Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Hanyoyi 5 da za ki magance zubewar gashin kai


Sau da dama mata kan samu kansu cikin shiga ukun zubewar gashi, wanda yawancin hakan na faruwa ne a garin neman a gyara gashin kai, sai kuma a bata, karshe gashin kai ya zube. Don haka ne na taho miki da hanyoyi biyar da idan kin bi kowacce daga ciki za ta magance miki zubewar gashin kanki, ta kuma kara wa gashin kanki tsawo da kyawu da kuma sheki.

    1.     Amfani da mayukan gashin kai: Ki samu daya daga cikin man gashin kai kamar su, Man Olibe oil da Coconut oil da Canola oil da sauransu. Daga nan sai ki zuba daya daga cikin man da na lissafa a sama a cikin tukunya, sannan ki dora a kan wuta. Ki bar shi ya yi zafi, amma ba wai sosai ko ya tafasa ba. Bayan nan sai ki sauke daga kan wuta, sannan ki shafa a gashin kanki. Yana da kyau ki shafa a kofofin gashin kanki, hakan zai taimaka wajen sanya gashin kanki ya yi tsawo da kuma sheki. Idan kin shafa sai ki rika amfani da hannuwanki wajen goggogawa da dan karfi-karfi. Bayan nan sai ki sanya hular ‘shower cap’ har zuwa awa daya. Bayan nan sai ki shafa man shampoo. Daga nan sai ki wanke kanki.

   2.     Amfanin da jus din citta ko tafarnuwa ko albasa: Ki samu albasa ko citta ko tafarnuwa, sannan ki markada daya daga cikinsu har ta zama kamar jus. Daga nan sai ki shafa a gashin kanki. Yana da kyau idan kika shafa sai ki kwana da shi. Da safe sai ki wanke sosai. Yin hakan zai magance miki zubewar gashin kai.

    3.     Tausa a kai da kuma gashin kai: Idan kina tausar gashin kanki lokaci zuwa lokaci yakan haifar da gudanar jini cikin sauki a kofofin gashin kanki. Masana kiwon lafiya sun ce idan har jini na gudana yadda ya kamata a kofofin gashin kai, to hakan zai sanya gashin kai ya kara tsawo. Shafa man essential oil kamar su Labender da bay essential oil da almond da kuma sesame a lokacin da za a yi tausar kai ko gashin kai yana sanya gashin kai ya kara tsawo da kyau da kuma sheki.

    4.     Amfani da abin da yake kashe kwayoyin cuta: Idan kina shafa abin da yake kasha kwayoyin cuta a gashin kanki zai hana gashin kanki zubewa. Misali ki samu kwalin ko ledar ganyen shayin ‘Green tea’ biyu, sai ki jika su a cikin kofi daya da ruwan zafi. Bayan ya huce, sai ki shafa a gashin kanki. Idan kin yi hakan za ki bar shi har zuwa awa daya, daga nan sai ki wanke. Ganyen shayin green tea yana dauke da sinadaran da ke hana zubewar gashi, a lokaci guda yana kara yawan gashin kai.

    5.     Ki rika samun hutu: Masana kiwon lafiya sun tabbatar da aikin wuya, rashin kwanciyar hankali hade da gajiya na haifar da zubewar gashi. Don haka idan ba kya so gashin kanki ya zube sai ki rika hutawa, a lokaci guda ki gujewa aikin wahala.
Tura Zuwa:

YADDA MACE ZATA MALLAKE MIJI DA KALLO KADAI

YADDA MACE ZATA MALLAKE MIJI DA KALLO KADAI

Kallo wani abune mai saurin isar da sako musamman a wajen masoya ko kuma Ma'aurata. Yawancin mata suna da wani matsala wacce itace ke sawa bayan anyi aure sai yaji matar tana fita masa a rai a hankali a hankali. Tun kafin auren mace bata iya bude idanuwanta ta kalli saurayinta saboda kunya, idan aka tashi kallonsa to kallo na daban take mai to wannan kallon da take masa na kunya yana da tasiri kwarai da gaske a wajen namiji. Akwai sinadarin da yake kunshe cikinsa. Da yin aure sai kaga mace ta canza, wannan kallon da ake masa lokacin samartaka yanzu an daina. Kallonsa take yi kamar yadda take kallon kowa. Kallo yana da nau'I iri iri. Anaso mace ta dinga yiwa mijinta kallo na musamman, kallo na 'kauna, da soyayya hade da daukar hankali. Matan da suka amsa sunan su na mata, sune masu kallo iri-iri kuma kowanne akwai manufarsa:


*Akwai kallon 'NAYI KEWAR KA', ka jima a office, yana ganin wannan kallon yasan yayi laifi zai fara rarrashin ki.

*Akwai kallon 'INA ALKAWARI NA'..., yana gani ya sani idan alkawarin bai cika ba zai sake miki wani alkawarin hade da ban hakuri.

*Akwai kallon 'BANI DA LAFIYA' a nan zai fara tambayar ki mai ya sameki? Kinsha magani?

*Akwai kallon 'KAYI MUN LAIFI', ka 'bata min, zai fara baki hakuri.

*Akwai kallon 'FARIN CIKI DA NISHADI', a nan zakiji yace menene labari yau naga nishadin yayi yawa.

*Akwai kallon 'GODIYA' a nan Maigida zaice kinfi haka duk abinda nayi miki ban biyaki ba, da dai sauransu.

*Akwai kallon 'INA DA BUKATAR KA' idan ya gani yasan me kike nufi. To Allah yasa mijinki mai karantar kallon kine. Ameen. Akwai salon KALLO da yawa wanda mace ta nan kawai ya isa ta isar da sako ba sai tayi magana ba, ko da kuwa za tayi maganar, ya zamo kallon ya riga maganar isa.
TO YA ZANYI IN KALLI MAIGIDANA? A koda yaushe mace idan zata kalli mijinta ya kasance kada ta bude idonta gaba daya, tayi 'kasa 'kasa dasu kamar mai jin bacci, ta rinka lumshe su, tana kiftasu a hankali, tana sarrafasu yadda ya kamata, musamman in an sami mai manyan idanuwa ce, sannan mata Ku dagye wurin sanya kwalli yana gyaran idon mace, kallon zai fi dakan zuciyar Maigida, Kuma kada ki 'kurawa Maigida idanu kai tsaye, bance kada mace ta kalli mijinta ba, ki kalli mijinki tunda naki ne, amma ki san irin kallon da zaki yi masa. 


TA HANYAR KALLO KADAI MACE ZATA FARA HAWA MATAKAN MALLAKAR MIJI...
Tura Zuwa:

SHAWARWARI DA TUNATARWA 3


SHAWARWARI DA TUNATARWA 3

⭕DUNIYAN FASAHA⭕

www.duniyanfasaha.blogspot.com

__________________________

SHAWARWARI DA TUNATARWA


Daga
Maman Ussey

   Yan mata da zawarawa muji tsoron Allah mukama mutuncin kanmu Duk wata rayuwa da zakiyi kisani cewa Allah yana kallonki dan naga yanxu gani kuke matar aure ita kadaice wadda takeda katanga to kusani cewa duk wani abu dazakiyi ko a boye ko a bayyane sai an rubuta sa cikin mizanin ayukanki gwara kiyiwa kanki kiyamul lail ki nutsu kisan abinda kikeyi Duk wani abinda kikasan Haramun ne ki gujesa kiyi nesa dashi Domin samun Tsira Karkiyi kawance da duk wata qawar da kikasan Ba akida ko al'adarku dayaba dan wata rana zata iya janyo ra'ayinki mu kasance mata nagari tayanda za'ayi Afahari damu a ko'ina anan zan dasa Aya. sai wani lokacin  in mai duka ya kaimu.

Tura Zuwa:

SHAWARWARI DA TUNATARWA 2

SHAWARWARI DA TUNATARWA 2

⭕DUNIYAN FASAHA⭕


www.duniyanfasaha.blogspot.com

__________________________

SHAWARWARI DA TUNATARWA


Daga

Maman Ussey

  Wani abin haushi abin takaici Wai yanxu mata bazaki sallah cikin lokaciba sabida an miki kwalliya karkije alwala ta goge Innalillahi wa'innah illaihirraju'un kenan kin xabi duniyarki a bisa lahira ko....?? wace riba gareki idan Allah ya dauki ranki kina cikin irin wannan halin...?? mezaki ce da mahaliccinki..?? kokinsan cewa mutuwa kowane lokaci zata iya yi miki bazata gaskiyq mata mugyara yakamata ace duk wani abu komai mahimmancinsa ki hakura dashi har sai kin gana da mahaliccinki (SALLAH) , Adaure ayita cikin lokaci kuma bada garaje ba dan naga wasu ma sallar basusan yanda zasuyita cikin nutsuwa sabida kawai dadin duniya ya shagaltar Dasu.
Tura Zuwa:

SHAWARWARI DA TUNATARWA

SHAWARWARI DA TUNATARWA

DUNIYAN FASAHA
www.duniyanfasaha.blogspot.com

SHAWARWARI DA TUNATARWA


Daga

Maman ussey


A'uzubillahi minashaidanir rajeem, Bismillahi rahamaniraheem.

  Dukan yabo da godiya su tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda yabamu ikon ganin, wan nan ranar mai albarka tsira da aminci su kara tabbata a gurin shugaban manzani Annabinmu dan gata Muhammad (S.A.W.)

ASSALAMU ALAIKUM MATAN WAN NAN ZAURE FATAR KUNA LAFEEYA ALLAH YASA HAKA AMEEN ZAN DAN FADAKAR NE GA MATA MUSAMMAN NA WANNAN ZAMANIN ALLAH YABANU IKON FADIN DAI DAI AMEEN


  Kalmar macce abu ne mai matukar girma sabida daraja da kuma kima irin ta diya macce Surah aka saukar dungurun gum(NISA'I) , Yaku yan uwana mata kada ku shagala da jin dadin rayuwar duniya kuyi biris da baiwar da Allah ya yi muku kusani cewa duk wank jin dadin ki mstsawar baki kame kanki daga aikata fasadi ba yazama na banza kuduba kugani yanxu Rayuwar da muke ciki a bin haushi matan aure basa fita irin wadda Addini ya umarcemu damuyi wa'iyazu billah haba mata, Ina kuka baro Hijabinku suturar ku wadda Allah ya ce ku lulluba da ita...??? Wai ace matar aure zata fita unguwa saita kashe makeup tamkar zataje gasar sarauniyar kyau amma abin haushi In kika tarar da ita A cikin gidanta tamkar yar aiki🤔, Wai bazatayi wanka da tsafta ba sai in zata gidan biki ko asibiti ko wani abin to wallahi kisani duk wanda zaiga adonki ya yaba matsawar ba mijinki bane kinyi a banxa.
Tura Zuwa:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *