaitun ana amfani dashi a ‘kasashen duniya da dama, musamman kasar Spain, France (Faransa), Italy, Greece (kasar Girka), Syria, Lebanon, Egypt, Libya, Tunisia, Algeria, Morocco da sauransu. Toh amma kasashen da suka fi yawan amfani dashi sune Portugal, Spain, Italy da Greece. Daga shekara ta 2000 zuwa ta 2009, kasashe 3 da suka fi yawan samar dashi sune: 1. Spain 2. Italy 3. Greece. Kasar Syria itace ta 4, sai mai-bimata kasar Tunisia, a matsayin ta 5.Sabili da muhimmancin itaciyar zaitun, Allah Madaukakin sarki, Mai -halittu ya ambace ta a cikin Al-Qur’ani Maigirma – Surat At- Tin da Surat An- Nur. Man-zaitun nada amfanin sosai ga lafiyar ‘dan adam. Binciken ilimin kimiyya ya nuna cewa yana da amfani kamar haka:

==> Yana ‘karfafa garkuwar jiki (domin yaki da kwayar cutar biras, bacteriya, fangas (fighting virus, bacteria, fungus etc.) da sauransu. Wadannan cututtuka suke haddasa matsalolin lafiya da dama, kamar irinsu ciwon-anta, tetanus da cin-ruwa.

==> Yana da sinadarai masu bada kariya daga kamuwa da ciwon daji (rich in antioxidant subtances).

==> Kariya daga cututtukan zuciya – yana rage yawan sinadarin kolestirol (reducing high cholesterol) wanda idan yayi yawa a cikin jini yake da illa ga zuciya.

==> Rage hawan jini (reducing high blood pressure).

==> Taimako ga masu ciwon-suga (helping diabetic patients).

==> Kariya daga ciwon jiki (sanyin jiki) dana gabobi (anti-rheumatism & arthritis).


==> Inganta lafiyar zuciya (improving heart’s function esp. to older people whose hearts are weak due to aging) musamman ga tsofafi wanda zuciyar su ta fara rauni wajen aiki saboda tsufa. Yana gyara zuciya da quruciya.

==> Kariya daga ciwon daji dake shagar fata (protection from skin cancer).

==> Inganta lafiyar qashi. (improving bone health).

==> Inganta lafiyar kwakwalwa wajen koyon wani abu kamar karatu ko rike karatun, musamman ga manya (improving cognitive function) da sauransu. Ana iya amfani da man-zaitun kamar haka:
          - Asha cikin babban cokali sau 2 a rana – safe da rana, cokali daya a kowane lokacin.
          - Ayi girki dashi a matsayin man girki ko a zuba cikin abinci bayan girki.
          - Manshafawa kamar sauran man amfani na jiki.
          -Giris ga ma’aurata (sex lubricant). Bugu da kari, zai kuma bada kariya daga cututtuka.
          - Ciwon-kunne, digo 2 ko 3 na man a cikin kunne.

          - Da sauran wasu hanyoyin na inganta lafiya.
Tura Zuwa:

Abubuwa bakwai da ke sanya fata tsufa

Abubuwa bakwai da ke sanya fata tsufa

Abubuwa bakwai da ke sanya fata tsufa...

Kowane mai rai dole ne wata rana ya tsufa. Amma akwai abin da in aka yi wa fata zai sanya ta tsufa da wuri. Kuma dole ne mu yi iya kokarin barinsu. Abubuwa da suka hada da rashin bacci da yawan gajiya da amfani da kayan kwalliyar da ba ta dace da fata ba. Yawan shan taba da kuma yawan cin naman shanu bayan an bai wa shekara arba’in baya.

==> Gajiya: Yawan gajiya da shiga damuwa na matukar sanya fatar jiki tsufa. Idan mutum ya shiga damuwa, fatar na fitar da wani abu ‘cortisol’. Wannan ‘cortis’ din yana yi wa fata dameji. Sai a ga mutum ya tsufa da wuri. Shi ya sa sai a ga wanda yake cikin damuwa da talauci yana riga sa’anninsa tsufa da ke birni, kuma cikin jin dadi. Don haka sai a yi iya kokarin rage sanya kai tunani da damuwa.


==> Kayan kwalliya: Akwai wasu kayan kwalliya da ke dauke da sinadarai kamar su; zinc odide da dimethicone da propylene suna iya sanya fata tsufa, musamman idan an yawaita amfani da su. Wasu sinadaren suna bata fuska suna sa kaikayi daga nan sai fesowar kuraje har fuska.

==> Taba: Yawan shan taba na sanya tsufar fata da wuri domin wannan sinadarin da ke cikin sigari nicotine, wanda ke toshe magudanar jini. Shan tabar na sanya fata ta sake karfinta. A rage shan taba saboda tana janyo tsufar fata.

==> Yawan cin soyayyen abinci da cin abinci a kan kari ba don yunwa ba na sanya fatar jiki kiba, kuma hakan zai janyo fatar fuska cika, sai a ga mutum tsabagen kiba ya fi shekarunsa.

==> Yana da kyau mutum ya san irin nau’in fatarsa kafin ya yi amfani da kowane irin sabulu. Idan sabulu bai dace da fatar mutum ba, zai iya sanya tsufan fata.

