Shafine da ake bude dan wayar da kan mutane abubuwa wanda zai taimakesu a harkokin yau da kullum, mukan taimaka da abubuwa ta bangaren shawarwari, gyaran jiki, kwalliya da su Girke Girke

Cikkaken Bayani Yadda Ake Samun Kudi A Yanar Gizo (Internet) Cikin Sauki

Cikkaken Bayani Yadda Ake Samun Kudi A Yanar Gizo (Internet) Cikin Sauki

Tare Da 

Muhammad Abba Gana

A mafi yawancin lokutan mukan yi korafin cewar bamu da kudi sannan bamu da hanyar da zamu sameta, wadda a hakikanin gaskiya bamu san wasu ba wasun kuma bamu jarrabasu bane. Sanin kowa ne dai a halin yanzu kusan ko wani daya daga cikin mu na mu’amala da kafar sadarwa ta yanar gizo (Internet) musamman dandalin sadarwa na zamani.

Mafi yawancin wadannan mune wato matasa yan uwana, mukan bata kusan dukkan lokutanmu ne wajen yin chatting, karanta labaran kwallo, neman yan mata, karanta littatafan hausa na soyayya ko yaki, neman saurayi, karatun boko, kallon videon kwallo, wakar hausa ko misic da dai makamantansu. Wannan shine abin da ya shagaltar da mu har ma ya sanya bamu kula da wasu manyan damammaki da zasu iya amfanemu domin samawa kanmu wasu ‘yan kudade na a kasha, wasu lokutan ma har yakan shagaltar damu wajen yin ibada.

A zamanin da muke ciki yanzu mutane sunfi sha’awar aikin gwamnati mutum yana so aji ana cewa ya tafi office ko kuma yana da hadadden office mai dauke da kayan sanyi na zamani sannan kuma a karshen wata yana da wani kayataccen albashi mai tsoka da wannan ake rudan wasu sannan a cusa musu sha’awar shigarta ta ko wacce hanya.

Idan kuma muka maida duba izuwa ga sana’ar hannu zamu ga cewar akwai wasu sana’oi da dama da mutum zayyi wanda zai iya tashi da dubu 5 koma fiye da haka wadda in an kwatanta za’a ga cewa abinda mutum zai samu a karshen wata zai nikka albashir mai aikin gwamnati har sau biyu ko fiye da hakan.

Wani abin mamaki ma shine kusan ko wane matashi sai ya yi wani sana’a  kafin ya iya samun kudin da zai siya Data, amma kuma bai san ta yaya zai iya samin kudin a saman yanar gizo (Internet).ta hanyar amfani da datar daya siya. Insha Allahu a wannan makon, Duniyan Fasaha zata kawo muku wadansu cikakkun hanyoyin da za’a iya bi domin neman na kashewa a saman yanar gizo (Internet).

1.==> HADA SHAFUKAN YANAR GIZO: Shafukan yanar gizo abune mai matukar amfani sabili da yana taimakawa wajen bada cikakkiyar bayani game da kasuwanci cikin sauki, A hakikanin gaskiya adadin shafuka a yanar gizo yana ninkuwa a kowace waye war gari, haka kuma adadin masu bukata yana kara bunkasa.

Masana kimiyya sun nuna cewar duk wata kasuwanci da bata hadayya da yanar gizo to hakika ta na rasa wasu damammaki da zata iya samu wajen tafiyar da kasuwancin, haka zalika alamomi sun nuna cewar duk wani kasuwanci da bai da shafi na mussanman a yanar gizo nan da wasu shekaru masu zuwa dole sai ya samo.

            Hada shafin yanar gizo ba kowa zai iya yinta ba sai wadda yake da ilimi sannan kuma yake da basiran yin hakan, akwai mutane da dama wadda suka gwanance wanje suranta shafukan yanar gizo sannan kuma sun dauke ta a matsayin sana’a.

Hada shafi a yanar gizo ba wani abu mai matukar wahala bane sai dai ya zamana dole mutum ya koyi wasu yaruka wadda aka fi sani da ‘programming language’ a turance wadda ita kwanfuta ke fahimta; misali: php, python, JavaScript, ajax, java, Asp.net da dai sauransu.  ko kuma mutum ya koyi yadda ake amfani da wordpress, wix (wadda zanyi jawabin su a wasu makonin masu zuwa) ko kuma blogger wadda nayi jawabinsa a wasu makonni da suka gabata. Koyon daya daga ciki ababen da na lissafo zai bada damar samun makudan kudi a yanar gizo.  

2.==> JAGORA: Wannan wata halattacciyar hanyace da ake samun kudi da ita ta hanyar jawo wani yayi rajista bayan anyi sannan kuma an tabbatar da ingancinsa. A mafi yawanci sa’oi wannan damar yana aiki ne ga manya ko kuma sabobbin shafuka dan samun mabiya da zasu taimaka musu wajen gudanar da kasuwancinsu.

Yadda abun yake anan shine: Bayan anyi ragista da ita kamfani a mafi yawancin lokutan sukan saka wani adadin kudi da mutun zai samu yayin da ya gayyato wani yayi ragista dan taimaka musu wanjen tallar hajarsu. Sukan bawa kowa addireshi na musamman da zaiyi amfani dashi wajen gayyato mutune.

Duk sa’an da wani yayi rajista da wannan addireshin wadda ya basa zai samu ‘yan wasu changi. Inji bahaushe Iya kudinka iya shagalinka haka zalika ‘Yawan mutanen da ka jawo yawan kudin da zaka iya samu’. Kamfanonin da ke samar da wannan dama sun hada da Konga.com, alibabab.com, Jumia.com.ng, Be With Me Technology, EntireWeb, Renkutten, Yllix, dadai sauransu.

3.==> HADA MANHAJAR WAYA: Adadin mutane dake amfani da wayar salula ya zarce yadda ake tsanmani, sannan adadin yana ninkuwa a kowace wayewar gari.  Wayar salula yakan taimaka matuka wajen sa da zumunta ta hanyoyi daban daban haka zalika adadin mahajar da ake kirkira yana kara ninkuwa a kowace safiya bisa la’akari da yadda mutane ke sa’awar amfani da ita musamman android.

Mutum zai iya hada mahajar waya sannan ya siyar ko kuma za’a iya biyansa ya hada hajar sai dai wannan yana tafiyane hannu riga dana fari dole sai mutum ya koyi wasu yarukan kwanfuta dana ambata a baya kafin cin ma manufa. Amma Alhamdullilahi a yanzu akwai wasu shafukan yanar gizo dake bada damar hada mahajar ba tare da koyon daya daga cikin yarunkan dana ambata a baya ba irin su Androidmob da kuma Appgeyser. Sai dai matsalar wayan nan shafukan basu bada cikkakiyar damar amfani da ita sai an biya wasu kudade.

Lallai ba shakka mutum zai iya samun kudi na hakika da mahajar da ya kirkira ta hanyar saka tallace tallace a ciki, duk sa’ar da wani ya danna wannan tallan zai samu yan wasu changi haka zalika za’a iya biyan mutum makudan kudade dan tallata wata haja kamar yadda zamuyi bayani a gaba.       

4.==> SAKA HOTUNA MAI MOSTI (VIDEO) A YOUTUBE:  Wata hanya da ba kowa ne ya san da ita ba ko kuma yasan amfaninta ba a cikin mutanenmu shine yadda za’a iya samin kude daga YouTube.

Wannan hanya ce mai matukar sauki. Kawai abin da kake bukata shine ka mallaki google account (gmail). Za ran ka mallaki gmail zaka iya zuwa YouTube domin da bude channel.

A cikin wadannan channel din ne zaka rika dora bidiyoyinka. Domin samin kudi a duk lokacin da wani ya kalli wannan bidiyo sai ka tabbatar ka shiga wajen settings kayi checking ko kuma ka zabi monetize, wannan zaya baka damar da zaka sami kudi a duk lokacin da YouTube suka sanya talla a cikin bidiyonka.

5.==> TALLA: Shima wannan wata hanya ce da ake samun kudi a internet ta hanyar yin talla, Duk wani wanda ya shahara da shiga Facebook zaya iya baka labarin yanda zaka ga wasu mutane sukan leka daga wannan zaure zuwa wancan, ba kuma komai ke kai su ba sai dai kawai suyi comment da wani link da zasu ce ka shiga domin samin wani abu. Wadannan mutane ba komai suke yi ba face yima wasu kamfanoni talla.

Da zaran ka danna wannan adireshin da suka baka to zaka shiga a website din kamfanin da suke yi ma tallar, su kuma za’a basu wani dan kaso na kudi sanadiyyar tura ka da suka yi zuwa wannan shafinn. Duk da cewa wadannan mutane suna yin talla ne ta hanyar da mutane ba kasafaye suka cika kulawa ba, kai idan kaso zaka iya yinta ta hanyar da ya kamata.

Misali zaka iya sanar da abokanka da kuke chatting da su cewa ga wani abu nan na karuwa shima ya shiga domin ya karu, da zaran ya shiga shima yayi rajista shi kenan kaima zaka sami kasonka.


Wadanna sune wasu daga cikin hanyoyin da aka fi amfani da su wajen samun kudi a internet, shin ka/ki na da wata hanya da ka/kika sani wanda ban ambata a cikin wannan kasidar ba? Za’a iya turo mana dan dad’awa wanda zai taimaka wa masu ziyara nan gaba. 


mawallafi:

Shugaban kamfanin Duniyan Fasaha, kuma Babban Editan Mujallar Duniyan Fasaha, mutum ne mai son sanar da mutane abinda Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Yanar Gizo, gyaran jiki da sauransu.

1 comment:

TALLA

TALLA

Chanza harshe

Contact Form

Name

Email *

Message *