Tare Da
Muhammad Abba Gana
A mafi yawancin lokutan mukan yi korafin cewar bamu da kudi sannan bamu da hanyar da zamu sameta, wadda a hakikanin gaskiya bamu san wasu ba wasun kuma bamu jarrabasu bane. Sanin kowa ne dai a halin yanzu kusan ko wani daya daga cikin mu na mu’amala da kafar sadarwa ta yanar gizo (Internet) musamman dandalin sadarwa na zamani.
Muhammad Abba Gana
A mafi yawancin lokutan mukan yi korafin cewar bamu da kudi sannan bamu da hanyar da zamu sameta, wadda a hakikanin gaskiya bamu san wasu ba wasun kuma bamu jarrabasu bane. Sanin kowa ne dai a halin yanzu kusan ko wani daya daga cikin mu na mu’amala da kafar sadarwa ta yanar gizo (Internet) musamman dandalin sadarwa na zamani.
Mafi yawancin wadannan mune wato matasa yan uwana, mukan bata
kusan dukkan lokutanmu ne wajen yin chatting, karanta labaran kwallo, neman yan
mata, karanta littatafan hausa na soyayya ko yaki, neman saurayi, karatun boko,
kallon videon kwallo, wakar hausa ko misic da dai makamantansu. Wannan shine
abin da ya shagaltar da mu har ma ya sanya bamu kula da wasu manyan damammaki
da zasu iya amfanemu domin samawa kanmu wasu ‘yan kudade na a kasha, wasu
lokutan ma har yakan shagaltar damu wajen yin ibada.
A zamanin da muke ciki yanzu mutane sunfi
sha’awar aikin gwamnati mutum yana so aji ana cewa ya tafi office ko kuma yana
da hadadden office mai dauke da kayan sanyi na zamani sannan kuma a karshen
wata yana da wani kayataccen albashi mai tsoka da wannan ake rudan wasu sannan
a cusa musu sha’awar shigarta ta ko wacce hanya.
Idan kuma muka maida duba izuwa ga sana’ar
hannu zamu ga cewar akwai wasu sana’oi da dama da mutum zayyi wanda zai iya
tashi da dubu 5 koma fiye da haka wadda in an kwatanta za’a ga cewa abinda
mutum zai samu a karshen wata zai nikka albashir mai aikin gwamnati har sau
biyu ko fiye da hakan.
Wani abin mamaki ma shine kusan ko wane
matashi sai ya yi wani sana’a kafin ya
iya samun kudin da zai siya Data, amma kuma bai san ta yaya zai iya samin kudin
a saman yanar gizo (Internet).ta hanyar
amfani da datar daya siya. Insha Allahu a wannan makon, Duniyan Fasaha zata
kawo muku wadansu cikakkun hanyoyin da za’a iya bi domin neman na kashewa a
saman yanar gizo (Internet).
1.==>
HADA SHAFUKAN YANAR GIZO: Shafukan
yanar gizo abune mai matukar amfani
sabili da yana taimakawa wajen bada cikakkiyar bayani game da kasuwanci cikin sauki, A hakikanin gaskiya adadin shafuka a
yanar gizo yana ninkuwa a kowace waye war gari, haka kuma adadin masu bukata
yana kara bunkasa.
Masana kimiyya sun nuna cewar duk wata
kasuwanci da bata hadayya da yanar gizo to hakika ta na rasa wasu damammaki da
zata iya samu wajen tafiyar da kasuwancin, haka zalika alamomi sun nuna cewar
duk wani kasuwanci da bai da shafi na mussanman a yanar gizo nan da wasu
shekaru masu zuwa dole sai ya samo.
Hada
shafin yanar gizo ba kowa zai iya yinta ba sai wadda yake da ilimi sannan kuma
yake da basiran yin hakan, akwai mutane da dama wadda suka gwanance wanje
suranta shafukan yanar gizo sannan kuma sun dauke ta a matsayin sana’a.
Hada shafi a yanar gizo ba wani abu mai matukar
wahala bane sai dai ya zamana dole mutum ya koyi wasu yaruka wadda aka fi sani
da ‘programming language’ a turance
wadda ita kwanfuta ke fahimta; misali: php, python, JavaScript, ajax, java,
Asp.net da dai sauransu. ko kuma mutum
ya koyi yadda ake amfani da wordpress, wix (wadda zanyi jawabin su a wasu
makonin masu zuwa) ko kuma blogger wadda nayi jawabinsa a wasu makonni da suka
gabata. Koyon daya daga ciki ababen da na lissafo zai bada damar samun makudan kudi
a yanar gizo.
2.==>
JAGORA: Wannan wata halattacciyar
hanyace da ake samun kudi da ita ta hanyar jawo wani yayi rajista bayan anyi
sannan kuma an tabbatar da ingancinsa. A mafi yawanci sa’oi wannan damar yana
aiki ne ga manya ko kuma sabobbin shafuka dan samun mabiya da zasu taimaka musu
wajen gudanar da kasuwancinsu.
Yadda abun yake anan shine: Bayan anyi ragista
da ita kamfani a mafi yawancin lokutan sukan saka wani adadin kudi da mutun zai
samu yayin da ya gayyato wani yayi ragista dan taimaka musu wanjen tallar
hajarsu. Sukan bawa kowa addireshi na musamman da zaiyi amfani dashi wajen
gayyato mutune.
Duk sa’an da wani yayi rajista da wannan addireshin
wadda ya basa zai samu ‘yan wasu changi. Inji
bahaushe Iya kudinka iya shagalinka haka zalika ‘Yawan mutanen da ka jawo
yawan kudin da zaka iya samu’. Kamfanonin da ke samar da wannan dama sun hada
da Konga.com, alibabab.com, Jumia.com.ng, Be With Me Technology, EntireWeb,
Renkutten, Yllix, dadai sauransu.
3.==>
HADA MANHAJAR WAYA: Adadin
mutane dake amfani da wayar salula ya zarce yadda ake tsanmani, sannan adadin
yana ninkuwa a kowace wayewar gari. Wayar
salula yakan taimaka matuka wajen sa da zumunta ta hanyoyi daban daban haka
zalika adadin mahajar da ake kirkira yana kara ninkuwa a kowace safiya bisa
la’akari da yadda mutane ke sa’awar amfani da ita musamman android.
Mutum zai iya hada
mahajar waya sannan ya siyar ko kuma za’a iya biyansa ya hada hajar sai dai
wannan yana tafiyane hannu riga dana fari dole sai mutum ya koyi wasu yarukan
kwanfuta dana ambata a baya kafin cin ma manufa. Amma Alhamdullilahi a yanzu
akwai wasu shafukan yanar gizo dake bada damar hada mahajar ba tare da koyon
daya daga cikin yarunkan dana ambata a baya ba irin su Androidmob da kuma
Appgeyser. Sai dai matsalar wayan nan shafukan basu bada cikkakiyar damar
amfani da ita sai an biya wasu kudade.
Lallai ba shakka mutum
zai iya samun kudi na hakika da mahajar da ya kirkira ta hanyar saka tallace
tallace a ciki, duk sa’ar da wani ya danna wannan tallan zai samu yan wasu
changi haka zalika za’a iya biyan mutum makudan kudade dan tallata wata haja
kamar yadda zamuyi bayani a gaba.
4.==>
SAKA HOTUNA MAI MOSTI (VIDEO) A YOUTUBE: Wata hanya da ba kowa ne ya san da ita ba ko kuma yasan amfaninta ba a
cikin mutanenmu shine yadda za’a iya samin kude daga YouTube.
Wannan hanya ce mai matukar sauki. Kawai abin
da kake bukata shine ka mallaki google account (gmail). Za ran ka mallaki gmail
zaka iya zuwa YouTube domin da bude channel.
A cikin wadannan channel din ne zaka rika
dora bidiyoyinka. Domin samin kudi a duk lokacin da wani ya kalli wannan bidiyo
sai ka tabbatar ka shiga wajen settings kayi checking ko kuma ka zabi monetize, wannan zaya baka damar da zaka sami kudi a
duk lokacin da YouTube suka sanya talla a cikin bidiyonka.
5.==>
TALLA: Shima wannan wata hanya ce da ake samun
kudi a internet ta hanyar yin talla, Duk wani
wanda ya shahara da shiga Facebook zaya iya baka labarin yanda zaka ga wasu
mutane sukan leka daga wannan zaure zuwa wancan, ba kuma komai ke kai su ba sai
dai kawai suyi comment da wani link da zasu ce ka shiga domin samin wani abu.
Wadannan mutane ba komai suke yi ba face yima wasu kamfanoni talla.
Da zaran ka danna wannan adireshin da suka baka to zaka shiga a
website din kamfanin da suke yi ma tallar, su kuma za’a basu wani dan kaso na
kudi sanadiyyar tura ka da suka yi zuwa wannan shafinn. Duk da cewa wadannan mutane suna yin talla ne ta hanyar da
mutane ba kasafaye suka cika kulawa ba, kai idan kaso zaka iya yinta ta hanyar
da ya kamata.
Misali zaka iya sanar da abokanka da kuke chatting da su cewa ga
wani abu nan na karuwa shima ya shiga domin ya karu, da zaran ya shiga shima
yayi rajista shi kenan kaima zaka sami kasonka.
Wadanna
sune wasu daga cikin hanyoyin da aka fi amfani da su wajen samun kudi a
internet, shin ka/ki na da wata hanya da ka/kika sani wanda ban ambata a cikin
wannan kasidar ba? Za’a iya turo mana dan dad’awa wanda zai taimaka wa masu
ziyara nan gaba.