Uwargida
Barkanki da warhaka, tare da fatar kina cikin koshin lafiya. Allah yasa Ameen!.
Kamar dai yadda muke fada a koda yaushe yana da kyau kina chanza girki lokaci
zuwa lokaci domin tsotsa kunnuwan mai gida.
Bamu
yi kasa a gwiwa ba A yau Duniyan Fasaha ta kawo miki wata hanya mai sauki na
yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwadawa domin yi wa Manyan Gobe ko shimi
mai gida a matsayin abin karyawa a duk safiya ko kuma yin sa domin sha’awar
cinsa ko kai wa aminan arziki da yan uwa.
Abubuwan Da Zaki Bukata:
- Fulawa
- Kwai
- Sukari
- ‘Baking powder’
- Ayaba
- Madara
- Bata
Yadda
ake yin hadin cikin sauki:
Ki
samu ayaba biyu ki kwaba su da cokali mai yatsu, sannan ki zuba fulawa a kwano
sannan ki zuba ‘baking powder’ da sukari da madara, sannan sai ki kwaba.
Daga
nan sai ki zuba BATA kamar cokali biyu sannan ki kwaba sosai. Sai ki fasa kwai
biyu da kwababbiyar ayabar a cikin fulawar da kika yi mata hadin sukari da
sauransu.
Sai
ki gauraya su sosai su kwabu. Sannan sai ki dauko tukunyar gasa burodi ki zuba
sannan kisa a gidan gasa burodi. Bayan
minti 45 ko hamsin sai ki cire.
Za
a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za’a iya aika
wa makwabta domin su dandani sabon salon burodi sai mayar da dogon kwadayi.