==> A rage cin abinci mai dauke da mai, musamman idan shekaru sun ja. Bai kamata idan an kai shekaru arba’in a rika cin naman shanu ba. Yawan cin irin wadannan abubuwa yana janyo ciwon kafa da sanya mutum tsufa.

==> Yana da kyau a rika samun barci a kalla awa bakwai a kullum. Rashin samun barci a kan kari na sanya tsufa da wuri.
Tura Zuwa:

Abinci Kala 15 Da Ke Kara Karfin Kwakwalwa

Abinci Kala 15 Da Ke Kara Karfin Kwakwalwa

Muna sane da rawar da abinci mai kyau ke takawa wajen bunkasa lafiyar jikin mu da inganta ayyukan da gabbobin ke gudanarwa. Amma so da yawa mu kan manta da rawar da wannan abinci ke takawa wajen bawa kwakwalwar mu lafiya da karfin yin aikin ta. Kasancewa kwakwalwa a cikin koshin lafiya a koda yaushe ba karamin mahimmanci yake da shi ba duba da yanda babu sashin jikinmu da zai aikatu ba tare da ita ba.

Wannan Ya sa mujallar Duniyan Fasaha ta kawo muku Abinci kala 10 da ke kara karfin kwakwalwar mu, bugu da kari dukkansu muna da su a gida Nijeriya kuma suna da saukin samu.

1.        Kifaye masu dauke da sinadarin Omega 3 acids kamar Tuna Da Salmon
2.        Alayyahu
3.        Dafaffen Jijiyar Kurkum (Turmeric root)
4.        Gero, Masara, Alkama (whole grains)
5.        Man Kwakwa
6.        Agushi
7.        Farfesun Kashi (Bone Broth)
8.        Tumatir
9.        Piya (Avocado)
10.    Wake (Beans)
11.    Kwar fulawa
12.    Gyadar yarbawa (Walnut)
13.    Korayen ganye
14.    Gyada
15.    Strawberries


Dukkanin wadannan abinci na kunshe da sinadaran da ke kara karfin kwakwalwa, kara nutsuwa, rage mantuwa, su kuma ba wa kwakwalwa abincin da take bukata domin yin aikin ta yadda ya kamata. Da fatan za’a kara adadin wadannan abinci da ake ci a kullum.
 

 
Tura Zuwa:

Yadda Za Ki Yi Amfani Da Kurkum Wajen Gyara Fatarki

Yadda Za Ki Yi Amfani Da Kurkum Wajen Gyara Fatarki

Kurkum na dauke da sinadarai da dama kamar su, bitamin B6 da bitamin C da sauransu. Kuma yana rike fata yadda ba za ta zama sakakkiya ba. Amfani da kurkum na sanya sabuwar fata fitowa da wuri a inda tsohuwar ta sami rauni . Yawan amfani da hadin kurkum na sanya fata musamman ta fuska laushi da santsi da kuma haske. Don haka, ya kamata kada a manta da wannan kurkum idan an zo kwalliya. Hadin kurkum

==> A sami garin kurkum da zuma cokali daya da ruwan lemon tsami kwatan kofi: A kwaba susosai har sai sun yi laushi. Sannan a shafa a fatar fuska a bari ya jima na mintun a 15 sannan a wanke da ruwan dumi. Yin wannan hadin na hana kurajen fuska fesowa. Za a iya yin wannan hadin kamar sau daya ko biyu a sati domin samin ingantaccen sakamako.


==> Amfani da kurkum na rage gautsin fuska: A kwaba kurkum da nono ko kindirmo. Sannan a wanke fuska kafin a shafa hadin a fuska. A jira na tsawon mintuna 10-15 kafin a wanke. Za a iya jarraba wannan hadin a kullum bayan an yi wanka.

==> Idan ke mai yawan aiki a karkashin rana ce, ya kamata ki samu kurkum kadan da kindirmo mai yawa sai ki rika shafa wa a inda kunan rana ta bata fuska. kunan rana na sanya fuska ta zama kamar mai shafe-shafe don haka wannan hadin zai magance wadannan matsalolin.


==> Ko kun san cewa kurkum na magance bakar fatar karkashin hammata? To! A sami zuma kamar cokali daya sai a hada da ruwan lemon tsami kamar cokula 3-4 sai a zuba garin kurkum kadan sannan a kwaba a shafa a karkashin hammata a bari ya jima na tsakwon mintuna 10-15 kamin a wanke.
Tura Zuwa:

Gyara jikinki da koren ganyen Shayi


Gyara jikinki da koren ganyen Shayi


Koren ganyen shayi na da amfani a jikinmu, domin shansa na kara lafiya da kuma kara gautsin fata. Za a iya shafa ganyen shayin a fuska. Koren ganyen shayi na da amfani a jikinmu, domin shansa na kara lafiya da kuma kara gautsin fata. Za a iya shafa ganyen shayin a fuska.
Tura Zuwa:

