Assalamu Alaikum Uwargida, barka da wannan lokacin. Yaya azumi?
Yau a filin namu na Girke-girken Azumi, za mu kawo muku yadda ake girka Alalen Doya.
Da farko dai ga kayayyakin da uwargida ke bukata don yin alalen:
- Doya
- Manja
- Man gyada
- Attarugu
- Albasa
- Kifin karafish
- Kayan kamshi
- Kwai
- Gishiri
- Sinadarin dandano
- Leda/gwangwani
Yadda ake yi:
Uwargida za ki fara gurza doya sai ki zuba albasa da atturugu a ciki ki markada.
Sai ki dafa kwai ki yayyanka shi ki ajiye a gefe.
Sannan ki sake yanka wata albasar ki zuba a kan markaden nan.
Sai ki dauko sinadarin dandano da gishiri da kayan kanshi da nikakken kifin karafish ki zuba a kai.
Daga nan sai ki zuba manja da man gyada a kai ki juya sosai.
Sannan sai ki dauko gwangwani ko leda ki rika zuba hadin alalen nan a ciki sannan ki dauko yankakken dafaffen kwai ki zuba a ciki.
Sai ki ajiye har sai kin gama sai ki zuba a tukunya yadda zai turara. Idan ya dahu sai ki sauke.
Shi ke nan alalen doya ya kammala.
A ci dadi lafiya.
No comments:
Post a Comment