Ba shakka rake na kunshe da ruwa mai yawa, haka zalika rake yayi fice wajen zaki mai sanyaya rai da kuma sanya nishadi, hakan ne ya sanya Hausawa ke danganta maganar wadda ke shan rake a matsayin santi. Wasu daga cikin amfanonin rake sun hada da:
1.==> Yana kara ruwan Jiki da karfi musamman ga masu aikin karfi ko aiki cikin rana.
2.==> Yana taimakon Koda wajen fitar fitsari da kyau.
3.==> Yana karfafa garkuwan Jiki. Yana taimakawa wajen kamuwa da cutar sanyi mura da cutar daji.
4.==> Yana taimaka wa Hanta, Zuciya, Ciki, Ido, Kwakwalwa da Al’aura wajen yin aikinsu yadda ya kamata.
5.==> Yana gyara Fata ya kasance yadda ake bukata.
6.==> Gara ka sha Rake da ka sayi lemun kwalba don yafi su amfani ga lafiyar jiki
7.==> Yana wanke Hakora (amma yana da kyau a kuskure baki bayan ansha saboda kwayoyin cuta na iya samun zakin a matsayin abinci).
8.==> Yana maganin yunwa kuma baya da illa ga masu cutar ciwon sukari (masu fama da diabetes su kula kada su sha da yawa domin zai iya kasancewa guba a garesu).
9.==> Shan rake na inganta lafiyar hakora
10.==> Shan rake na samarwa jiki Karin ruwa domin yin aikinta yadda ake bukata
11.==> Yana rage amai ga mata masu dauke da juna biyu
12.== > Shan rake na maganin kumburi ga mata masu ciki
13.==> Yawan shan rake na kara inganta lafiyar kwakwalwa
14.==> Shan rake na kara inganta lafiyar idao da kara karfin gani
15.==> Rake na daidaita adadin sugan dake cikin jinni
16.==> Yawan shan rake na hana cushewar ciki
17.==> Shan rake na gayara fatan jiki
Wasu daga cikin amfanonin shan rake Kenan ga lafiyar jiki, yana da kyau mu kara adadin shan rake domin hakan zai taimaka wa lafiyar jikinmu sosai.