Shan ruwa dayawa nada matukar muhimmanci ga lafiyar jikinmu, sai de ta dayan bangaren kuma yawan shan ruwan sanyi yakan iya zama babbar matsala, domin kuwa a duk lokacin da muka sha ruwan sanyi bayan chin abinci yakan je kai tsaye ya toshe magudanar jinin jiki wadda hakan kan janyo cututtuka bila adadin kamar irinsu ciwon sugar wadda aka fi sani da Diabetes a turance, ciwon daji wato cancer da dai makamantansu. Haka zalika ruwan sanyi yakan zama tamkar guba a cikin jikinmu mussamman ga wayenda basu iya rayuwa ba tare dashi ba. Ruwan sanyi na tattare da illoli masu yawan gaske wadda zamuyi bayani a wasu makonni masu zuwa.