Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda Za’a Rage Kaushin Tafin Kafa

Yadda Za’a Rage Kaushin Tafin Kafa

 Akwai abubuwa da dama wadanda suka kamata a yi domin rage kaushin kafa ko rabuwa da shi baki daya.

Kaushin kafa yana fito wa mutum ne a lokacin sanyi sakamakon abubuwa kamar: Yawan shekaru da rashin cin abinci mai gina jiki da kuma jinsi.

Akwai nau’o’in mai da dama wadanda ake sayar da su domin magance matsalolin kaushin fata, amma yawancinsu suna da tsada.

Domin bin hanya mafi sauki wajen magance wadannan matsaloli na fata sai ku karanta abubuwan da zan lissafo muku.

  1. Kaushin kafa yana fito wa mutum ne a lokacin sanyi sakamakon abubuwa kamar: Yawan shekaru da rashin cin abinci mai gina jiki da kuma jinsi.
  2. Lemun tsami da sukari suna taimakawa wajen fitar da fatar da ke da gautsi a jiki, sannan suna sa fata haske. A samu sukari kamar cokali daya sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki, sai a rika shafawa a fuska a bari na tsawon minti uku kafin a wanke.
  3. Za a iya kwaba fiya, sannan a shafa a jiki a bari na tsawon minti 15 sannan a wanke kafin a shiga wanka a kullum. Ko kuma a hada jus din fiya a rika sha domin magance kaushin fatar daga cikin jiki.
  4. A rika amfani da man kwakwa a fatar jiki. A dora man kwakwa a wuta ya danyi dumi sannan a mulke fatar jiki kaf da shi, na tsawon minti 30 kafin a shiga wanka a kwanta. A rika yin haka a kullum.
  5. Shan madara kofi daya kafin a kwanta barci a kullum yana taimaka wa fata sosai.
  6. A rika shafa man kadanya a jiki bayan an yi wanka da dare kafin a kwanta barci. Sai a mulke jikin gaba daya da man kadanya domin samun fata mai laushi mai sheki.
  7. A samu ayaba da nono ko kindirmo sannan a kwaba a waje daya, a shafa a fuska ko fata na tsawon minti 20, sannan a wanke da ruwan dumi.
  8. A yi amfani da daya daga cikin abubuwan da na lissafo. Kada a hada duka a jiki, yin amfani da abubuwa da yawa a fata yana haifar da kuraje a fata.
  9. A shafa zuma a fatar jiki baki daya sannan a bari na tsawon minti biyar zuwa 10 kafin a shiga wanka a kullum.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *