Kallo wani abune mai saurin isar da sako musamman a wajen masoya ko kuma Ma'aurata. Yawancin mata suna da wani matsala wacce itace ke sawa bayan anyi aure sai yaji matar tana fita masa a rai a hankali a hankali. Tun kafin auren mace bata iya bude idanuwanta ta kalli saurayinta saboda kunya, idan aka tashi kallonsa to kallo na daban take mai to wannan kallon da take masa na kunya yana da tasiri kwarai da gaske a wajen namiji. Akwai sinadarin da yake kunshe cikinsa. Da yin aure sai kaga mace ta canza, wannan kallon da ake masa lokacin samartaka yanzu an daina. Kallonsa take yi kamar yadda take kallon kowa. Kallo yana da nau'I iri iri. Anaso mace ta dinga yiwa mijinta kallo na musamman, kallo na 'kauna, da soyayya hade da daukar hankali. Matan da suka amsa sunan su na mata, sune masu kallo iri-iri kuma kowanne akwai manufarsa:
*Akwai kallon 'NAYI KEWAR KA', ka jima a office, yana ganin wannan kallon yasan yayi laifi zai fara rarrashin ki.
*Akwai kallon 'INA ALKAWARI NA'..., yana gani ya sani idan alkawarin bai cika ba zai sake miki wani alkawarin hade da ban hakuri.
*Akwai kallon 'BANI DA LAFIYA' a nan zai fara tambayar ki mai ya sameki? Kinsha magani?
*Akwai kallon 'KAYI MUN LAIFI', ka 'bata min, zai fara baki hakuri.
*Akwai kallon 'FARIN CIKI DA NISHADI', a nan zakiji yace menene labari yau naga nishadin yayi yawa.
*Akwai kallon 'GODIYA' a nan Maigida zaice kinfi haka duk abinda nayi miki ban biyaki ba, da dai sauransu.
*Akwai kallon 'INA DA BUKATAR KA' idan ya gani yasan me kike nufi. To Allah yasa mijinki mai karantar kallon kine. Ameen. Akwai salon KALLO da yawa wanda mace ta nan kawai ya isa ta isar da sako ba sai tayi magana ba, ko da kuwa za tayi maganar, ya zamo kallon ya riga maganar isa.
TO YA ZANYI IN KALLI MAIGIDANA? A koda yaushe mace idan zata kalli mijinta ya kasance kada ta bude idonta gaba daya, tayi 'kasa 'kasa dasu kamar mai jin bacci, ta rinka lumshe su, tana kiftasu a hankali, tana sarrafasu yadda ya kamata, musamman in an sami mai manyan idanuwa ce, sannan mata Ku dagye wurin sanya kwalli yana gyaran idon mace, kallon zai fi dakan zuciyar Maigida, Kuma kada ki 'kurawa Maigida idanu kai tsaye, bance kada mace ta kalli mijinta ba, ki kalli mijinki tunda naki ne, amma ki san irin kallon da zaki yi masa.
TA HANYAR KALLO KADAI MACE ZATA FARA HAWA MATAKAN MALLAKAR MIJI...
No comments:
Post a Comment