Muhimmancin Ilimin Computer – Kowa ya iya allonshi ya wanke 2

Muhimmancin Ilimin Computer – Kowa ya iya allonshi ya wanke 2

Abun kamar almara. Dawo bangaren “na duke tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya taras” wato noma da kiwo, wadannan sana’o’i a wannan zamani za ka ga yadda na’urar Computer ta ke taimakawa wajen ganin inganci gona da abinda manomi zai shuka, da yadda ake yin taki, da yadda ake fitar da magungunan kwari, da dai makamantansu. A yau akwai Computoci wadanda suke sarrafa kayan gona, kamar irin computer da take tsotse ruwan jikin tumatiri ta kyafeshi a cikin dan kankanin lokaci, babu ruwanka da shanya da makamantansu. Idan kuwa muka zo bangaren kasuwanci, ai abin ba a cewa komai, ka duba hada-hada irin ta banki yadda abubuwa suka saukaka, a da, babu yadda za ka je wani banki ka ajiye kudi sannan kaje irin wannan banki ka cire kudinka, ballantana ace kaje wani gari ko kuma kaje wata kasa, ai babu hali. Amma a wannan zamani da ilimin computer ya yawaita, bama ka saka kudi a cikin account dinka ba, hatta saye da sayarwa za ka yi a duk inda kake so a duniya, kuma a kawo maka inda kake so, ba tare da kaje wurin ba, ko kayi magana dasu baki da baki ba, ta Computer za a gama komai, su nuna maka irin kayan da suke da su, da farashinsu, su kuma gaya maka idan har ka siya wadannan kaya kwana kaza za suyi daga kasa kaza zuwa kasa kaza. Koma ga kananan ‘yan kasuwanmu masu sayar da kayan taro da sisi sannan kuma masu son su kididdige cinikinsa, to, kaga abinda yafi dacewa da su itace Computer. Domin itace wacce komai yawan cinikin da akayi a rana ko shekara idan aka ce ta kawo lissafinsa za ta kawo ba tare da wani bata lokaci ba. Ba lissafi kadai za ta iya yi maka ba, hatta irin ribar da kake son ka samu zata fitar maka, zaka gaya mata kudin kaya, ka gaya mata kudin dako, ka gaya mata kudin abincinka da yaran shagonka, ka gaya mata adadin yawan kayan da ka siyo, ita kuma ta baka mamaki wajen fitar maka da taswirar yadda za ka sami cikakkiyar riba. Kai hatta abubuwan da ka siyar a baya ita Computer zata iya fitar maka da bayanai na ban mamaki, kamar ta gaya maka a shekaru talatin da ka ke kasuwanci shekara kaza kafi cin riba, sannan wata kaza kafi cin riba, sannan ta fitar maka da shekarar da kafi faduwa da rashin ciniki, sannan ta gaya maka kwastomanka da yafi kowa siyan kaya awurin ka da wanda ya siya kaya sau daya da sanda suka yi kasuwanci na karshe da abinda suka siya da kuma kudin da suka biya.


Sabo da haka, idan ka lura za ka ga cewar Computer wata makami ce da mutane suke amfani da ita wajen tafiyar da alamuransu na yau da kullum, sannan a wannan zamani da muke ciki a yanzu zai wahala dan adam yace zai gujewa amfani da Computer, domin na farko kusan mafi yawan mutane suna amfani da wayar tafi da gidanka (GSM), ga amfani da ATM wajen fito da kudi, da dai makamantansu, ballantana wanda yake da akwatin email, ko kuma yana amfani da dandali irin su Facebook ko twitter, ballantana wanda yake aikin jarida ko ma’aikacin asibiti da dai dukkan wanda rayuwarshi ta shafi harka da Computer. “Bama a nan gizo ke saka ba” ka duba yadda duk mutumin da yayi karatun zamani komai zurfin karatun da yayi sai ka ga ya hada da na Computer, kuma zai yi wahala ace mutum yana da ilimin Computer ko yaya yake yaje neman aiki ace ba a sa sunan shi a cikin wadanda za a tantance ba, musamman ace ya karanta wani fanni mai mahimmanci, ko kuma wata babbatar ma’aikatar da ta kera wani program ko hardware sun bashi shaidar cewar shi kwararre ne (Certification). Kamar mutumin da ya karanta fannin kasuwanci ya sami daraja ta biyu (Second Class) amma gashi ya iya amfani da Computer har yana da shaidar kwarewa akan Excel ko Peachtree wanda su wadannan software suna taimakawa wajen warware matsalar kasuwanci. To zai yi wahala yaje neman aiki ya zamanto ga wanda yake da daraja ta farko (First Class) amma bashi da wancan ilimin ace ba a dauke shi ba. Irin wadannan misalai suna da yawa, kamar mutumin da ya karanta fannin zane-zanen gidaje sannan ya zamanto bai iya amfani da computer ta fannin zane ba, kaga zai yi wahala a ce ga wanda ya karanta irin kwas na shi kuma ya san daya daga cikin program da ake zane dasu ace wancan aka dauka ba shi ba. To ashe idan har gaskiya ne Computer ta kewaye kusan ko ina a harkar mu ta yau da kullum, babu abinda ya fi dacewa illa mutum ya fahimci yadda zai sarrafa wacce yake tare da ita, ko da kuwa yaya kankantarta yake. Na san mutane da yawa ba da son ransu suke son a ce su kai aikin sirrinsu wajen Business Center ba, wajen da babu sirri, ba ka san waye zai karanta sirrinka ba, ga shi kuma kana da Computer a gida ko kuma a ofis amma abin bakin ciki ba ka iya sarrafa ta ba. Ka duba wani abin haushi “nama na jan kare” zaka samu hatta waya a wannan lokaci zaka ga mutane da yawa basu iya sarrafa ta ba, sai dai idan an turo musu da sako su kira wani ya duba musu. Bama wannan shine ya fi ban takaici ba, hatta ATM wanda ba a son wani ya san lambobinka guda hudu da kake amfani da su na sirri ka ciro kudi, sai kaga mutum duk sanda zai ciro kudi sai ya nemo wani sannan ya ciro mishi. Ashe idan haka ne ilimin sanin yadda zaka sarrafa Computer wajibi ne.
Tura Zuwa:

Muhimmancin Ilimin Computer – Kowa ya iya allonshi ya wanke 1

Muhimmancin Ilimin Computer – Kowa ya iya allonshi ya wanke 1
Muhimmancin Ilimin Computer – Kowa ya iya allonshi ya wanke


Ko ba a gwada ba an san linzami yafi karfin bakin kaza, domin mahimmancin computer da iliminta ya wuce a ce mutum bai sani ba. Domin ko ba a fada maka ba lura da yadda ta mamaye kusan mafi yawanci abubuwan mu na yau da kullun. tun daga makarantunmu, ma’aikatunmu kasuwancinmu, asbitocinmu, gidajen yada labarai da makamantansu, dukkanin su za ka samu a na amfani da ita Computer.

Kusan a wannan zamani, computer ta samar da sauki wajen tafiyar da alamura ga dan adam. Kama daga rubutun takardar wasika zuwa takardar sanarwa ta wajen aiki ko takardar notice, takardar biyan albashi da lissafin kudaden kasa dayin kasafin kudi, hada da harkar hada- hada, da bayanai na kididdiga da fitar da kudade a bankuna, duk computer ta kawo sauki ta kowanne fanni.

Haka kuma computer ta samar da sauki wajen tafiyar da harkar banki, ka duba ATM yanda yake, computer take karbar cheque ko kuma ta baka kudi, ko kuma ta cireshi. Ga wadanda suke sayan kaya a kasashen waje suna amfani da computer wajen duba yanayin kayan su da kuma sannin a wane wuri kayan suke da kuma lokacin da kayan zasu iso. Ta bangaren kasuwanci, idan ka zuba wa computer bayanan harkar kasuwancin ka, kayan daka siyo, ka ware mata kudaden wahalhalunka, kama daga kudin abinci, kudin sallamar ma’aikata, kudin dauko kaya, kudin shago da kudin wuta za ta fitar maka da ribarka ko kuma faduwarka a dan kankanin lokaci.

Haka za ta iya a jiye maka wasu mahimman bayannanka bayan tsawo shekaru idan ka nemi ta fitar maka za ta fito maka da su. Haka da zamu koma wajen fanin kula da lafiya ana amfani da computer wajen binciko yanayin cuta da mazauninta a jikin dan adam, ba tare da likita ya tambaye shi ba, hakanan ana iya bincikar cikin da mace take dauke da shi a gane lafiyar shi ko rashin lafiyar shi da yanayin kwanciyar shi, duk a cikin dan kankanin lokaci. Dawo bangaren makarantu zaka samu suna amfani da computer wajen saukaka bincike da nazarin darussa ga yara. Sukan yi amfani da ita computer ta wajen kimiyya da fasaha don gano adadi da kididdiga. Ana samun na’ura da take dauke da muhimman takardu ga daliban fiye da dubu dari uku wanda zai yi wahala a sami wani laburari a karamar makaranta dake de littafi daban daban har dubu goma.

Ta hanyoyin sadarwa computer tana taimakawa gidajen jarida, da na watsa labarai wajen gyare gyaren tarin rubutu, video da sauti wanda a dan kankanin lokaci sai su gyara ayyukansu don watsawa don haka da taimakon computer ba sa bukatar sai sun shiga studio kafin su dauki bayanan da za su watsa. Haka nan sadarwa da aka samu ta yin amfani da wayoyin ta fi da gidanka(salula) za ka iya rabuta wasika ka aika, zaka iya aje alama ta tunatarwa, zaka iya daukar hoto ko video zaka iya yin lissafi da dai makamatansu ciki dan kankanin lokaci ba tare da wahala ba. Kasancewar ci gaban internet ya mamaye dukkan fannonin rayuwar dan adam a yau ba ta tafiya yadda ya kamata sai da internet ilimin computer shine sinadarin cin moriyar internet Idan kuwa muka duba bangaren tsaro, a zamanin da, zaka samu yana da wahala a gano file (kundin) na laifi da mutum yayi bayan an kai shi kotu, amma yanzu da zarar an saka bayanan shi, nan take za a samu, ka duba irin Computer da take bincikan ‘yan yatsu da fuskar wanda ake zargin shi da laifi, ko da yake yanzu ne aka fara irin wannan tsari a wannan kasa ta mu Najeriya.

