Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

SIFFOFIN UWA TA GARI 3


LALLE

Yar’uwata ki sani lalle kwalliyace ga duk ya mace kuma mace idan ta bar hannunta ko kafarta ba lalle to ba’a iya banbance ta da namiji. Kuma kowace irin kalan lalle da mata sukeyi kema kiyi da zaran ya goge sa ki biyoshi da wani kala domin cika siffarki ta ya mace.

BANGAREN ADO

Yar uwa  ki sani kirkire kirkiren adon zamani wajibine akanki a gidan mijinki harma da irin naki salon adon, kuma duk wata dressing da mata sukeyi a duniya dolene ki rinka yiwa mijinki matukar bai sabawa addinin musulunci ba, sannan kiyi masa ado da duk irin kayan da kika mallaka.

KISISINA DA KARERAYA

Ya yar’uwata mace bata cika mace ba idan bata iya kisisina irin ta mata ba, kamar su kareraya, yanga da rigima. Kuma ki sani irin wadannan dabi’un su suke daukaka martabar mace a wurin mijinta acikin dukkan alamuran su, Magana ko tafiya ko kallo da makamantansu.

DAMUWA DA DAMUWARSA

Yar uwa wajibine ki karanci halin mijinki sosai kisan mijinki acikin halin farin ciki da kuma bakin ciki kuma ki lura da yanayin sa a lokuta kamar haka:
Ø Lokacin fita nema
Ø Lokacin dawowa daga nema
Ø Lokacin gajiya
Ø Lokacin farin ciki
Ø Lokacin bakin ciki

Ø LOKACIN FITA NEMA: A wannan lokaci yaruwata ki sani dolene ki tabbata mijinki ya fita daga gida cikin kwanciyan hankali da natsuwa. Akwai wani dabi’a da matan magabata sukeyiwa mazajensu, su kan shirya bayan sunyi wanka da kwalliya sannan sai su raka mazan su har kofar gida ko kofar daki, sannan suna tafiya suna taku daddaya da rangwadi kuma su kan yimusu addu’a sannan su basu wasiyan cewa idan Allah yasa ka samu halal ka kawo mana, idan kuwa baka samu ba zamuyi hakuri da azabar yunwa akan azabar Allah. Bayan ya fita yayi nisa sai ki kirashi da wani sunan soyayya mai dadi sai kiyi masa Kiss da hannunki. Sai kice masa Allah ya bada sa’a. Allah ya sa mudace Ameen.

Ø LOKACIN DAWOWA DAGA NEMA: Ki sani yar’uwata miji yana dawowa gida a halin gajiya kafin ya dawo kin shirya ma dawowarsa.

Ø LOKACIN GAJIYA:A wanna lokaci ki sani zaki nemi ruwa mai dumi a lokacin sanyi idan kuma lokacin zafine, sai kinemo ruwan sanyi ki kai masa wurin wanka bayan ya gama wankan ya dawo daki ki bashi abinci

Ø LOKACIN FARIN CIKI: Yar’uwata a wannan lokacine zaki baje kolin shagwabar ki da rungumarsa

Ø LOKACIN BAKINCIKI: Yar’uwata a wannan hali babu wasa babu tsokana a tsakaninku har sai kinji mai ya bata masa rai, idan ya fita bai samo bane sai ki kwantar masa da hankali, sai ki nuna masa kullum Allah yana basa sai kawai don yau baka samo ba sai muyi hakuri mu godewa Allah. Idan kuwa wani ne ya bata masa rai, sai ki bashi hakuri da kuma kwantar masa da hankali, sannan idan ya dawo miki cikin tashin hankali sai ki warware masa bayan kinji mai ya faru dashi. Idan ba zaki iya warware masa ba sai ki kaishi inda za’a warware masa damuwarsa.

IYA ABINCHI

Rashida wallahi wannan shine babban hanyar sace zuciyar miji idan har kin iya abinci sosai, wallahi sai dai kiji mijinki yana cin abinci yana santi yana kuma cewa amarya Allah ya miki Albarka harma ya miki kyauta sakamakon santin cin abincin. Sannan ba zai taba jin tsoron duk bakon da akayi ba ta bangaren abinci kam ko da kinyi masa laifi sai yace ya yafe saboda santin abincin.

mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

No comments:

Post a Comment

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *