A ranar Jumma’a, daya (1) ga watan Oktoban 2021 ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya so kaddamar da sabon nau’in kudin zamani mai suna: e-Naira, a tsarin gwaji.
Sai
dai CBN ya dage kaddamar da sabon nau’in kudin saboda wasu dalilai da ya
alakanta da al’amuran da za a gudanar a kasar na bikin cikarta shekara 61 da
samun ’yancin kai.
Haka kuma wannan jinkiri ya zo na kwana guda bayan da wani kamfani mai suna ENaira Payment Solutions Limited ya shigar da karar Babban Bankin Najeriya a gaban Babbar Kotun Tarayya kan amfani da sunan ENaira.