Haka idan ka duba hatta cikin motoci da abubuwan hawa kamar jirgin sama, da jirgin kasa da jirgin ruwa za ka samu akwai computer a jikinsu, daga abinda yake sarrafa yanayin zafi ko sanyin abin hawa computer dake ciki take tafiyar da shi. Ballantana uwa uba ire-iren abubuwan hawa da ake kerowa na zamani a yanzu akwai motar da ake samun computer a cikin ta wacce duk inda wannan motar take a duniya za a iya kashe ta ko kuma a kunna ta, haka nan jirgin sama muna da labarin jirage irin na yaki wanda kasahen da suka ci gaba suke da su wadanda babu matuki a cikinsu, computer da ke ciki ita take sarrafa su, wanda ko da abokanen gaba sun harbo wannan jirgin to ba za a rasa rai ba. Computer ta kawo sauki ga masu ayyuka irin wanda a da sai an dauki tsawon lokaci ko kwanaki kafin ace an kammala su. Misali abin da ya shafi lissafin dukiya don fitar da gado an sami sauki mai yawa ,idan ka duba Computer da take rabon gado wanda duk abinda mutum ya mallaka komai yawansu, komai yawan wanda za su gaje shi, da zarar an gama zuba mata bayanan dukiyar da magadan sakon biyar yayi yawa ta gama raba wannan gado kamar yadda Allah madaukakin sarki ya fadi ayi ba tare da ta rage wani abu ko ta karashi ga wani ba. Mu koma bangaren kere-kere shima Computer tana taka mahimmiyar rawa wajen kere- keren abubuwa wanda a zamanin da, sai an sami karti majiya karfi suke iya kera wannan abun. Idan muka koma harkar zane zane, yanzu an kai fagen da idan ka nuna fili kace ga girmanshi, kana son bishiya kaza, filawa kaza, kana kuma son mota irin kaza, ga irin fenti da kake so, ga irin kofofi da dai dukkan abinda za ka fadi da ya kamata a ganshi, kana gama lissafi wanda zai zana maka gidan yana kwafewa a ‘yar karamar takarda a hannunshi, da zarar ya gama zana gidan sai yayi amfani da daya daga cikin program na Computer ta gina wannan gida a cikin ta kamar yadda kace kana son, ka ganshi kamar da gaske babu wani abu da za ka ce ba na gaske bane, wanda idan kace kana son a bude maka cikin gidan kaga yadda kujeru da bayi da kayan kichin suke duka za ka gani. Kuma idan aka gama gina maka gidan na zahiri za ka ga babu bambanci tsakanin na cikin Computer da naka na waje.
Tura Zuwa:

Yadda ake gyara wayar hannu idan ta jike da ruwa.

Yadda ake gyara wayar hannu idan ta jike da ruwa.
Yadda ake gyara wayar hannu idan ta jike da ruwa.

Ka dauka ruwa zaka yi anfa ni dashi sai wayar ta fada cikin ruwan, kayi maza maza ka dauko ta, a daidai lokacin da ka dauko ta ta riga ta jike sharkaf da ruwa. Mataki na farko da zaka dauka shine sai ka cire batir din ta sanan ka tabbatar ba ka kunnata ba domin idan ka kunnata a wannan lokacin lallai za ka yi damejinta. Ita kowa matsala ta fadawar waya cikin ruwa wannan ku san ruwan dara ne wanda ke gama da duniya, kusan wannan matsalan ta na damun mutane da dama, sannan kuma kowa da irin mataki da ya ke dauka, kusan rabin mutane da wannan matsalan ta ke shafansu kokari suke yi su bi hanyan da za su bi su iya tsane ita wayar tasu. Saura kuma ta ke kawai ta ke mutuwa, saboda wasu ganganci da su ke yi bayan sun fito da ita wayar ta su a cikin ruwa. Saboda haka duk wanda wayar shi ta fada cikin ruwa ya yi hanzari ya stamo ta nan take ya cire murfin wayar ya kuma zare batir din ta, zai iya saka batidin a fili ko kuma wayar da batir din a fili yanda rana za ta gasa su. Sanan kuma ya da kyau a lokacin da ya bude wayar ya cire batir ya sake dubawa ya gani shin ruwan ya riga ya shiga har cikin injin wayar ko kuwa bai shiga? To idan har ka lura cewar ai ruwan ya shiga ciki zaka iya daukanta ka rike gefenta ta rika yarfeta kamar yadda ka ke yarfar da kaya idan an wanke su, za ka ci gaba da yin haka har sai ka tabbatar cewar wayar babu sauran ruwa a cikin ta sannan ka sake mayar da ita cikin rana, ka kuma kifa bayanta a kasa, wato fuskanta yana kallon kasa bayanta na kallon sama saboda kada rana ta bata screen din wayar.


To idan kuwa ka fuskanci cewa lallai wayar ta jike sharkaf to abu na biyu shine ka sakata a cikin danyar shinkafa? Shinkafa? Na san da yawa za su ji abun banbarakwai me ya kawo kuma shinkafa a maganar tsane waya? Wannan haka ya ke, lallai shinkafa za ta iya tsane maka dukkanin ruwan da wayar ka ta debo a cikinta. Yadda zaka yi shine, za ka samu wani kwano mai girma wanda zai iya daukar wayar ka saka ta da batirin ta a gefe sai ka cika wannan kwanon da danyar shinkafar ka sami murfi ka rufeta ruf, sai ka barta har tsawon awowi shida, daga nan sai ka daukota ka mayar da batirinta, idan ka kunna ta zata tashi da yardar Allah. (Wannan an jarabta kuma yayi aiki) Haka kuma mutum zai iya amfani da abin hura gashi wanda mata ke amfani da shi idan suka jika gashin kansu (Dryer) domin ya bushe. Amma shima idan za ayi anfani dashi dole a lura da wani irin dryer za ayi amfani da shi, domin a lokacin da ka fuskanci cewar lallai wayar ka ta jike sosai har kana ganin cewa idan kayi anfani da danyar shinkafa ba zai yi tsane ruwan ciki ba, ka ga a nan kana bukatar amfani da dryer. Da farko dai zaka cire batirin wayar sannan ka rike wayar ha hannun ka sosai sannan ka fara yarfed da ita kamar yadda ake yarfar da kaya da suka jike, bayan ka gama yarfarwa ka tabbatar da babu sauran ruwa a jikin ta sai ka ciro ko kuma ka je shagon da ake yiwa mata gyaran gashi su baka karamin dryer sannan kuma ka yi amfani da mai sanyi ba mai zafi ba, domin idan ka yi amfani da mai zafi to zaka karawa wayar ka wata matsala ta daban, haka zaka ci gaba da busa mata iskar har sai ka tabbatar da wayar ta bushe sosai, sannan ka mayar da batirin sannan ka saka ta a caji baya wani tsawon lokaci sai ka kunnata. Shi ya sa yana da matukar kyau idan ka na da waya kuma ta na da tsada ko kuma halin gyara to yana da kyau ka rika saka mata irin rigunan ruwa da kuma abubuwan da zasu hanat lalacewa. Wannan shine a takaice hanyoyin da zamu iya bi domin muga mun dawo da hayyacin wayarmu a lokacin da ta fada a cikin ruwa. A karshe nake cewar ayi hattara!
Tura Zuwa:

Yadda ake cincin mai kama da kek

Yadda ake cincin mai kama da kek
Yadda ake cincin mai kama da kek

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan lokaci uwargida, tare da fatan an yini lafiya. Mata da dama ba su iya amfani da fulawa wajen sarrafa ta wajen yin kayan marmari ba. Da yawan mata sun fi kwarewa ne a harkar girke-girken da ake yin su da albasa da kayan miya. Ganin hakan ne yasa a yau na kawo muku yadda ake yin cincin mai kama da kek. Tare da fatan za a gwada a gida domin sanya kunnuwan maigida su yi motsi. A sha karatu lafiya.

1.          Fulawa
2.          Suga
3.          ‘Baking powder’
4.          Butter/ man gyada
5.          kwai 15
Da farko dai, za a samu kwano ko roba sannan a fasa kwai guda goma sha biyar a ciki. Bayan haka sai a samu kofi tsaka-tsaki a auno suga daidai girman wannan kofi sannan a zuba a cikin ruwan kwan a yi ta gaurayawa har sai ta narke. A sake dauko wannan kofin da aka auna suga a narkar da ‘butter’ sannan a zuba a kofin har sai ya cika sannan a zuba a cikin hadin suga da kwai a cigaba da motsawa da muciya, sannan a debo ‘baking powder’ babban cokalin cin abinci daya ya cika sosai sannan a zuba. A cigaba da gaurayawa. A sake debo fulawa daidai cikin wannan kofin da aka auno suga da sauransu a auno fulawa kofi daya sannan a zuba a cikin hadin a cigaba da juyawa. Idan hadin ya yi ruwa-ruwa sai a dan kara fulawa kadan ta yadda in an sanya hannu ba zai manne ba. Amma kada a bar fulawar ta yi taurin hadin cincin din da aka saba.


A wanke hannu a goge sannan a gutsuro wannan kwabin a danna a tafin hannu a mulmula sannan a yi masa rami a tsakiya kamar awarwaron da yara mata ke sanya wa a hannu, sannan a dora man gyada a kan wuta a soya. A bar shi a kan wuta domin hadin ya soyu daga nan sai a soke. Za a iya cin irin wannan cincin da shayi da kuma lokacin da za a tarbi baki.
Tura Zuwa:

PROGRAMING LANGUAGE WANE NE YA KAMATA NA FARA KOYA? – (2)

PROGRAMING LANGUAGE WANE NE YA KAMATA NA FARA KOYA? – (2) 
Fashin baki ga kowane ra’ayi guda cikin shidan nan

1                Ba su san dalilin da ya sa suke koyon programming ba.

Ga waɗanda suka tsinci kansu a cikin karatun kwamfuta kuma suka dace da shiga bangaren Programing Language to shawarar da zamu basu ita ce su koyi Python.

2                Domin amfani yara.

Duk wanda yake son ya koyin yaren kwamfuta domin ya kirkiri wata manhaja domin kanan yara ko kuma ya koyi yaren da yake son ya koyawa yaransa suma a fara damawa da su a kan abin da ya shafi Programing Language to ya koyi Python.

