Idan za’a tuna, fiyar (5) ga watan Yunin shekaran data gabata, gwamnatin Najeriya ta haramta amfani da dandalin twitter wadda ta zarga da taimakawa wajen ta da husuma a cikin kasar.
Ko da yake, dakatar da shafin ya biyo ne
bayan goge wani sako da shafin Twitter tayi na Shugaba Buhari.
Wata sanarwa data fito daga wajen mai
taimakawa shugaba Muhammadu Buhari a fannin kafofin yada labarai na zamani wato
Bashir Ahmad yace, gwamnati ta dauki wannan mataki ne bayan da Buhari ya
amince.
A cewar Bashir Ahmad, Shugaban kwamitin sasanta
tsakanin kasa Najeriya da kamfanin Twitter wadda shi ne shugaban hukumar NITDA
na kasa, Kashifu Inuwa ne ya sanar da wannan sabon mataki.
Karanta: Shugaban Twitter ya yimurabus saboda matsin lamba
Haka zalika Twitter ta amince ta hada kai da
kasa Najeriya don a yaki mutanen da ke amfani da kafafensu don jawo kiyayya,
kyamar juna, rabe-raben kawuna, fitina, addini, kabilanci da kuma kawo tashin
hankali a kasar Najeriya baki daya." cewar Garba Shehu.
Bugu da kari Malam Garba Shehu ya ce daga
yanzu kamfanin Twitter za ta rika biyan haraji kamar yadda suke biya a kasashen
Turai ga kasa Nigeria.
Karanta: Yadda Ake Duba Sakamakon Jarabawar Jamb Na Shekaran Dubu Biyu Da Sha Tara 2019
Ya kara da cewar irin arzikin da kamfanin
sada zumuntar Twitter ya samu a Najeriya ya dace a ce yana biyan kudaden haraji
masu yawa, .
No comments:
Post a Comment