Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Dabi’u Bakwai (7) Da Za Su Tabbatar Maka Da Farin Ciki Da Koshin Lafiya

Dabi’u Bakwai (7) Da Za Su Tabbatar Maka Da Farin Ciki Da Koshin Lafiya

A ganina, samun farin cikin kowane mutum hakki ne da ya rataya a kansa. Kuma ma, a duk lokacin da ka fawwalawa wani dan adam ko ka damka masa ikon samuwa ko rashin murna da farin cikinka, daga wannan lokaci ne za ka yi ban kwana da farin ciki da murna dawwamammu.

Wannan hasashe nawa ba wai yana nuna ba za ka iya samun farin ciki daga wani ba, a’a. ‘Yan uwa, iyali, abokan arzuka da wasau da za mu hadu da su akan hanyarmu ta zuwa wani wuri, hanyoyi ne na samar da farin ciki a tare da mu. Amma dangantarkarmu da su komai kusacinta kuma komai nisanta ba dalili ba ne na mu hannunta musu mukullin budewada rufe farin cikinmu.

Ita ma lafiya kamar murnarmu da farin cikinmu, sau tari a hannunmu take. Allah shi ke bada lafiya, amma kiwon lafiyarmu hakinmu ne kuma wajibinmu ne mu yi duk mai yiwuwa wajen nema hanyoyin da za mu nemawa kanmu farin ciki da koshin lafiya. Kuma in mun same su, kar mu tsaya a nan, sai mu ci gaba da rainonsu da duk karnmu.

Ga wasu hanyoyi guda 8 da za su taimaka maka kasancewa cikin farin ciki da koshin lafiya a mafi yawan lokutan rayuwarka:

 

Kar Ka Taba Kawowa Barcinka Cikas: Dan uwa, in har ba ka samun wadataccen bacci to ina mai tabbatar maka da cewa duk wata dabi’a ko hanya da za ka bi wajen inganta lafiyarka da samun nishadi da farin cikinka ba zai haifar da wani sakamako mai kyau ba. Akalla ka samu barcin dare da bai gaza na sa’o’i 7 zuwa 8 ba.

Kar Ka Zama Bola; Wajen zuba Sharar Kowa: Daga lokacin da mutane suka fahimci kana ketare iyakarka wajen warware matsalarsu, wajen ciresu daga damuwarsu, wajen dadada musu, daga wannan lokaci ne fa za su ci gaba da tattaro duk wani shirgi da shirme da nauye-nauye su jibga maka don ka warware musu ko da kuwa hakan kai zai jefa ka cikin damuwa. Nunawa mutane akwai iyaka a irin taimako, agaji, ko farin cikin da za ka iya basu. Kada ka faranta ran wani ta hanyar jefa kanka cikin matsala da damuwa.

Kar Ka Jira: Kar ka jira sai abubuwa sun kyautata kan ka fara. Ka fara iya yadda za ka iya. Ka zama daga cikin wadanda suka samo mafita a kowace harka.

Kar Ka taba Kokarin Zama Wani: Kowane mahaluki da yadda Allah ya hallice shi kuma akwai iya abinda zai iya yi. Wasunmu sunfi wasu ruhi mai karfi, wasunmu sun wasu karfi na jiki, haka ma karfin aljihu. Kuskure shi ne ka so yi irin kitson kan wane alhalin ba ka da irin sumarsa. Za ka iya kwatanta abubuwan alkhairi da wasu suke yi, amma ka yi su a matsayinka na kai din asali.

Zama Gwani Wajen Iya Sarrafa Damuwarka: Ababen da za su iya kawo mana damuwa wasu abubuwa ne da ba mu da tasarrafi wajen faruwarsu ko akasin hakan. Sau tari, damuwa na zuwa ba tare da bamu wata alama ba. To, tunda bamu da iko wajen kare faruwar damuwa, sai mu zama masu iko wajen kare kanmu daga illar da damuwa ke jefa mutum. Illolin damu a tare da mu na shafar lafiyarmu, yanayinmu, alakarmu da abokan zamanmu, kai wani lokaci ma ya shafi al’umma baki daya in muka amayar da shi ta hanya mai tsananin dafi. Hanyoyin da ake magance damuwa sune: Karanta Al’Qur’ani ko sauraren karatunsa, sauraren wa’azi, samarwa kai da nishadi ta hanyoyin da ka san kana samun nishadi, karanta azkarai, yin wasannin motsa jiki da dai sauransu.

Ka Inganta Imaninka: Addinin musulunci ya zo mana da ginshikai guda 6 na imani. Imani da su wata hanya ce da za ta samar maka da nutsuwa, farin ciki da nishadi, wanda hakan zai samar da inganci ga lafiyarka. Ka yi imani da Allah, da manzanninsa, da mala’ikunsa, da litattafansa, da ranar karshe (lahira) sannan ka yi imani da kaddara mai kyau da maras shi.

Zamar Da Kanka Karamin Yaro: Da zarar mun fara girma sai ya kasance mun daina gwada wasu abubuwa saboda muna tanunin gwada yin abubuwa yarinta ne. Kamar yadda aka ce ba a cewa yaro ya da garma, kai ma kar ka yar da garmarka har sai ka tabbatar garmar ba za ta amfana maka ba. Yaro ko za ka kwana kana nuna masa cewa in ya rike tukunya a kan wuta za ta kona shi ba ya gamsuwa sai ya faki ido ya taba, daga ranar da ya taba ya ji, zai samu wani ilimi na musamman wanda a gaba shi ma zai iya bawa wani shi. Ka zama kana gwada duk wani abu da tunaninka ya gamsu zai haifar maka da farin ciki ko da kuwa makusanta za su fada maka ba zai yiwuwa ba, in ya yiwu, kalas, in bai yiwu ba ka samu ilimi kan wannan darasi na rayuwa.



mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *