Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Illolin Amfani da VPN

 

Illolin Amfani da VPN

Tun bayan da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dakatar da amfani da shafin Twitter, wasu 'yan kasar da dama suka rungumi tsarin amfani da wata manhaja ta zillewa hanin da ake kira VPN wajen ci gaba da amfani da shafin.

Manhajar na aiki ne wajen haɗa wayar mutum da sadarwarsa ta Internet ba tare da wata barazana ba, sannan idan ka hada manhajar da Internet dinka, wannan zai ba ka cikakkiyar kariya wajen ziyartar shafukan da watakila aka dakatar.

Akwai manyan nau'ikan manhajar ta VPN guda biyu, waɗanda ake iya amfani da su a kyauta da galibi su 'yan Najeriya suka fi amfani da su, da kuma waɗanda sai an biya kuɗi.

Amfani da manhajar VPN ta kyauta na iya jefa ka cikin haɗari, za ta iya janyo maka abunda ko da wasa baka taɓa tunani ba, gwara gwara ma wadanda ake biya kafin amfani da su domin sukan iyae kare bayanan mai amfani da su a kan kudin da bai taka kara ya karya ba.

Idan kuwa ra'ayinka shine amfani da manhajar VP kyauta, to ya kamata tun wuri ka san irin kaulbalen da ke tattare da hakan, gasu a ƙasa za mu yi bayani daki dai.

Za a iya satar bayananka

Illolin Amfani da VPN

Ɗaya daga cikin muhimman dalilan amfani da manhajar VPN shine ganin an kare ka daga masu kutse, to amma fargabar ita ce maganar gaskiya wasu manhajojin na VPN na kunshe da wani siddabaru da ake amfani da shi wajen satar bayananka da kuma amfani da wanan dama wajen aiwatar da wata mummunan manufa da ake son cimmawa.

Irin waɗannan manhajoji na kyauta na VP na amfani da tallukan da suke sanyawa masu amfani da su wajen wawashe bayansu, kasancewar sun dogara ne da 'yan tallukan da suke samu wajen samun kudin shiga.

Ana bibiyar duk ayyukanka

Illolin Amfani da VPN

Babban dalilin da ya sa mutane ke amfani da VP bai wuce kare sirrinsu a lokacin da suke bincike a Internet ba, to sai dai yawancin manhajojin VPN na kyauta na da wasu mutane da aka sanya da ke bibiyar abubuwan da ke faruwa a cikinsu, suna tattara bayanan masu amfani da su, don haka a wannan bigire maimakon a aiko maka da wani tsari da kake da damar amincewa da shi ko ka latsa kalmar a'a, sai kawai a tunkudo maka talla, wanda a lokacin da kake kallonsa sai kuma a rika kwasar bayananka salin alin ba tare da ka danna komai ba.


Iyakance Bayanai

Illolin Amfani da VPN

Yawancin VPN na kyauta na iyakance adadin bayanan da za ka iya amfani da su. Suna yin wannan ne don tura masu amfani da su zuwa tsarin da ake biyan kuɗi kafin a samu cikakkiyar damar yin abunda ake son a yi, kamar yadda Hausa kan ce ne ''Iya kudinka iya shagalinka''.

Manhajar VPN ta kyauta na haifar da jinkiri wajen samun bayanai a Internet, abun da ke kawo damuwa ga wanda ke amfani da su, to dalilin shine yawancin mutane na raja'a ne ga na kyautan don cin bulus.

Sannan su kansu tallukan da suke sanyawa da zummar satar bayanai na iya haifar da rashin saurin na Internet, dalilin sanya tallan shine tunda masu amfani da su garabasa kawai suke ci, to bari su tallata wata haja tunda dama masu karin magana sun ce ''Da ruwan ciki ake jan na rijiya''.


Barazanar harbuwa da cutukan intanet

Illolin Amfani da VPN

Manhajojin da ake amfani da wasu wajen sada waya ko na'urar kwamfuta da Interner na ɗauke da wasu hanyoyi da yawa da ake sanyawa a cikinsu wajen satar bayanai ko yin kutse ko shirya wata kutunguila.

Wasu manhajojin na VPN da ake amfani da su a kyauta ana tsara su ne da zummar cewa masu su na da ikon sarrafa bayanan mutane yadda suka ga dama, kuma suna ba da wannan ikon ga abokan cinikinsu masu biyan kuɗi don riba.

Wannan yana da matukar hadari kamar yadda masu aikata laifuka ta yanar gizo ke iya yin amfani da wannan yanayin don ƙaddamar da hare-hare kan masu amfani da VPN da basu da masaniyar duk wannan al'amari.

Manhajojin VPN na tattare da cukumurda iri iri da ke da bukatar zuba kudi da yawa a harkar don samar da kariya da kuma tsare bayanan masu amfani da su,

Akwai kuma buƙatar masu su, su riƙa sabunta tsare tsaren bada kariyar da suke amfani da su a kai a kai dai dai da zamani domin tabbatar da kare abokan huldarsu.

Sai dai kash, rashin mayar da hankali ga wadannan abubuwa da suka kamata ne ya sa masu manhajar VPN ta kyauta ke cin karensu ba babbaka ta hanyar cusa talluka da wasu tsare tsare da ke zaman babban haɗari ga masu amfani da manhajar.

A ƙashin gaskiya, wannan ba wai kawai abu ne mai matuƙar haɗri ba, ya kuma ci karo da dokokin bayar da kariya da tsaro da su kansu ka'idojin amfani da manhajojin na VPN.


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *