Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Abin da uwargida za ta yi don kyautata mu'amalarta da kishiyarta

Abin da uwargida za ta yi don kyautata mu'amalarta da kishiyarta

 Shirin ya yi duba ne kan yadda uwayen gida za su gyara zamantakewarsu da amarensu ko kishiyoyinsu da sauran mutanen gidansu.

Uwargida ran gida... Uwargida sarautar mata... Uwargida jagorarar gida... Kirarin dai da yawa ba sa lissafuwa.

Mun san cewa kishi halitta ce a jikin kowace mace, amma kuma a ko yaushe a kan so a yi halattcen kishi wanda babu cuta ba cutarwa a cikinsa.

Mafi akasari a gidajen aure a al'ummar Hausawa Musulmai, za a samu cewa akwai mce fiye da ɗaya kamar yadda shari'ar Musulunci ta ba da ikon auren mata har huɗu idan da hali.

Sai dai duk da hakan, mata da yawa su kan samu kansu a yanayi na kishi, daga kan ita uwargidan har kan wacce za a kai a matsayin ta biyu ko ta uku ko ta huɗu.

Irin wannan kishi wasu lokutan uwargida kan fara shi tun ma kafin a ce mijin ya furta batun ƙaro auren. Wata ma tun a auren fari ita da mijin kafin ma su kai ga yin auren za ta fara nuna wa saurayin nata kishi ƙarara ta yadda ba ta so ta buɗi ido ta gan shi da wata.

Irin wannan kishi a mafi yawan lokutan ya kan saka mace cikin damuwa da sukurkutar da ita.

To ko mece ce mafita ga irin wannan lamari?

To ko mece ce mafita ga irin wannan lamari?

Eh na san kishi akwai ciwo, amma ki tuna cewa dama can ba ku yi ajanda da shi cewa ba zai kawo miki wata ba.

Ki kuma tuna cewa ko ba a kanki ba a cikin danginki ba za a rasa wacce ta je a ta biyu ba. To irin adalci da kyakkywar zamantakewar da kike so a yi da ita, ke ma ki daure ki yi da wata.

Wani fitaccen dan fim, furodusa, kuma mai ba da umarni, sannan mai rubuta waƙe Malam Ibrahim Mandawari a wata wakarsa ta fim ɗin Ki Yarda Da Ni na Anti Bilkin Funtua, ya ce: Ina yin kira gun matan cikin duniya, ku ɗau haƙuri in an zo batun kishiya.

"Ku san kishiya sunna ce ta Al-Mustapha, mijin Aisha yardajje mijin Mariya."

Sannan shi ma Sha'iri Bashir Dandago a wata waƙarsa ya ce "uwargida taho ki riƙe kishiya ba abar gaba ba, ai ƴar uwarki ce zama da kishiya ba haramun ne ba."

Matakin farko shi ne uwargida lallai ki sani cewa ke ce tubali na gyara kafatanin gidanki.

Idan kika kyautata mu'amalarki kuka kafa tushe mai kyau na zamantakewa ke da maigida to haƙiƙa za ki zama tauraruwa kuma gidanki zai zama abin kwatance, ko da kuwa mata uku zai ƙaro bayan ke.

Ya ƴar uwata uwargida ki sani cewa muƙaminki shugabanci ne, shi kuwa shugabanci yana nufi jagoranci cikin adalci, yana nufin jajircewa.

Shugabanci yana nufin kyautatawa duk wanda ke zaune da ke daga kan mijinki da danginsa da wasu matan nasa da ya auro bayan ke, da ƴaƴansa kafatan da ma'aikatansa.

Idan kika lura za ki ga a shekarun baya a kan kira uwar gida da sunan Yaya a gidajen iyayenmu da kakanninmu.

Ko kin san me yasa ake mata wannan karamcin? Sabo da ta rungumi kowa hannu bibiyu, kama daga sauran matan mai gida da kuma ƴaƴan gidan. Kishi wanda yake ɗabi'a ce tamu, bai sa ta ce kowa ya yi ta kasan ba.

Ki sani cewa ke ce fitilar da za ki haskawa sauran mutanen gida don bin hanya mai kyau. Sannan ki fahimci cewa ba alfarma za a yi wa amaryar da za a auro miki ba, yadda kika zo ibada ita ma haka za ta zo ibada.

Ki daure ka da tsananin kishinki ya bayyana ƙarara, don kuwa hakan na iya janyo miki raini maimakon ganin girma daga wajen amarya.

Tun daga lokacin da mijinki zai zo miki da zancen aure ki daure ki danne zuciyarki, kar ki dinga ƙoƙarin sanin abin da yake ciki.

Ki kama kanki sosai ban da yi masa shisshigi da katsalanda, sannan ban da tozarci da wulaƙanci.

Idan biki ya zo ki tsaya masa tsakani da Allah a inda ya dace, kar ki shiga hurumin da ba naki ba.

Kar ki ce za ki yi amfani da kissar da ba ta dace ba ki mamaye masa hidima ki hana amarya rawar gaban hantsi, ki bar ta lokacinta ne, ke kuma ki kame a inda ya dace.

Ga ƙarin wasu ƴan dabaru da za ki bi don jin daɗin zaman naku kamar yadda ƙwararru irinsu Sheikh Ibrahim Khaleel da marubuciya Anty Bilkin Funtua suka bayyana:

 • Ki zama mai haƙuri
 • Ki kama girmanki
 • Ki ja amarya a jiki amma ba don ki cutar da ita ba sai don ku fahimci juna har zama ya yi dadi
 • Ki dinga sanya ta cikin al'amuran cikin gida irin su "zo ki taya ni mu yi kaza, zo mu yi kaza," sai dai kar ta sakar mata komai ita kaɗai don gudun kar a ce ta mayar da ita ƴar aikinta
 • Ki zama abar koyi ta gari
 • Kar ki zafafa kishinki a kanta a gabanta
 • Kar ki bada ƙofar da za a dinga kawo mata labara
 • Ki wanzar da gaskiya da amana a cikin gidanki
 • Ki zama babbar bishiya, ba babbar kwabo ba
 • Ki zama mai tausayi da jin ƙai ...
 • Ki zama mai sauraro da iya bayani ...
 • Sannan ki tsarkake zuciyarki ... ban da karfar baka. Karfar baka shi ne ki guji dinga haɗa wa amaryarki sharri ko yin kutungwila a wajen mijinku. Ki sani cewa ALlah Yana kallo kuma ba ya barin haƙƙin wani a kan wani.

A ƙarshe zan ba ki wani sirri. Uwargida ki daure ki iya rabo. Ina nufin rabo kowane iri ne daga abinci har na makuɗan kuɗin da maigida zai dinga baku akai-akai ladan gyara zamantakewar gidanku.

Duk wadannan abubuwa za ki yi su ne don tsaro ba don tsoro ba.

Mu tara a mako na gaba don duba zamantakewar amare masu uwargidaye.mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *