Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layukan Sadarwa Cikin Sauki

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layukan Sadarwa Cikin Sauki
Kamar yadda hukumar sadarwa ta kasa Nigeria wato NCC ta ba da umarni, na cewar ana bukatar duk ‘yan Nijeriya da su hada lambar shaida ta kasa {NIN} da layukan sadarwan su, kamar dai yadda muka alakanta lambar BVN din mu da asusun mu na banki.

Insha Allahu yau a Duniyan Fasaha, zamu nuna muku yadda zaku duba kuma ku tabbatar idan layin ku na sadarwa yana da nasaba da katin kasa (NIN) ko a’a. Bugu da kari, zamu nuna muku yadda za’a hada katin kasa wato NIN da wasu daga cikin manyan layukan sadarwa a Nigeria kama daga MTN, Glo, 9Mobile da kuma Airtel.  

Yadda Za’a Tabbatar Da Matsayin Katin Kasa A Layin Sadarwa

Idan har mutum bashida tabbaci sosai akan matsayin katin kasar sa a layin san a sadarwa sai ya bi matakan nan domin tabbatarwa:

Mataki:  Da farko Za’aje wajen kira dake waya sannan a rubuta *346# a kira. Bayan ya budu sai a bisa da amsa da “1”.

Muddin an taba rajistar, lambar katin kasa da layin sadarwa, za’a nuna wa mutum lambar katin kasa, haka zalika idan har ba’a taba yin rajistar da layin sadarwa da aka yi amfani dashi ba za’a nemi mutum da ya ziyarci ofishi na NIMC mafi kusa domin yin rajistar kuma ana yinsa kyauta ne.

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layin Sadarwa Na MTN Nigeria

Yanzu haka za’a iya danganta lambar shaidar kasa (NIN) zuwa layin sadarwa na MTN cikin sauki. Akwai matakai guda biyu da za’a iya bi wajen aika ta hakan, kuma dukka masu sauki ne sai de daya daga ciki na bukatar yanar gizo.

Mataki Na Farko:

Za’a je wajen kira sannan a danna *785#

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layukan Sadarwa Cikin Sauki

Sannan sai a shigar da lambar NIN dake jikin kati bayan an kammala sai a latsa “Aika” wanda aka rubuta a matsayin “SEND”.

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layukan Sadarwa Cikin Sauki

Abin Kula: Lambar kati na kasa wato NIN lambobine guda sha daya (11) ne, sannan za’a iya samun sa ne a jikin dan karamin farar takarda da ake badawa bayan kammala rajista, kamar yadda ake ganinsa anan.

Mataki Na Biyu (Amfani Da Yanar Gizo):

Domin hada layin sadarwa na MTN da kati na kasa akwai bukatan mutum ya ziyarci wannan addreshin: https://nin.mtnonline.com

Muddin shafin ya budu za’a bukaci mutum ya sanya wasu daga cikin bayanan sa wadda sun hada da:

Suna (First Name)

Sunan Mahaifi (Last Name)

Sunan Kaka (Middle Name)

Lambar Waya (Phone Number)

Lambar Kati Na Kasa (National Identity Number)

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layukan Sadarwa Cikin Sauki

Bayan an kammala saka duk abubuwan da muka lissafo sai a latsa ma bullin “Submit” hakan shine zai bada damar shiga shafi na gaba. 

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layukan Sadarwa Cikin Sauki

Jim kadan bayan latsa ma bullin “Submit” zamu samu sako a cikin akwatin wayan mu; wannan sakon na dauke da lambobin sirri guda shiga ko ma fiye da haka amma a mafi yawancin lokutan yana zuwa ne guda shida(6).

Sannan ana bukatar a sanya su cikin akwatin da aka bamu bayan latsa mabullin na submit. Abin kula: Yana da kyau a san da cewar wayan nan lambobin sirrin suna iya lalacewa bayan yan mintuna kalilan; yana da kyau mu sanyasu muddin sun shigo.

Bayan an saka lambobin sirrin sai a latsa mabullin “Submit” Yin hakan shine zai tabbatar da baya nan da muka sanya.

