|
ABUBUWA 8 DA ZA AYI LA’AKARI DA SU KAFIN ASIYA WAYA KO TABLET (SMARTPHONE
|
Idan aka
ce smartphone ana magana ne da wayar da ta cika gari a wannan lokacin wacce zai
yi wahala ka samu mutum biyu wadanda suke rike da waya amma kuma ba a samu mai
ita ba. Irin wadannan wayoyi sun cika ko’ina, ga shi kuma kamfanonin da suke
yin su kullum kara fito da sababbi suke yi kasuwa.
Kodayake a
irin tunani namu na bakaken fata kasancewar waya na da tsada shi ne ke nuna
cewar wannan wayar tana da kyau, wani lokaci kuma neman iyawa da bajinta da
nuna isa shi ke sa mu mallaki waya wacce take da tsada ba yin la’akari da me ke
cikin wannan wayar ba ko kuma me wannan wayar zata iya yi mana.
Wani abu
kuma da yake daurewa masu son su siya sabuwar waya shine, idan na samu kudi
wace irin waya ya kamata in siya, ko kuma mene ne abin yin la’akari da shi idan
ina son canza waya ko kuma sake sabuwa. Amsoshin wannan tambayar ya danganta da
me kake son yi da wayar, domin wani yana yin la’kari da karfin wayar wurin rike
wuta ko caji, wani kuma yana yin la’akari da kyau na hoto da take dauka, wani
kuma yana yin la’akari da karfin network da take da shi, wani kuma yana yin
la’akari da girman fuskarta, da dai makamantan wadannan.
1. ==> GIRMAN FUSKAR WAYAR
A wurin
siyan waya ko tablet mutane suna yin la’akari da girman fuskar wayar wato
(screen). Wani yafi so ya ga waya faskekiya a wurin sa, wani kuma baya son
ganin haka. To shi dai maganar fuskar waya ra’ayi ne, kuma wanda yayi maka ba
dole ba ne yayi wa wani. Amma dai a zahiri idan kasan kai mutum ne mai son
wayarka ta rika zama da caji to girman fuskar waya da barin ta cikin haske
sosai na taimakawa wurin cinye caji.
2. ==> KAURI DA NAUYI
Kauri da
nauyin waya abu ne mai muhimmanci a lokacin da mutum zai sayi waya ko tablet.
Kauri dai an fi lura da shi akan komai, wani lokaci sirantaka a wurin kayan
computer bai cika bayar kaya masu inganci ba a wani lokaci. Saboda haka ya
danganta gare ka idan kana son kyau fiye da inganci sai ka tsallaka siriyar
waya ko tablet. Kodayake wadansu wayoyin suna da jikin karfe ne saboda haka tun
kafin kabar wurin siya ka tabbatar ka duba don kada karfen ne ya sata tayi
nauyi.
3. ==> MANHAJOJIN (Operating System) DA
WAYA TAKE AMFANI DA SU
Babbar
Manhajar da take sarrafa komai da ke jikin waya shi ake kira da Operating
System, shi yake lura da hatta maballan da kake tabawa wurin kunnawa da
kashewa, shi yake lura da sauti da kalan da yake fita a wayar. To lallai wurin
siyan waya yana da kyau ka duba da kyau domin ka san wane irin manhaja ce a
cikin wannan wayar. Kamar yadda da yawa daga cikin mu suka sani cewar wayoyin
da muke rikewa suna da banbanci wurin gininsu da kuma wane ne yayi su? Kunga
dai wayoyi idan ya zo ga maganar Operating System akwai na Android, sannan ga
iOS, sai Microsoft Phone 7, sai Blackberry ga kuma web OS da Symbian, dukkan
wadannan da na lissafo da yawa daga cikin mu sun dauka cewar waya ce. A a
kamfani da yake yin karfe da kyan da suke jikin waya daban sannan manhajar da
ake saka mata da ba. Wadancan sunaye da aka ji na lissafo mutane sun fi sabawa
da su a matsayin waya maimakon Babbar Manhaja ce.
4. ==> WURIN ADANA BAYANAI
Mafi yawan
kanfanonin da suke yin wayoyi da tablet a wannan lokaci suna kokarin ganin sun
yi mata mazubi da ya kai girman gig 16GB, wanda zai baka dama domin a jiyar hotuna
da rubutu da sauti da hotuna masu motsi. Kodayake wadansu saboda yanayin yadda
suke tara abubuwa a cikin wayoyinsu suna bukatar karin abubuwa a ciki. To a nan
yana da kyau ka sani wayoyin da kamfani Apple suke yi su basa bada ramin kara
ma’ajiya wato Memory, saboda haka idan kasan kai mai sun ajiyar abubuwa ne sai
ka nemi koda wayar Apple amma mai mafi girman mazubi.
5. ==> KARFIN SHIGA INTERNET
Kusan
dukkan wayoyin tafi da kidan ka suna zuwa da tsarin sadarwa maras waya
(wireless) wanda ya ke basu damar iya kulla alaka tsakaninsu da ko kamfanin
layukansu ko kuma hanyoyin shiga intanet da yake gida ko kuma ofis da dai
makamantansu. Irin wadannan hanyar da ake amfani da ita domin samun sinadarin
shiga intanet ba tare da amfani da layin waya ba shine ta hanyar amfani da
Wai-Fai (Wireless Fidility). Amma yana da kyau wanda zai sayi waya a wannan
lokaci ya san cewar yanzu ma muna karni na uku bane 3G (Third Generation) ta
wurin shiga intanet, a’a a wannan kasa yanzu haka akwai kamfanoni da suka
tsallaka karni na hudu 4G.
Wayoyin da
aka yi a baya sun fara ne da 1G sai kuma suka shiga 2G wanda irin wadannan
wayoyin ba sa ba msutum damar shiga intanet da sauri, koda kuwa a inda mutum ya
ke akwai network mai kyau da karfi. Daga baya suka shigo da 3G wanda yake bamu
damar har kallon hotuna masu motsi (video) muke yi ba tare da yana tsayawa ba.
Saboda haka yanzu mafi yawan wayoyin da ake yi suna baka damar amfani da karfin
network na 3G da 4G, sai a kiyaye idan an je siya.
6. ==> KANA NAN MANHAJOJI
Daya daga cikin
abin da mutane da dama suke yin la’akari da shi shine idan na sayi waya iri
kaza shin dawe application ne zan iya aiki, kusan a wannan lokaci da muke ciki
kasancewar wayoyin Android sun fi yawa da kuma saukin koyan yadda ake kirkiran
manhajojinsu, yasa mutane da dama suke son siyar wayar Android. Amma kuma idan
aka zo ga zafafan Manhajoji to sai muce manhajojin da ake amfani da su a waya
kirar Apple sun fi shahara da kwarjini.
Misalia
shagon Apple akwai manhajoji dubu dari uku na kyauta da kuma na siyarwa, a kuma
shagon Android akwai manhajoji dubu dari biyu da hamsin na kyauta da kuma
siyarwa. Suma sauran manhajoji irin su Blackberry da makamantansu suma suna da
shagunan da ake samun manhajojinsu saidai ba su kai na Apple da Android yawa
ba.
7. ==> Kamara da Nado Sauti'
Hakika
wadannan abubuwa guda biyu sun karawa wayoyin tafi da gidanka daraja, kusan a
yanzu mutane da dama suna yin amfani da kamarar jikin wayoyinsu domin daukar
shagulgulan biki da suna da taron siyasa, wa’azi, wasan kwaikwayo da dai makamantansu.
Wannan dalilin ne ya sanya wayoyi a wannan lokacin suke kara yin tsada, duk da
cewar mutane da dama basu cika kiyaye haka ba.
Kusan a
yanzu akwai wayoyin da ake da su wadanda saboda karfi da kyau yanayin hotuna da
suke dauka hatta mawaka suna amfani da su wurin shirya wakokinsu. Haka yan
jarida a wannan lokaci suna yin amfani da wayoyi wurin nado sauti da zasu iya
kai rahoto da shi. Duk da cewar karfin wata wayar ya fi na wata, amma waya da
kamara da kayan daukan sautin da ke jikinta ya mayar da mutane ‘yan jaridan
tafi da gidanka amma wasu ba su sani ba. To ba kowace waya bace ta ciki inganci
a kan haka. Sannan idan ka san kai baka damu da kyau na hoto ba to ba sai ka
sayi waya mai tsada ba.
8. ==> DADEWAR BATIRI
Lallai ko
ba a fada maka ba kasan cewar batir yana da matukar muhimmamci a jikin waya
domin duk irin aikin da waya zata yi maka idan har batirin wayar baya dadewa
abin ya zamo da shirme ke nan. Shi yasa kuwan mafi yawan kamfanonin da suke
kirkirar waya suka fi mayar da hankali wurin ganin batar na dadewa, duk da irin
kurakurai da ake samu wadansu kamfanonin suna yi sai ka samu kamfani yayi waya
kuma cikawa batirin sinadari da idan ya ji rana zai kama da wuta, amma dai suna
kokari.
Zaka samu wayoyi a wannan lokaci ana inganta batirinsu
har kaga waya tana iya kwana uku tana aiki, kodayake ba kowa yasan wayoyin
wannan lokacin suna haka ba, kasancewar idan muka sayi waya bama karanta
takardar da take zuwa da ita.
Wannan
shine abubuwan da zan iya kawo muku wadanda sune abubuwan da ya kamata mu rika
yin la’kari da su wurin sayin waya.