KAFIN NA FARA
JAWABIN BAN YARDA A JUYA WANNAN SAKO TA KOWACCE HANYA BA, HAKA KUMA BAN YARDA A
CIRE WANI ABU DAGA CIKI BA TARE DA CIKAKKEN IZININA BA KO WANI DAGA MUJJALAR
DUNIYAN FASAHA KO KUMA SHAFIN HANYAN TSIRAH. A KIYAYE! WANDA KUMA YAYI MUN
BARSA DA ALLAH. A MATSAYINKI NA MACE BUDURWA INDAI KINSAN KINA SOYAYYA TO
KIKULA DA WANNAN SAQO KI KARANTASHI.
1.
ki tsayar da saurayi guda daya tak na kirki bisa la
akarai da ayyukan sa da halayensa na zahiri.
2.
kitabbata kina sonsa sosai kuma shima yana sonki sosai.
3.
Kada ki yarda kidade da saurayi, ko kishaqu dashi ko ki
nuna masa tsananin so batare da iyayensa sun gana da iyayenki ba. In yaqi
turosu kirabu dashi tunkafin yagama sace zuciyarki.
4.
Kizama mebin shawarar iyayenki, da neman shawararsu a
harkar soyayya, kada kibi shawarar Qawaye ko saurayi kobin shawarar zuciyarki.
5.
Kada kiyarda a kawo miki gulmar saurayinki ke kuma
kidauka koki kama zargin sa. A'a sai kinyi bincike na adalci ko kingani da idonki.
6.
Kada ki kuskura kiyiwa saurayinki qarya kizama me fada
masa gaskiya, da yimasa bayanin komai iya saninki.
7.
Kizama me yawaita addu'ah da bawa Allah zabi a dukkan
lamarinki.
8.
kikiyaye zargi da binciken laifinsa matuqar ya sanar
dake komai bai 6oye miki gaskiya ba.
9.
kidauka dan adam tara yake bai cika goma ba, kinga zai
iya kuskure, dan haka sai kiyi masa afuwa.
10.kizama me kare mutuncin kanki, da
kuma kulada matsayinki batare da girman kaiba ko jan aji ga masoyi... JAN AJI A SOYAYYA BA ABIN DAYAKE HAIFARWA SAI
NADAMA. idan saurayinki ya tsaneki ko yagudu yabarki ko kin rasa wani abu
da yake baki, kiyi haquri kada kijuya masa baya, kisa masa shakka a ransa yadinga
tunanin anya kuwa kina son sa da gaske???
KEDAI
KAWAI KI KARE MUTUNCINKI DA IYA TAKUNKI.
11.Kada kiyarda ki sakarwa saurayinki
fuska yana shigo miki da kalmomin da basu daceba ko dabi'u. kamar yace zai
samiki zobe, ko zaiga awar waronki ko zaisa miki jaka, ko zaiga fulawarki ,ko
zai auna kaurinki dadai sauransu.
SABODA
HAKA KIZAMA ME BATA RAI ADUK SADDA KIKAGA HAKA, KODA YATAFI KIRABU DASHI, DAMAN
BA NAGARI BANE, SOYAKE YA BATAKI. Wakilin shaytanne.
12.Kizama me yiwa saurayinki Al-qawarin
nuna masa soyayya bayan aurenku, sannan dayi masa biyayya dai dai gwargwadon iyawarki.
KISANI
DAYAWAN SAMARI AKWAI MAKIRCI. Wani yasan ba aure zaiyi ba amma zaizo
yabata miki lokaci. Wani soyake yakoyi zance sai kawai yazo wajenkibyayi tayi
miki qarya batare dakin fargaba zai dasa miki ciwon so, YA KORAR MIKI SAMARIN KI NAKIRKI. Wani kuma kawai so yake yana zuwa
wajen fati dake. Saboda haka zaina saya miki kaya kala kala yana fira da ke zai
fake da cewa SAI YAGAMA School KO SAI
BAYAN YAGAMA KARATU ZAI TURO KUYI AURE.
Duk fati ko fikines zai daukeki kutafi. Wani
kuma soyake kawai yana taba jikinki yaji dadi koda bai kwanta dakeba, saboda haka
zaita binki sauda qafa yana soyayya dake. Wani kuma so yake ya bataki. Irin
wadannan samarin sunfi kowanne hatsari. Idan yaganki yana sonki yana fara
karantar halayenki IDAN YAGA KE
USTAZIYACE TO ZAIYI SHIGAR USTAZAI HARDA LITTAFIN SA A HANNU, HAKA ZAITA KAFA
MIKI TARKO HARSAI KIN FADA.
Idan yaga 'yar BOKOCE zai fito miki a dan
boko. Idan yaga ke yar duniya ce toshima a hakan zai fita.
Irin wadannan samarin har kayan mungani
munaso suna kaiwa budurwa, har iyayensu suna turowa daga qarshe daya kwanta
dake shikenan yabiya buqatarsa, bazai bari kisami cikiba zaibaki kwaya da zarar
yaga baki da ciki yasan yayi free tunda yasami abinda yake nema, zai Qirqiri
laifi yalaqamiki domin ku6ata a karbo kayan sa daga gidanku, koma yabar miki
kayan...
Irinsu akwai makirci da nuna tsagoran
soyayya ga budurwa, domin sukanyi kukan hawaye a gaban budurwa duk da sunan so
amma yawanci domin ya raunana zuciyar kine. Yakan maqale miki har unguwa yana
rakaki koda yaushe.
YAR UWA IN SOYAYAYYA TAI GARDAMA WAYE YAFI
SHAN WUYA DA TOZARTA ??? SHIN ANAIWA NAMIJI CIKIN SHEGENE KO BUDURWA AKEWA??? IDAN
ABIN KUNYA YAFITO WAYE ZAI ZAUNA A GIDA KO MAQOTA BAI ZUWA DAN KUNYA NAMIJI KO
MACE??? MEYASA NAMIJI ZAI IYAYIWA YAN MATA BIYAR CIKI BATARE DA AURE BA AMMA
INYAZO NEMAN AURE SAI ABASHI??? IDAN KUWA MACE TAYI CIKI SAU DAYA DA KYAR TAKE
AURUWA KOMA SAI TABAR GARIN??? MEYASA MACE INTAI CIKI AGIDAN SUMA TSANARTA
AKEYI, AMMA NAMIJI DAYA KAWO RAGO DA KUDIN ICE SHIKENAN??? MATA NAWANE SABODA
CIKIN SHEGE SUKABAR GARINSU KO RAYUWARSU TA GURBATA AMMA SHI NAMIJI KAMARMA
BAIYI KOMAI BA??? KO KAMUWA KIKAI DA MUGUN CIWO WAZAI KULA DAKE YABAKI KUDIN
MAGANI DUK WATA??? KINTABA GANIN ANSA WUQA A WUYAN NAMIJI ANCE INBAKA FADI
WACCE KAYIWA CIKIBA SAINA YANKAKA??? AMMA WA AKEWA HAKA???
'Yar uwa kada dadin soyayya, ko dan kudin
da saurayi zai baki kodan zai saki a gaban mota, kodan wasu yan riguna dazaina
saya miki HAKAN TASA KIBASHI DAMA HAR YASANKI 'YAMACE WALLAHI KIN KADE.
IN HAKAN TAFARU TO KITUBA GA ALLAH (S.W.T)
DOMIN SHI MAI GAFARANE. FATAN "HANYAN TSIRAH" ANAN SHINE, ALLAH YASHIGA
TSAKANIN NAGARI DA MUGU. ALLAH YAHADA KOWACE YA MACE DA SAURAYI NAGARI DA ZATA
KAISU GA AURE NAGARTACCE. MUMA MAZAN ALLAH YABAMU MATA NAGARI. BISSALAM
No comments:
Post a Comment