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layin Sadarwa Na GLO Nigeria

Yanzu za’a iya hada katin kasa da layin sadarwa na GLO ta hanyar tura sako a wannan tsarin: Da farko za’a rubuta “UPDATENIN” sai a bada sarari sannan sai a rubuta suna sai sunan baba misali: UPDATENIN MUHAMMAD ABBA sai a tura zuwa ga “109”.

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layukan Sadarwa Cikin Sauki

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layin Sadarwa Na AIRTEL Nigeria

Za’a je wajen kira sannan a danna *121*1#

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layukan Sadarwa Cikin Sauki

Bayan ya bude sai a shigar da lambar NIN dake jikin kati muddin an kammala sai a latsa “Aika” wanda aka rubuta a matsayin “SEND”.

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layukan Sadarwa Cikin Sauki

Abin Kula: Lambar kati na kasa wato NIN lambobine guda sha daya (11) ne sannan za’a iya samun sa ne a jikin dan karamin farar takarda da ake badawa bayan kammala rajista a ofishin su.

Haka zalika za’a iya amfani da shafin su dake yanar gizo ta hanyar ziyartan wannan addireshin: https://airtel.com.ng/nin/

Abu na fari da za’a yi bayan shiga shafin shine sanya lambar waya cikin akwati dake sama mai dauke da “+234”. Abin Kula: Ba’a bukatar mutum ya sanya sifili na farko da ke dauke a cikin lambar wayansa misali mai makon na sanya 0903906969 a matsayin lambar wayana sai na sanya 9039016969.  

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layukan Sadarwa Cikin Sauki

Bayan kammalawa sai a latsa kan rubutu mai dauke da “Send OTP” yin hakan zai sanya mu samu sako mai dauke da lambobin sirrin guda shida wadda zamu samu cikin akwatin sakonni dake wayanmu.

Muddin mun sami sakon sai mu sanya lambonin sirrin da aka turo mana cikin akwai na biyu. Idan har lambonin sirrin ya dace da wadda aka turo mana wani akwai zai fito a kasan sa wadda zai bamu damar saka lambar mu na katin kasa wato NIN.

Bayan Mun gama sai mu latsa mabullin “Proceed” Domin tabbatarwa.

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layukan Sadarwa Cikin Sauki

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layin Sadarwa Na 9Mobile Nigeria

Za’a je wajen kira sannan a danna *200*8#

Sannan sai a shigar da lambar NIN dake jikin kati bayan an kammala sai a latsa “Aika” wanda aka rubuta a matsayin “SEND”.

Abin Kula: Lambar kati na kasa wato NIN lambobine guda sha daya (11) ne sannan za’a iya samun sa ne a jikin dan karamin farar takarda da ake badawa bayan kammala rajista.

Har ila yau za’a iya amfani da shafin su dake yanar gizo ta hanyar ziyartan wannan addireshin: https://nin.9mobile.com.ng

Da fari mutum zai sanya lambar wayansa sannan ya latsa mabullin “Next” yin hakan zai bada damar samun lambobin sirri da za’ayi amfani dasu nan gaba.

Zamu sanya Lambobin sirrin da aka turo mana cikin akwatin da aka tanadar sannan mu latsa mabullin “Next” domin zuwa gaba. 

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layukan Sadarwa Cikin Sauki

Akwai bukatan mu dauka hoto da na’uran da muke amfani dashi wajen shiga shafin nasu domin tabbar da inganci. Za’a iya dauka hota ta hanyar latsa mabullin “Capture Camera”. Bayan mun dauka wani akwati zai fito wadda zai bamu damar saka lambobin katin mu na kasa wato NIN bayan mun kammala, sai mu latsa mabullin “Next” domin tabbatar da bayanai da muka sanya.

Yadda Za’a Hada Katin Kasa Da Layukan Sadarwa Cikin Sauki

Cikakken bayani kenan ta yadda za’a hada katin kasa da wasu daga cikin manya-manyan layukan sadarwa da muka dasu a gida Nigeria. Dafatan hakan ya taimaka matuka wajen jagora. Allah shi bamu sa’a Ameen! Kada a manta a turawa wasu daga cikin yan uwanmu domin su amfana.  



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *