Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Yadda Ake Hada Meat Pie

Yadda Ake Hada Meat Pie

Assalamu Alaikum Barkanmu da war haka barkanmu da sake saduwa da ku cikin Shirin namu na Girke-Girke wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha. Insha Allahu yau zamuyi jawabine akan yadda akeyin meat pie cikin sauki.

Cimakar Meat Pie na daya daga cikin kayan taba-ka-lashe kuma abun marmari na karbar baki.

A kullum muna ba uwargida shawarar kada ta bar gidanta ba komai saboda bakin ba-zata da mutane suka saba.

Za’a iya hada wannan abin makulashe ne a lokacin bukukuwa kamar Sallah ko bikin radin suna ko kuma don karbar baki da makamantan su.

KAYAN HADI:

 • Fulawa
 • Butter
 • Gishiri (kadan)
 • Nama ko kaza
 • Dankalin Turawa
 • Attarugu da albasa
 • Sunadarin dandano
 • Curry da thyme
 • Bakar hoda (Baking powder)
 • Meat pie cutter
 • Man gyada (in soyawa za a yi)
 • Oven (in gasawa za a yi)
 • Meat mincer

YADDA AKE HADIN:

Bayan uwargida ta yanka nama ko kaza, sai ta silala da sunadarin dandano da curry da thyme da albasa har sai naman ya yi laushi.

Sannan ta tsame ta zuba a meat mincer ta cakuda naman. Idan ba ta da meat mincer sai ta yayyanka naman kanana sannan ta jajjaga shi da attarugu.

Sai ta sa mai kadan a kan wuta kafin ta mayar da dakakken naman ta yayyanka dankalin Turawa, sai ta dafa shi, sai ta yanka shi kanana.

Sai ta hada da dakakken naman a wuta tana gaurayawa. Idan sun nuna tare sai ta sauke daga wuta.

Sai uwargida ta dauko fulawarta ta zuba butter kamar karamin cokali biyu da bakar hoda da gishiri kadan.

Sai ta yi ta kwabawa da dan ruwa kadan. Sai ta yi masa kwabin cincin. Sannan ta sa shi a tire filla-filla kamar za ta yanka cincin.

Sai ta dauki Meat Pie Cutter ta yanka. Sannan sai ta zuba kayan su naman da dankalin a tsakiyar Meat Pie Cutter sai ta ku ninke.

Ta soya ko kuma ta gasa shi a gas. Lallai sai kunnen maigida ya yi motsi.mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *