Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Abubuwa Da Za’ayi La’akari Dasu Kafin Siyan Kwanfuta

Abubuwa Da Za’ayi La’akari Dasu Kafin Siyan Kwanfuta

Barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon Shirin namu wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha. Insha Allah yau zamu tattauna ne game da abubuwan daya kamata muyi la’akari dasu kafin siyan na’ura mai amfani da kwakwalwa wadda aka fi sani da kwanfuta a turance.

Wannan batu ya taso ne bisa yawan tambayoyi da jama’a suke yi lokaci zuwa lokaci na neman sanin yadda mutum zai tantance irin Kwamfutar da ta dace ya siya domin gudanar da ayyukan yau da kullum.

Kamar dai yadda wayoyin salulan zamani suke haka zalika haka kwanfuta suke, ko wani kwanfuta na dauke da abubuwa daya banbanta shi da wasu. Sanin muhimman abubuwa kafin mutum ya mallaki na’ura mai amfani da kwakwalwa (Kwanfuta) yanada matukar amfani kwarai da gaske. Abubuwan suna da yawa amma zamuyi kokarin lissafo wasu daga ciki wadda suke da muhimmanci sosai.

Jama’a da dama sukanyi la’akari da kyalkyalin kwamfuta, surarsa ko sunan kamfanin da ya kera kwamfuta, duk da cewa sunan kamfani yana da matukar tasiri musamman kamfanin da yayi jijiya wajan samar da nagartattun na’urori. To amma wasu lokutan akan yi zaben tumun dare. kaga mutum kwana biyu da siyan kwamfuta, yazo yana neman siyar da ita domin ya sayi wadda ba zata dace da bukatar sa ba. Kuma dole ne ya yi asara wajan sake siyar da ita don kuwa ba lallai a siya yadda ka siya ba ko kuma yadda kake son siyarwa ba.

Abubuwa Da Za’ayi La’akari Dasu Kafin Siyan Kwanfuta

Muddin mutum ya tabbatar bashi da ilimin fahimtar ingancin na’urori, to yana da kyau ya tuntubi wada ya sani ko kuma kwararre a wanan bangaren musamman dalibai masu nazari a fannin ilimin kwamfuta. A matakin farko yanada kyau mutum ya tantance bukatar irin kwamfutar da ta dace ya siya, ta girke (Desktop) ko ta yawo (Laptop). na biyun su kuma karfin aljihu (Budget), na ukun kuma ga su kamar haka;

Rumubn Aiki (RAM ko Memory): 

Rumubn Aiki (RAM ko Memory)


A mafi yawancin lokuta saurin masarrafi (CPU) a kwamfuta ya dogara ne da girman rumbun aiki da take amfani dashi. Dukkan ayyukan da akeyi da na’urar Kwamfuta a cikin wannan rumbu ake gudanar da shi. Kuma ana auna adadin girmansa a tsarin ma’auni na Gigabyte (GB). Saboda haka a kowacce irin bukata ana so ya kasance mai girma akalla 4Gigabyte koma fiye da hakan.

Rumbun Ajiya (Hard Disk Drive): 

Rumbun Ajiya (Hard Disk Drive):


Wannan shine abu na biyu mai muhimmanci, wannan shike da alhakkin adana dukkan aiyuka, manhajojin aiki, manhajara sarrafa na’ura ma acikin sa ta ke da sauran abubuwan da ake iya adanawa a kwamfuta. Shi ma girmansa yana taka muhimmiyar rawa wajan siyan kwamfuta. A shekarar 2014 aka samar da sabon samfurin rumbu ajiya na musamman mai suna Solid state. Ya bambanta da na asali kamar haka; Saurin aiki da kuma kasancewar sa babu tarkace masu motsi a cikinsa kamar na asali. Amma kuma yanada matukar tsada sosai. Anan mutum zai iya siyan kamar 320GB, 500GB, 650GB, 750GB ko 1Terrabyte ya dan gana da nauyin aljuhun mutum.

Masarrafi (Processor): 

Masarrafi (Processor)


shi ne a matsayin kwakwalwar na’urar kwamfuta, kuma ana bayyana saurinsa wajan sarrafa aiki a matakin GigaHertz (GHz). A koda yaushe yana da muhimmanci mutum ya siya kwamfuta wadda take mafi saurin sarrafa aiki, amma kuma ta kanyi tsada saboda saurinta shi ne darajarta.

A wannan matakin yana da kayu mutum yayi nazari akan bukatarsa ta mallakar kwamfuta da kuma irin aikin da zai yi da ita. Idan ya kasance aikin da zayyi da ita bai wuce rubuce-rubuce ba, irin na aikin ofis ko amikacin haka, baya bukatar siyan kwamfuta sama da 1Ghz na masarrafi. Idan kuma ya kasance aikin sa mai nauyi ne kamar aikin sarrafa Hotuna, Bidiyo masu nauyi da inganci sosai, to anan akwai bukatar babban masarrafi kamar 1.5Ghz zuwa 2.5Ghz ko 3.0Ghz.

Injin Sarrafa Hoto (Graphics Card): 

Injin Sarrafa Hoto (Graphics Card)


Yanada matukar fa’ida, saboda shi ne jigo wajan sarrafawa da tace hoto da bidiyo a kwamfuta domin bada ingantaccen hoto a manunar kwamfuta (Display). haka kuma akwai manhajoji wadan da aikinsu ya dogara ga ingancin hoto ko bidiyo domin samun cikakken sakamakon aikin su Misali HD Videos da Advance Games.

An fi samun na musamman masu inganci fiye da wadanda suka zo a cikin kwamfuta. Sai dai an hada su da kwamfuta ta hanyar USB ko kuma Hanyar karawa kwamfuta sassa na musamman (expansion slot).

Wasu daga cikin abubuwan daya kamata muyi la’akari da su kenan a duk lokacin da muka tashi siyan na’ura mai amfani da kwakwalwa wato kwamfuta.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *