Yadda ake jus din gurji mai zobo
Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin
namu na girke girke wadda yake zuwa muku kai tsaye daga mujallar Duniyan Fasaha
tare da fata ana cikin koshin lafiya. Yana da kyau a san yadda ake yin nau’ukan
girke girke da kuma mahadinsu. Ina nufin jus ke nan. Duk dadin abinci yana
bukatar mahadi da zai dada wa girkin armashi. Don haka ne a yau na kawo muku
yadda ake wata mahadar girki; jus din gurji.
Abubuwan
da ake bukata
·
Gurji
·
Kankana
·
Ayaba
·
Lemu
·
Amfuna
·
Gwanda
·
Zobo
·
Flaba
·
Sakari
·
Citta
·
Kanumfari
Hadi
A sami gurji kamar goma sai a fere sannan a
markadasu a na’urar markade a tatse ruwan a ajiye a gefe. A sami kankana a
yayyanka kanana sosai a wata roba da ayaba da amfuna da gwanda duka a
yayyankasu kanana sannan a ajiye a gefe.
A tafasa zobo da kayan kamshi kamar su citta
da kanamfari da kuma bawon abarba. Sannan a tafasa sosai sannan a tace a ajiye
ya huce sannan a zuba sukari da flaba sannan a sanya a gidan sanyi.
Bayan haka, a debo wannan ruwan gurjin a zuba
a zobon sannan a zuba wadannan yankakken ’ya’yan itatuwan a zubasu a kofi
sannan a zuba wannan jus din zobon. Ana sha ana tauna.