3                Domin jin dadi da nishadantarwa

Wanda yake da ra’ayin yin Programing Language  amma kuma yana yin shi domin jin dadi da debe kewa, da nishadantarwa, to akwai tambayoyi da za ayi masa, irin amsar da ya bada ita ce sakamakon idan ya kamata ya kai kanshi wurin abin da ya cancanta ya koya.
Kana da wani yare da kake da sha’awar amfani da shi a cikin guda shidan nan? Idan ba shi da shi, kawai shi dai ya son a koya mishi wanda zai fara to yana da zabi guda hudu.
1.      Yana son ya koyi programmin language cikin ruwan sanya – to ka koyi Python.
2.      Idan kuma kana son ka koyi Programing Language da ya fi cancanta da kyau wurin koya – to ka kuyi Python
·         Idan kuma kana son ka koyi Programing Language amma ta yare mai dan wahala to a nan zamu baka zabi ka koyi yaren da ake amfani da shi wurin sarrafa moto ta hawa waɗanda suke da tsarin manu’al da Idan ka na son zaka koyi yaren da zaka rika yin manhajoji da zasu rika yin aiki a motoci na manu’al sai muce ka koyi yaren C Programming. Idan kuma kana son ka koyi yaren da zaka rika yin manhajojin da zasu rika yin aiki a cikin motoci auto sai muce ka koyi JAVA Programming.
1.      Idan kuwa yana son ya koyi Programing Language ta hanyar da tafi kowacce wahala wacce zai samu sauki idan yana son nan gaba ya koyi wani yare sai muce ya koyi C++ Programming.

4.      Yana da ra’ayin yin programming

Shima wanda yake da ra’ayin yin Programing Language , shima za a tambaye shi Kana da wani yare da kake da sha’awar amfani da shi a cikin guda shidan nan? Idan ya amsa cewar yana da shi. Sai a sake tambayar sa wane yare ne kuma bangaren me? A wannan wurin yana da zabi guda hudu (4).

a)    Ina son in rika yin webdesign.

Ka na son web site da zai rika yin aiki irin su facebook ko twitter da makamantansu? Idan amsar ta zama e sai mu ce maza ka koyi JavaScript. Idan kuwa ya ce bai sani ba, zamu tambaye shi kana son ka gwada wani abu sabo a rayuwarka ta bangaren web design? Idan ya ce e, sai mu tambaye shi shin a cikin kayan wasa na yara wanne ne kake ra’ayi ko kuma ya fi baka sha’awa. Idan yace lego sai muce ya koyi yaren Python. Idan kuma ya ce Play-Doh shi ne kayan wasan da ya ke ra’ayi sai muce ya koyi Ruby Programming. Idan kuwa yace shi bai san wani kayan wasa ba, ko kuma yace yana son ya yi amfani da kayan wasanni tsofaffi na dai sai muce ya koyi PHP.

b)   Ina son aiki a manyan kamfanoni

Idan ka ce kai bayan ka iya yin programmin language kana son ka sami aiki ne a manyan kamfanoni na kimiyya da fasaha, zamu tambaye ka ko kana da ra’ayin aiki a kamfanin Microsoft? Idan ka ce e to sai muce ka je ka koyi C# Programme. Idan kuwa domin jin dadi da nishadi ne sai muce ya koyi JAVA Programming.

c)    Aiki da wayoyin komai da ruwanka

Idan kuma ya ce ina son idan na gama koyon Programing Language ina son in rika yin manhajojin da zasu rika aiki da wayoyin komai da ruwanka (Smart Phones) sai mu tambaye ka wayoyin guda biyu ake da su. Akwai waya kirar Apple masu tsarin babbar manhajar iOS, da kuma wayoyi kirar Android. Idan yace ya son ya yi aiki da wayoyi kirar Apple sai muce ya koyi C Programming.  Idan kuwa ya ce yana son ya yi aiki da wayoyi kirar Android sai muce ya koyi yare JAVA.

d)   Domin hada kayan Games

Idan kuwa yace yana son bayan ya iya programming ɗin sa ya rika yin manhajojin da ake amfani da su a cikin na’urorin game kamar playstation da irinsu Nitando da dai makamantansu sai muce ya koyi C++  amma sai dai yana dan wahalar koya.

5.      Yana son karawa kanshi sani a cikin Programing Language

Ga wanda daman ya dan san programming kuma yana son kawai ya karawa kanshi sani ne ko kuma sanin madogara shima za a tambaye shi Kana da wani yare da kake da sha’awar amfani da shi a cikin guda shidan nan? Idan ya amsa cewar yana da shi. Sai a sake tambayar sa wane yare ne kuma bangaren me? A wannan wurin yana da zabi guda hudu (4).

a)    Ina son in rika yin webdesign.

Ka na son web site da zai rika yin aiki irin su facebook ko twitter da makamantansu? Idan amsar ta zama e sai mu ce maza ka koyi JavaScript. Idan kuwa ya ce bai sani ba, zamu tambaye shi kana son ka gwada wani abu sabo a rayuwarka ta bangaren web design? Idan ya ce e, sai mu tambaye shi shin a cikin kayan wasa na yara wanne ne kake ra’ayi ko kuma ya fi baka sha’awa. Idan yace lego sai muce ya koyi yaren Python. Idan kuma ya ce Play-Doh shi ne kayan wasan da ya ke ra’ayi sai muce ya koyi Ruby Programming. Idan kuwa yace shi bai san wani kayan wasa ba, ko kuma yace yana son ya yi amfani da kayan wasanni tsofaffi na dai sai muce ya koyi PHP.

b)   Ina son aiki a manyan kamfanoni

Idan ka ce kai bayan ka iya yin programmin language kana son ka sami aiki ne a manyan kamfanoni na kimiyya da fasaha, zamu tambaye ka ko kana da ra’ayin aiki a kamfanin Microsoft? Idan ka ce e to sai muce ka je ka koyi C# Programme. Idan kuwa domin jin dadi da nishadi ne sai muce ya koyi JAVA Programming.

c)    Aiki da wayoyin komai da ruwanka

Idan kuma ya ce ina son idan na gama koyon Programing Language ina son in rika yin manhajojin da zasu rika aiki da wayoyin komai da ruwanka (Smart Phones) sai mu tambaye ka wayoyin guda biyu ake da su. Akwai waya kirar Apple masu tsarin babbar manhajar iOS, da kuma wayoyi kirar Android. Idan yace ya son ya yi aiki da wayoyi kirar Apple sai muce ya koyi C Programming.  Idan kuwa ya ce yana son ya yi aiki da wayoyi kirar Android sai muce ya koyi yare JAVA.

d)   Domin hada kayan Games

Idan kuwa yace yana son bayan ya iya programming ɗin sa ya rika yin manhajojin da ake amfani da su a cikin na’urorin game kamar playstation da irinsu Nitando da dai makamantansu sai muce ya koyi C++  amma sai dai yana dan wahalar koya.
A darasin mu na gaba da yardar Allah za mu yi cikakken bayani a kan mataki na karshe wato IDAN MUTUM NA SON YA SAMI KUDI A BANGAREN PROGRAMMING LANGUAGE ME ZAI KARANTA.
Mu yi karatu lafiya

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

PROGRAMING LANGUAGE WANE NE YA KAMATA NA FARA KOYA? – (1)

PROGRAMING LANGUAGE WANE NE YA KAMATA NA FARA KOYA? – (1)

 Mene ne Programing Language?

WANI TSARARREN RUBUTU NE DA AKE YI DOMIN KURMAN MASHIN, AMMA KUMA YA SANYA SHI YA KASANCE MAI JI KAMAR MAI KUNNE.

Daga ina ya kamata ka fara?

Mene ne dalilin da ya sa ka ke son ka fara yin Programing Language ? Wannan ita tambayar da ya kamata ka fara yi wa kanka da kanka, kasancewar kowane Programing Language  akwai abin da ya ke yi, da kuma abin da ake iya yi da shi, da kuma irin mashin ɗin da ya ke iya sarrafawa, da kuma alaƙar da take tsakanin sa da sauran Programing Language da ake da su.

Programing Language nawa ne a duniya?

Programing Language suna da matuƙar yawa, tun daga wanda ake amfani da shi a cikin ƙananan na’urori da kuma manya, da waɗanda ake amfani da su a cikin gida da kuma ma’aikatu da kuma waɗanda ake amfani da su a harkokin mu na yau da kullum. Sai dai a cikin waɗannan Programing Language  ɗin akwai waɗanda suka sami karɓuwa akwai waɗanda ko sunan su ma ba mutane da yawa ba su san su ba.
A wannan muƙalar zamu ɗauki yaren Kwamfuta waɗanda su ka fi shahara guda tara (9) a wannan zamani, waɗanda kuma da su ne duniya ke taƙama kuma kusan duk wani abu da za ka gani a wannan lokaci idan dai na’ura ce, tun daga kayan wasan yara (games) da na’urorin da manya suke amfani da su kamar wayoyin tafi-da-gidanka, da ma manya da ƙananan manhajoji dukkaninsu ba sa wuce ɗaya daga cikin waɗannan Programing Language  ɗin.
Wadannan programming guda tara ne, waɗanda suka hada da
·         Python
·         JAVA
·         C
·         PHP
·         C++
·         JavaScript
·         C#
·         Ruby
·         Objective-C

Mene ne dalilin ya zai sa na koyi Programing Language ?

Akwai ra’ayin mabambanta ga masu koyon yaran kwamfuta. Waɗannan dalilai sun sha bambam, sai dai daga baya ra’ayin yana komawa ga mataki na karshe amma kuma dukkansu babu matsala ga wanda mutum ya ɗauka.
An tattara ra’ayoyin jama’a masu koyon Computer Programming har gida shida (6), ta hayar la’akari da ta ina mutum ya ɓullo da kuma ina yake son ya ɓulla a wannan harkar.
·         Ba su san dalilin da ya sa suke koyon programming
·         Domin amfani yara.
·         Domin jin daɗi da nishadantar wa
·         Yana da ra’ayin yin programming
·         Yana son ƙarawa kanshi sani a cikin Programing Language
·         Domin ya sami kudi.
A darasin mu na gaba za mu ɗauki kowane ɗaya daga cikin waɗannan ra’ayoyi mu bada shawara ingantacciya ga duk mutumin da yake son ya koyi programmig language cikin wadannan ra’ayoyi shida.
In Sha Allah.

-------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Zaku iya samuna a kan shafukan sada Zumunta kamar haka:

Whatsapp ko Kira: +2349039016969
Twitter: @muhdabbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Facebook: Muhammad Abba Gana Kolo ko kuma ta hanyar latsa nan

Instagaram: @real_abbagana ko kuma ta hanyar latsa nan
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *